...Wani kekkyawan mutum ne bak'i, mai tsananin kama da Amrah yake tsaye ta bakin K'ofar d'aya daga cikin kofofin dake cikin parlour'n._
_Hannun yasa ya share hawayen da suka suka samu daman silalowa, daga haka ya juya ya koma cikin D'akin......._
_koma mene ne yasan shi yaja musu, kaddaransa ne ya shafesu, tun farko shine bai zaba musu Uwa ta gari ba_
_Kaman jiya yau ma, haka tasha aikinta, a yayin da Amrah kebgefenta tana wasa......._
_Tana gamawa tasa na Abbansu a Warmer, sannan ta had'a na Mummy dana Afrah, sai kuma nasu data zuba a plate......._
Tana gama jerasu, ta d'auki na Abbansu tayi hanyar D'akinsa dashi, bayan ta saka acikin madai-daicin try, kana tasa plate da Spoon, sannan na d'ora bottle d'in ruwa a kai.
Tana tafiya Amrah na binta a baya har suka isa bakin K'ofar D'akin Abba.
3 Minutes da sallama ta shiga.
Samunsa tayi yana zaune akan Gado, a yayin da ya jingini bayansa da allon gadon.
Durguzawa tayi a jiye plate d'in, sannan ta dago ta kalleshi, cikin muryan tausayawa ta ce
"Abba barka da rana." Ido ya lumshe mata, ba tare da ya ce komai ba.
Bata sake magana ba, don tasan bazai yi abunda ya wuce hakan ba. ta fara kiciniyar zuba masa abinci acikin plate
.Bayan ta zuba masa acikin plate kana ta mika masa, Ruwan dake cikin bottle d'in ta bud'e, dai'dan yadda zai masa, sannan ajiyeshi a gefe.
Daga haka ta fita daga D'akin, abincinsu data zuba cikin plate da d'auko, kana ta dawo D'akin, suka fara shi, ita da Amrah, yayin da Abba yake cin nasa.
Bayan kaman 30 minutes, zuwa wannan lokacin kuma sun gama cin abinci.
Abba ne zaune a k'asa, a yayin da Amrah da SIMRAH suke gabansa.
Hannayensa dukkansu biyu ya d'ora a saman kansu, kana ta lumshe ido idanusa, bayan wani wani lokaci, ya bud'e tare da cire hannayen daga kan kayunansu.
Hannyensu yasa acikin nasu, har kuma zuwa lokacin bai tofa ko da "A" ba, sai dai wannan lokacin kuma SIMRAH yake kallo yana lumshe idanunsa.
Sai daya d'auki lokaci mai tsayin gaske, kafin ya d'age idanusa daga kanta.
Gane me yake nufi yasa ta murmushi a yayin da idanunta ke tara k'walla.
Cikin sanyin murya ta ce "Kayi hakuri Abba, insha Allah zanci gaba da hak'uri kaman yadda kake horani dashi a kullum.
"Duk da nasan baka magana amma kullum kana min nasiha akan nayi hak'uri, insha Allah zanyi.
"Kullum Abba ina maka addu'a, a wajen Allah, ina rokon Allah daya nunamin randa bakinka zai bud'u, dan Allah kayi tawakkali akan kaddara daya sameka.........
"Ban tab'a jin randa kayi magana ba, ban tab'a jin muryanka ba, ban tab'a ganin Bakinka a bud'e da sunan magana ba. inason ina kallonka kana magana, kodon ina magana da da tad'i da kai kaman ko wacce 'Ya, sabida na daina jina daban acikin mutane ..........
"I have a lot of questions da nakeso maka a game dani da rayuwar gidan nan, inason naji wacece Mahaifiyata! wacece ta haifeni? Nasan Mummy ba Mahaifiyata bace ba! nasan bata haifeni ba! Idan da Mummy bace ta haifeni shin wacece Mahaifiyata Abba?? Inason ganin tawa Uwar, Inason jin maryanta,
"Idan kuma Mummy ce ta haifeni meyasa bata so na? Meyasa ta tsaneni take azabtar dani? meyasa k'iyayyar da takemun ta shafi Amrah? Meyasa kuma tafison Adda Afrah akanmu?
"Kawai saboda muna bak'ak'e? Adda na fara? me laifinmu don muna cikin layin wad'annan skin colour d'insu ya kasance black?
"Kenan mu muka halicci kanmu?
Ta k'arasa maganar tana girgiza Abba, wanda tunda ta fara magana, yake jijjiga mata kai, a yayin da idanusa keta zubar da hawaye, itama kukan takeyi.......
Amrah kuka takeyi, tamkar tasan meke faruwa.........
Sai dai kukan nata, baya rasa nasaba da wanda SIMRAH keyi..........
Domin ita dai a rayuwarta ta tsani ganin kukan SIMRAH, ko ganin wani abu ya samu SIMRAH, don ita kam a ganinta SIMRAH itace Uwarta, domin bata da kamarta..........
Tunda tun tashinta bata ganta a gaban kowa ba, hatta Uwar data haifeta ta bata nuna mata wani so ba..........
Tsakaninsu da Mahaifiyarsu k'yama, hantara, da kuma duka da zagi..........
Hakan yasa tsakaninsu da Mahaifiyarsu babu wani shakuwa ko k'auna.
Haka suka taso tamkar wad'anda basu da Uwa a raye, don a wassu lokutan ji take tamkar wad'anda Mahaifiyarsu ta rasu ma, sun fisu gata, galihu, da kuma kwanciyar hankali.
Tunaninta ne ya katse lokacin da tajita a jikin Abba, wanda yake kuka tamkar ransa zai fita, don har jikinsa yana wani irin rawa tamkar wanda wayan wuta ya kama...........✍️
*# Share fisabilillah👏*
[11/29, 12:05 PM] 'YAR GATAN ROYAL STAR: *