43

14 0 0
                                    

………"Ka bautawa Allah kaman kana ganin sa, kaji tsoron Allah babana, ka da ka cutar da matar da aka aura maka sa bo da baka sonta, ka sani tana da hakkoki a kanka kayi adalci, don Allah kar ta shiga cikin kunci ta dalilin zaman gidan ka, do Allah kamin alk'awarin bazaka cutar da ita ba, haka kuma zaka zauna da duk yarinyar da ka ga na Aura maka, dan Allah ka riketa kada ka wulakantata, ka sani idan ka wulakanta ta tamkar ni d'innan ka wulakanta domin ni na aura maka.


Yau gani mahaifiyarka ina rokon ka dan Allah don Annabi daka rike Khadija amana dan Allah Babana, ta k'arasa maganar tana had'a hannayenta alamar roko.

Cikin rawan murya ya matso kana ya ce.  "A'ah Ammy, please karki rokeni zanga tamkar ni din ban cika d'a na gari a gareki ba. Zanga tamkar ban maye miki gurbin yan uwana da suka rasu ba, zanga kaman ko bayan ranki bazan iya kasance miki waladun salihun ba, umarni kawai zaki bani kinji Ammy na....

Hawayen daya silalo mata ta share kana ta ce Allah ya muku albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyi ba, sai da safe.

Daga haka ta Mike ta shiga toilet d'in dake manne da D'akin.....


Yy zaman minti biyu kafin ya mik'e cikin mutuwar jiki ya yi waje,

Motansa ya fad'a kana yy rivers daga haka ya cilla hancin motan kan ti-ti bayan mai gadi ya wangale masa get d'in.




Tamkar zai wuce a lokacin daya iso dai dan BANDARIWO SUYA ABK, sai kuma ko me ya tuna sai ya fasa ya tsaya.

Kaji ya siya guda uku manya had'in amare, kana sai kuma no-no mai danbu da empty sannan yoghurt, daga haka ya biyasu K'udinsu yy cikin mota ya k'arasa gida......



            "Tabbas ban kasance Uwa ta gari ga Yaya na ba, na bi son Zuciya da hudubar Shaid'an na azabtar da yaya na, na gina musu tsana ta da kai na, Yaya na ne amma basu damu dani ba, kaga dai Simra yadda yara ke Fad'awa jikin Mahaifiyarsu suna kuka a yayinda za'a kaisu gidajen mazajensu suna kuka, amma Simra jikin Kubrah ta fad'a, hakan ya tabbatar min da cewa Simra  bata min kallon Uwa, tana min kallon *WATA UWAR* da ta gallaza mata, tana min tana min kallon *MUGUWAR UWA* Wayyo ni Allah na naga ta kaina..... Mummy ta k'arasa maganar tana fashewa da kuma mai k'arfi.

Abba kam daya gaji da rarrashin ta sai kawai ya zuba mata ido yana kallon ta.


Tafiya mai d'an tsayi yy kafin ya kawoshi K'ofar gidansa, hancin motan ya Danna cikin bayan mai gadi ya bud'e masa get.


Parking ya dai-dai ta kana ya kashe motan, ya rufe bayan ya d'auki abunda ya siya acikin motan.

Lumshe ido idanusa yayi, a lokacin da khamshi mai sanyin ya bugi kofofin hancin sa.

Kan dining ya ajiye ledojin shi kuma ya tafi D'akinsa don watsa ruwa. Bai dauk'i lokaci mai tsayi ba ya fito cikin shirin pyjamas riga da wando dark blue da suka karb'i asalin fatarsa.

Direct D'akin da yake kyautata zaton nan aka kawota ya nufa, don shi har ya na manta da wata amarya.

Haka kawai yakejin bugun Zuciyarsa na k'aruwa, yana k'ara taku yana yadda Zuciyar ke ta harbawa da k'arfi tamkar dai idan yana Simra, to me hakan yake nufi sai ya kauda tunanin tuna cewa yanzu haka itama tana gidan mijin ta.  Ya kai ayar tunanin a lokacin daya iso bakin K'ofar D'akin.

Knocking yy sau uku, jin ba'a bud'e ba yasa kawai ya murd'a handle d'in ya shiga bakin sa na d'auke da sallama.

Simra kuwa wacce ta tsorata ita tsorata, don ita a tunanin ta duk bai kawo mata cewa mijin natan bane, hakan yasa ta hada kai da gwuiwa taci gaba da kuka, jin an bud'e K'ofar yasa cikin hanzari ta d'ago  kanta, take kuwa idanunsu suka tsarke cikin na juna, kaman an jona musu shock haka suka kurawa juna ido.

WATA UWARWhere stories live. Discover now