32

13 0 0
                                    

……… "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!", shi ne abun da ya fito a bakin Illahirin jama'ar da suke gurin.

         da gudu mutane duk suka yi kan motar domin bashi taimakon gaggawa,cikin sauri aka juya motar Sadiq da tayi datsa² glases din duk sun rarratse...


         jini ne kawai yake fita ta ƙasan motar,da sauri suka bude motar suka fito da shi,cikin halin mutuwa, gaba d'aya fuskarshi jini ne ya wanketa..


           matsawa suka yi da shi da sauri, ganin motocin biyu da suka haɗu suna fitar da hayaƙi alamar wuta zata tashi...


         suna janyeshi daga gurin hayaƙin ya ƙaru, gaba daya gurin ya turnuƙe,cikin abun da ba zai wuce minti biyar ba, motocin duka biyi suka kama da wuta...


         Da sauri mutanan da suke gurin suka jaa baya cikin tsoro, cikin inuwa suka mayar da Sadiq kafin motar Ambulance ta  ƙaraso.


         suna nan tsaye motar Ambulance da motar Yan Sada ta tsaya a gurin, da sauri Nurses suka fito daga cikin motar, cikin zafin wutar suka ƙarasa gareshi suka []aukeshi akan wani []an bed da ake daukar wad'anda sukayi accident....


          suna shigar da shi mota, motar yan kwana² (motar kashe gobara), ta ƙaraso gurin, cikin sauri suka firfito, suka fara ƙoƙarin kashe gobarar......

          suna kashe wutar tana []ara hauhawa har wani harshe take, dakyar da ci[]in goshi suka samu halin kashe wutar.......



           bayan an d'auke shi ne , ba'a tsaya dashi ko ina ba sai '''DOMA SPECIAL HOSPITAL'''....


        cikin gaggawa aka fito dashi daga motar zuwa cikin Accident and Emergency
*A&E*......


          gaba daya Dr's din da suke cikin Asibitin  '''Doma'''  wa[]adan ke duty a ranan, suka tattaru a kanshi, domin ceto rayuwarshi, dan bayan zuciyarshi da take bugawa ta cikin na'ura da bb alamar fa zata nuna maka cewar yana raye, gaba daya jikinshi ya saki, fuskarshi ta kumbura, jikinshi ta ko ina ciwo ne....


          tun daga nan na sare da yana yinshi, dan ba shishigi da ikon Ubangiji ba, amma kallo daya zaka mishi kasan ba zai rayu ba, ko da kuwa ya rayu to ya nakasa....


          Yan Sanda ne gaba daya a gurin da aka yi Accident din . sai checking gurin suke, ko da zasu ga shaidar ta inda Sadiq ya fito, ko wani abu da zai nuna Ahlinshi.


             wani ne ya ƙaraso gurin Inspector  da yake tsaye, bayan sun gaisa yace "Yallaɓai ga wani phone nan da Yaro ya tsinta daga nan gurin, ko ta d'aya daga cikin wanda suka yi Accident din ne....?"......

             ya fada yana nuna mishi, ai kuwa ana kunna power na wayar sai ga pic din Sadiq ya bayyana agaban wayar, hakan yasa Inspector din ya jinjina kai ya ce, "Tabbas na d'aya daga cikinsu ne. kuma ina tunanin  zan iya samun wani information na wanda yayi haɗarin, wanda har zamu samu Ahlinshi".....

         Ya fada yana daddana wayar, godiya yawa mutumin kafin ya wuce zuwa hospital d'in....


           ko da yake Doma har lokacin ba'a fito da Sadiq daga Room din da aka shiga dashi ba......


           d'aukar wayar Inspector yayi tare da fara duddubata. cikin sa'a babu wani code hakan yasa ya fara duba last Call din Sadiq, cikin sa'a ya ga wata number da take sama an rubuta '''SWEET MAAMY'''......


            hakan ya tabbatar wa da Inspector cewar Mamar Sadiq ce, dealing number yayi , bugu na daya, na biyu, na ukku Maami ta dauki wayar cikin sanyi jiki.....

WATA UWARWhere stories live. Discover now