🔚🔚🔚 *P. 96–––100* 🔚🔚🔚🔚
*Last page,🤧🤧*
_Alhamdulillah I'm ever grateful ya Allah....._
…………Yana gama had'a mata na jakin ya tattara ta da kayanta ya watso su waje, ya maida kofa ya rufe kiribbbbb......
A dai dai wajen kuma d'aya daga cikin yaran da Sadiq ya saka su nemo masa Afrah ya ganta.....
Ba tare da b'ata lokaci ba kuwa ya dannawa Sadiq kira. Nan ya shaida masa gashi nan zuwa.
Ba bata lokaci kuwa suka zo, tunda Sadiq ya hango Afrah a wajen yake wani shu'umin murmushin shi kad'ai yasan ma'anarsa, hakan yasa cikin tafiya mai kama da yan iska ya nufo inda take.
Sunanta ya kira cikin wata irin siririyar murya daya SA ta gane ainihun mai kiran natat, cikin kukan halin bakin cikin rashin mafita na takaicin da Fahad ya jefata, don dai kuwa yy hacking d'in account, ta d'ago da fuskarta Don ganin wake kiran ta.
Arba dashi idanunta da sukayi yasa ta d'ago cikin mamaki, baki ta bud'e da nufin yin magana sai dai tuni taji saukan mari, bata farfado daga wancan ba taji saukan wani, a take sai daya jera mata Mata biyar.
Wanda yake bayansa ne yake ganin tamkar dukan bai isheta ba, hakan yasa cikin rashin mutunci ya saka hannunsa ya doki bakin ta, take sai ga hak'oranta biyu na gaba sun biyo hannun sa, wajen faduwa k'asa.
Cikin rashin imani Sadiq ya mikawa na bayansa Hannu, bata lokaci kuwa ya mik'a masa goran dake hannunsa.
Har inda take yashe ya matso, cikin zallan rashin imani SA rufewar ido akan abunda ta masa ya kalleta kana ya ce.
"Dukan da aka miki na b'ata min lokaci wajen yaudarata da kikayi, shi kuma zubar da hakora na zaga min mahaifi da wannan bakin nakin yayi, sai kuma mai gayya mai aiki, Yanzu zan cika alk'awarin dana d'auka akanki, "Ai idan baki manta ba, nace miki ki rubuta ki ajiye don kada yayi miki wahalan tunawa, sannan wannan alk'awari ne dana d'auka sai na lalata wannan kyan da kike tak'ama dashi, ya kai ayar maganar yana watsa mata abunda yake hannunsa.
Ihu Afrah ta saka sakamakon rad'ad'i, azaban da suka gwauraye kwa-kwalwarta.
A take su kuma suka bar wajen, ba tare da wani ya gansu a wajen ba.
Wasa-wasa babu wanda ya kalli Afrah ballen tana ya d'auketa zuwa, sai da dare yy masu patrol d'in ranan suka ganta, ba bata lokaci sukayi asbiti da ita.
Likitoci sunyi iya abunda zasuyi, sai dai sun kasa shawo kan matsalan, domin kuwa acid d'in ya gama kona fuskarta, don ko gani batayi, hakan yasa kawai suka nade fuskar bayan sunyi abunda zasu iya.
Hakan yasa ba bata lokaci suka dukufa wajen bincika jikin ta da ko zasu abunda zai nuna musu inda iyayen ta suke.
Da kyar da sud'in goshi suka samu wayanta da kuma wani card nata, ba tare da b'ata lokaci ba sukayi anguwan su, don Fad'awa iyayenta abunda yake faruwa da yarsu.
Kuka sosai Mummy keyi sbd jin masifar data samu Afrah, tasan koma me ne ne ita ta jawo mata, hakan yasa ba bata lokaci sukayi asibitin, sai dai ko ganin ta ba'ayi, a bisa jagorancin d'aya daga cikin yan 999 mai suna Muhammad Hassan Muhammad shi ne ya raka su office d'in Dr. Manasa,
Kallo ya k'are musu bayan ya tsaida idanunsa akan Abba kana ya ce.
"Ammm..... Alhaji gaskiya a bisa dogon binciken da mukayi, mun gano cewa ruwan acid din da aka watsamata yaci naman ta sosai, hakan yasa bazamu iya treating d'in ciwon a nan ba, sbd rashin wadatattunkahan so shiyasa na ce me zai hana ku fitar da ita waje. Kai kawai Abba ya gyada masa, kana daga nan kuwa suka sallameshi suka fita.