SHIMFIDA

98 2 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
       *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa...

🌼🌼Oumm Arfah🥰.

1.

_SHIMFIƊA_

    Gidanmu gida ne na mata guda biyu, mahaifiyata da abokiyar zamanta. Sannan a gidanmu zama ne ake na komai kika yi sai nayi fiye da shi, wato dai abin nufi gidan mu kullum cikin gasar canza kaya ake walau na ɗaki ko na kicin, kuma abin da zai ba ku mamaki, falo ɗaya suke sharing haka kuma kicin ɗin ba dan mai gidan bai da hali ba, a'a kawai shi mutum ne mai son haɗaka musamman ta iyalansa, a tunaninsa yin hakan zai kawo shaƙuwa a tsakanin iyalan nasa, toh za a iya cewa yayi nasara kaɗan don ni da ƴar uwata kan mu a haɗe yake, don ita kam anyi dukan Ni ma hakan an dake ni duk akan tarayyar mu da ita amma basu ci nasarar hakan ba, sai daga baya...
Wannan kenan!
   Mahaifin mu mutum ne mai wadata, kuma mai sakakken hannu, wato mai kyauta,  mutum da ya fi ƙarfin gidan sa, Uba ne na mai Uba, kuma uban maras Uba. Sunan mahaifina Alh. Muhammad Abdullahi Mai Zare, kaf ɗin unguwar kai kusan ma zance kaf garin namu babu wanda bai san Mai Zare ba. Sunan mai zare ya samo asali ne daga lkcn da ya fara harkar sai  da zare da allura, sana'ar da ya gada ce a wurin mahaifinsa bayan noma da kiwo, idan zance ake ta su waye suka gina dukiyarsu daga tushe babu gadon iyaye, tabbas mahaifina idan bai zo a farko ba, toh ba zai wuce biyar ɗin farko ba.
  Sai dai da yake shi ɗan adam tara yake bai cika goma ba, toh hakan ce ta kasance da babanmu, don idan ana lissafin kyawawa ba a zancen mahaifina, don irin mahaifina su ake wa laƙabi da _money miss road_ wato kuɗi sun yi ɓatan hanya, amman abin mamakin kuma duk cikin matan Babanmu babu mummuna, dukkanninsu kyau gare su kamar fitina, shi yasa kowacce take jin ita wata ce.
    Ɗakunan gidan mu aƙalla sun kai guda biyar, domin gidan mu babban gida ne, daga wajen gidan ba ka taɓa tunanin mamallakin gidan nan na da kuɗin da suka kai dubu 100, domin wani rin gini aka mai tun waccan lkcn irin na daidai masu rufin asiri, daga wajen ƴar ƙofa ce haka dai ba ƙarama ba, kuma ba babba kamar gate ba, idan ka shigo kofar ƴar zaure ce ko in ce maku soro, a cikin soron nan akwai wani fallen ɗaki mai girma, an sa katifa ƙatuwa da kujerar 2-seater ɗaya sai kafet ɗin da rufe tsakiyar ɗaƙin wato Centre Carpet, sai labulen kofa da na taga.
   Idan ka baro soron, nan zaka risƙi pankaceciyar tsakar gida wanda aƙalla zai ci motoci uku a Wadace babu takura, daga wurin kana hangen kofar falon gidan, daga can kusan ƙarshen gidan wata ƙofa ce kamar ta gaban gidanmu, ita kuma wannan ƙofar kana shigar ta zata sadaka da garejin motocin mahaifina.
   A cikin falon akwai ƙofofi guda huɗu, ɗaya zata sadaka da ɓangare Hajjah Babba, dayan kuma shi zai miƙa ka dakin mahaifiyata, wanda a ciki suke da ɗakuna bibbiyu kowanne da bayi, ɗayar ƙofar kuwa wacce ke tsakiyar ƙofofin matan gidan shi ne na mu, sai dai shi ɗaki ɗaya ne amman fa wankacece ne da bayinmu, gadonmu guda biyu, kowacce wardrobe ɗin kalar da ta ke so ne a gefen inda gadonta yake, nawa ya kasance fari ne, na ƴar uwata kuma coffee brown, wannan yasa fentin ɗakin side ɗaya fari, side ɗaya coffee brown.
  Ɗayar ƙofar da ke kallon namu kuma ita zata kai ka kitchen da store, sai kofar fita ta cikin kicin ɗin. Kaf ɗin gidan nan kuma yara mu uku ne kawai a cikinsa, daga ƴar uwata wacce ta ban shekara ɗaya da wata ɗaya sai ni sai ƙanina mai bin min.
   Kusan zan iya cewa hakan familyn mu suke, ba mu da yawa zuri'a, don mahaifina su biyu kawai mahaifiyar su ta haifa, shi da ƙanwarsa Ramatu, sai kishiyar kakarmu ce mai huɗu, Baffa Iro, Baffa Ado, Gwaggo Mairo sai Gwaggo Sailuba. Su ɗin ma daga mai biyu, sai mai ɗaya mai yawan zuri'a a cikin su shi ne Baffa Ado don matan aurensa huɗu da yara tara. Gwaggo Ramatu kuwa ƙanwar babanmu ita haifa take suna komawa, don haihuwar ta goma sha uku amman ɗaya ne kawai ke raye, mace ko namiji ne oho Ni ban sani ba, don rabon mu da ita tun haihuwar ƙanina Abdullah, shekaru kusan goma kenan, lkcn ma da ciki jikinta kamar wannan ne ke raye....

   Shi mahaifina sai da ya fidda rai da haihuwar ma kafin Allah Ya ba shi mu. Don shekarar su shida da aure shi da Shema'u bata haihu ba kafin ya auro mahaifiyata, Bilkisu. Ita ma sai da ta shanye shekaru uku a gidan sannan Allah Ya bai wa Haj. Shema'u haihuwa in da ta haifi Fa'iza, watan ta Fa'iza huɗu Allah Ya bai wa mahaifiyata cikina, ta haife ni aka samin sunan Rahmatu, mahaifiyata ce ta zaɓar min sunan, a cewar ta Ni ɗin Rahma ce ta Ubangiji _*Rahmatullah*_.
   Mahaifiyata mace ce mai kyau na gani a tanka, sai dai da ta haifo ni sai ban ɗauko duka ba, hancina irin na mahaifina ne mai buɗaɗɗen ƙasa, amman fa akwai karan hanci, haka ma idanunsa na ɗauko masu ɗan girma da wadataccen gashin gira da na ido, sai duhun fatarsa, gashin kai da tsawo sai ƙirar mata kawai na ɗauko na mahaifiyata, saɓanin Fa'iza da babu abin da ta ɗauko na babanmu komai na mahaifiyarta ta ɗauko, hakan ya sa ta kasance mai kyau, ina nufin kyau mai suna kyau, har wani lkcn na kan ji dama ni ce ita...

  Bayan haihuwa ta da shekaru takwas ne ta samu cikin ƙanina Abdullah, haihuwarsa ita ce dalili ko ince mafarin komai, ciki kuwa harda janyewa da ƴar uwata Fa'iza tai daga gare ni....
  A cewar mahaifiyarta, maman mu ce ta hanata haihuwar ƊA NAMIJI... Sannan ta haifi Abdullahi ne don ta mallaki duk dukiyar babanmu, a faɗar ta, idan Fa'iza ta ci gaba da bi na, ba za a barta ta auru ba ko ta samu mai arziƙin da suke fata ba musanman ganin yadda Fa'iza ta ke da kyau na gani a faɗi, saɓanin ni, tohm ni dai sai dai a ce babu laifi, don ni ba kyakkyawa ba ce sannan ba za a sani a layin munana ba, amman for sure ina cikin mata masu abin nunawa, nawa kyaun kenan....

Toh fa! Me kuke tunani? Next page za mu fara nitso cikin labarin, wannan shimfidar kawai background ɗin su, yanayin yadda suka faro da dalilin rabuwarsu...

🌼🌼Oumm Arfah🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now