🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 30
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Alhmdulillah Alaa ni'imatil Islam_
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
Tashi na kenan daga bacci, na samu daƙon Mammy ban damu ba don waya ta a kashe ta kwana sbd damu na da bawan Allahn nan ya yi da sai na turo masa shigar da na yi ta bacci, na tura ɗaya kuma wai sai dai na cire kayan mu yi vid call, ban ga zan iya ba gsky, may be nan gaba, don haka na kashe wayar. Ko karyawa ban yi ba, na fito don Mamma da kan ta ta zo ta tashe ni don ban yi bacci ba cikin dare ciwon mara ya saka ni gaba, Allah Allah na ke jinin nan ya zubo ko na samu sa'ida ance idan ka san namiji shi kenan kai da ciwon mara har abada, amma ina ga ban da ni, sai bayan asuba na samu baccin ya ɗauke ni bayan na yi sallah, shi ne sai yanzu ana neman 11 na safe. Ɗaki na bi Mamma na gaida ta sannan na je ɗakin Mama (Haj Shema) na gaishe ta, na koma ɗaki ina ɗan haɗa kayan da za su min kwana biyu , Fa'iza ta shigo ta ce "duk murnar tafiyar ce haka? Za ki gudu gidan surukai ki bar mu ko?" Na ce "kai Ya Fa'iza ina kewar Mammy ne kawai fa" ta ce "uhm na ji...yauwa ni kam ina passport ɗin ki da aka mana ne?" "Tab ina na san inda ya ke, wani abu ne?" Fa'iza tace "so na ke na gani national ne ko international" na ce "ya ake gane wa?" Ta ce "nemo na nuna miki, ina son idan Mama za ta je Saudi Arabia ganin likita na bita" da ƙyar na samu ganin passport ɗin a cikin wasu shirgin littafan mu, na ba ta na juya na kama wani sabgar, na fita zan yi ma Baba sllm, ban sani ba ma ashe yau sammakon fita yayi, sbd kayan da ya saka order sun iso. Sllm na musu har Fa'iza na shiga mota ina ɗokin ganin Mammy (faɗi gaskiya) an ce ka so mai son ka. Muna isa gidan, na nufi ɓangaren su Mammy sai dai a rufe ya ke alamun ba su tashi ba don daman a kicin ɗin waje ake dahuwar abincin masu aikin, idan sun tashi bacci kuma Mammy ke musu na su. Jin ƙofar a rufe na dawo wurin driver na ce a rufe ne, sai ya nuna min wani ɓangare wai na shiga, rai na ɗaya na bi inda na nuna min, na tarar da wani tsararren flat mai kyau da kwantance ban taɓa zuwa wannan gidan ba don dai bayan dawowar su ne suka tare don haka komai a sabo na ke ganin shi, ina isa ƙofar na danna bell, maimakon a zo a buɗe min sai na ji doorbell na ce "say your name pls" ikon Allah, na ce "Rahma... Rahmatullah Muhammad Abdullahi" ina gama faɗe na ji an ce "wicm Mrs Abdurrahman Wazata" nan ƙofar ta yi unlocking kan ta ta buɗu, na shiga ciki ina mamaki wato kudi masu gidan rana ne, wato idan ba a san ka ba za ka iya shiga ciki ba kenan, amma a ƙasan raina ina ta maimaita *Mrs Abdurrahman Wazata* da aka kira ni da shi, da gaske fa ni ɗin matar Abdurrahman Wazata ce ko? wani nishaɗi na ji sosai tuna haka, ina ta tunani ban kula ba na tsinci kai na a tsakiyar falon, ina ɗago kai na kuwa na yi arba da kyakkyawar zane wanda sai da na sunada kyau na gane zane ne ba hoto ba, zanen Mrs Abdurrahman Wazata ne don a ƙasan hoton ma hakan aka rubuta da wani salon rubutu...wait idan na fahimta ɗakin sa na shigo kenan? Inna lillahi ko ba nan aka kwatanta min ba? Na juya na nufi ƙofa zan fice, sai dai kuma fitar ma sai da izinin mamallakin sashen. Tashin hankali kenan, ba mafita dole na ja ƴar jaka ta na rungume a jiki na na zauna kan kujerar falon ina jiran sarautar Allah... Ƙarar buɗe kofa ne ya sa na ɗago kai na zuwa ga inda ƙarar ke fitowa, Master ne ya fito sanye da pyjmas jikin sa, wani kallo ya ke min da idanun bacci ya na wani lumlumshe su, ɗauke kai na yi da sauri don abin da nake gani cikin idanun sun girmi ƙarakin kwanya na, nufo ni yayi kan sa tsaye, ya ɗago ni ya rungume tsam kamar za a ƙwace masa ni yace "Bae ba gaisuwa?" "Ina kwana?" Na furta a hnkl, sbd yadda ya ƙanƙame ni ɗin, bai amsa ba sai ya kama fuska ta ya sumbace ni kaɗan, ya ce "daga yau wannan gaisuwar na ke so, kin ji?" Bai jira cewa ta ba ya kama ni "mu je mu ɗan ci abinci, mu kwanta, tun ɗazu na ke jiran zuwan ki amma ba ki zo ba ashe shi ne bai tafi ɗauko kin ba, yanzu bacci ya fara ɗauka na kamar a bacci na ji ƙamshin ki na fito, ashe da gasken ke ce" kicin ya kai ni ya kawo kujera ya zaunar da ni ya ce "zauna ki kalli yadda mijin ki ke aiki, mene ki ke so?" Ni dai ba baka sai idanu kallon sa na ke yadda ya dage yana fito da abin da zai buƙata "mene ki ke son ci?" Ya kuma tmby ta, budar baki na nace "kunun gyaɗa sai alkuɓus da miya" dakatawa yayi daga wanke tumatir ɗin da ya ke yi ya kalle ni yace "amma wasa kike yi ko?" Na gimtse dariya ta na ce "da gaske na ke" ya ce "zaki iya jira? Sai na gyara gyaɗar da waken" na ce "in dai zaka min zan jira" ya ga dai da gaske nake, sai ya nufi store ya fito da waken da gyaɗar, tsayuwa yayi a gaban sink yana kallon su yana tunanin ta inda zai fara, ya kalle ni ya ce "Bae ki bari gobe sai na miki, yanzu fa 11 da kusan rabi, kin yarda gobe na miki?" Ni dai na dage na ce idan ba shi ba, ban cin komai, ganin lkc na tafiya kuma yana son yin min abin da na zaɓa sai kawai ya ɗau gyaɗar zai sheƙa mata ruwan zafi, da sauri na riƙe hannun shi ina murmushi na ce "just kidding, wasa na ke yi fa" ina iya ganin irin yadda fuskar sa ta wadatu da farin cikin jin wasa na ke amma sai ya ce "kin tabbata?" Na gyaɗa kai na ina mai jin daɗin yanayin da mu ke ciki, ko bai so ni ba, idan zai riƙa tarairaya ta haka, ban da mtsl, hakan ma ya fiye min so a fatar baki kawai. "Kin tuna wannan ƙwan da na taɓa soyawa ki ka cinye a kicin, in yi irin shi?" Ƴar kunya na ji, sbd tuna ranar, sai na sa kai na cikin jikin shi wai ni kunya, ya ce "to sake ni, kafin na wuce gona da iri, kin san mijin naki lafiyayye ne" kallon sa na yi ina auna maganar sa kafin na fahimci me ya ke nufi, hanyar waje kawai na yi, taku biyu ya dawo da ni ya zaunar ya cigaba da aikin yanka tumatir, sai da aka zo kan albasa ne ya gane shayi ruwa ne, kuma sai Allah Ya sa albasar mai zafi ce, haba kafin kace me? idon sa ya yi face-face da hawaye, tausayi ya ba ni, na tashi zan amsa, amma maimakon ya ba ni sai ya ce "share min hawayen ne, bari zan ƙarasa" ina gama share masa hawayen ya sa ni a gaban sa kan sa a kan kafaɗu na na ɗago kai na kalle shi yace "na san abin da ki ke so kenan" in short omelet ɗin nan kafin a gama shi an kusa 12, muna gama ci kuma ya ja ɗakin sa wai na taya shi wanka, ko da na tsaya musu, cak! ya ɗaga ni sai cikin ruwan da ya tara a bathtub, nan ma a lalace ya ke komai, komai ya ce sai ya fanshe ƙwalelen da na dinga masa da su don na ga bai da ido. Ƙarshe dai kiran sallah ya fito da mu daga bayin nan. Allah Ya sani, wannan rayuwar ita ce irin rayuwar da nake fata da buri, sai aka yi dace, zuciya na son abokin tayin, don haka ban ɗau lkc ba na fara mayar da martani, wanda na kula hakan ya ke so shi ma, sallahr ma jam'i ya ja mana mu ka idar, ba mu nemi wani abincin ba ya ja kan gadon sa haɗaɗɗe ya naɗo ni jikin sa bayan ya tabbatar bai bar abu ɗaya mai amfani a jiki na ba, sai bacci. Za ku yi tunanin na san inda na ke ko? Toh gaba ɗaya na manta inda nake, da wadda na zo gidan domin ta, Abiey na kawai na ke ji da gani...

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Storie breviMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...