🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*RAHMATULLAH*_Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah🥰.
_Allah Ya kai haske da RAHMA zuwa kaburburan ƴan uwa Musulmai wanda suka riga mu gidan gaskiya. Allah Ya jikansu da RAHMARSA._ Ameen.
5-6
Daga wannan ranar na koma sanya niqabi wanda daman ina sawa, don gani nake kowa zai ke nuna ni ace ni ce wanda saurayin ta ya barta saboda muninta...
**********
"Alhaji yanzu ya ake ciki ne?" Cewa Ghali p.r.o "idan zancen nan ya fita da, ba Ni kadai ba dukkan mu abin zai shafa gwara a san mai yiwuwa tun da wuri" Alh. Bulama ya kalle shi sannan ya kalli abokin sa yace "take care of it" yayi sama abin da yana cewa "zan turo maka da kuɗin anjima" cikin nuna girmamawa da ƙara neman wurin zama yace "an gama ranka ya dade....mu je ko" ya faɗa yana kallon Ghali. Nan suka rankaya su fito daga gidan baƙin sannan kowa yayi hanyarsa...
*********
Wata uku suka shige cikin goman da aka sa na biki, tuni Hajiya Babba ta ke ta daka order na kayan kicin na kece raini, da tsadaddu beddings na manyan sosai, mamma dai na ta ido, amma ta kudiri niyyar yi mata gyara irin na amaren gayu a matsayin gudunmawar...
Ranar yau na daga cikin ranakun da ba zan manta ba... Tafe nake bayan na kai wani sakon turare set na amare da Mamma ta aike ni na kai wa wata Hajiya da ta yi order na kayan turarukan, sanye da niqabi na ina tafiya sai jin sallama na yi daga bayana, banyi ƙasa a gwuiwa ba na amsa sallamar tare da juyowa thinking zai yi tambaya ne akan wani abin, amma abin mamaki maimakon yin tambayar da na ke tunani a'a sai ya tambayi sunana da izinin zuwa gidan mu, kamar ba zan basa ba, amman me? Ni ɗin mai yunwar a so ta ne, don haka babu jinkiri na fada masa suna na, jin bai tambayi gidan mu ba sai jikina yayi sanyi, na wuce ina tunanin yadda zai zo gidan mu alhalin ban faɗa masa ba. Nan na fara tunanin sa, wato shi ɗin dogo ne amma ba can ba ya na da dan jiki wacce komai wuya bata saukan nan, kuma shi ɗin ma baƙi ne amma ba can ba don ya fini haske kan sosai, na lumshe ido ina tuno yadda ya furta min sallama cikin natsuwa, nan na roƙi Allah Ya sa wannan ɗin RABONA NE... Abin da ban sani ba ashe bi na ya yi a baya har ya gano gidan mu, da yamma kuwa sai ga shi an aiko kira na, cikin ƴar fargabar yadda zan fuskance shi da fuska ta babu niqabi na fita cikin sanyin jiki, na same sa a waje, kai na ƙasa ban ɗago ba na masa sallama sannan na mai jagora zuwa cikin zauren... Na buɗe baki zan mai bayani ya riga ni da faɗin "sorry ban nemi iznin zuwa zance ba tun mahaifin ki ba amma gashi na zo, kiyi hakuri na kasa hakura ne har sai tmby ɗin"...ya nisa sai kuma ya cigaba "suna na Ibrahim Muh'd, zancen gsky mlm Rahma ni ba wasa na zo ba aure ya kawo ni, kuma yadda nake ji idan kin amince min na shirya aurenki, da zaran mun ɗan fahimci juna, idan kuma ba ki da ra'ayina pls kada mu ɓata wa juna lkc, kin ji"...duk maganar nan da ya ke sau ɗaya ban ɗago ba amma nasan deep down tausayin kaina nake don na san yana ganin munin fuska ta zai canza shawara "kin yi shiru, kuma kin ƙi ɗago kai ki kalle ni, ya za ayi ki san ko na miki". "Kayi hakuri Allah Ya baka wacce ta fi ni amma ni ban dace da kai ba" na fada da rauni a murya ta"mene yasa kika faɗi hk Mlm Rahma masoyi ai bai zama maƙiyi, don Allah ki ƙara nazari zan dawo jibi, sa min numbarki pls" ya faɗa yana miƙo min wayarsa...ban karɓi wayar ba amma nayi kasadar ɗago kaina sannan na haska da fitilar wayata sbd duhun zaure, ido ya ƙura minkamar ya ga wata abar da bai taɓa ganin ba, ganin haka ya sa na kashe hasken wayata nace mai "ka ga dalilin da yasa nake cewa ni ban dace da kai ba ko? Me za kayi da ni? Pls ban son sai an kai wani matakin kuma zance ya sauya, don haka, Allah Ya ba mu alkhairi...." Da faɗar haka na juya zan tafi ya tsayar da ni ta hanyar kiran sunana, na tsaya amma ban juyo ba, ya ce "ai kya tsaya ki ji mai zance ko, na fa sanki tun kafin na zo nan ɗin kawai sunan ne sai yau Allah Ya sa zan sani, amma tun sanda kike fita ba niqabi na ke ta son na miji mgn, amman kwarjinin ki ya hanani, don haka ni ba kyan ki ko wani mai gushewa ya kawo ni, ke nake so da zuciyar ki ba yanayin halittar ki ko jikin ki ba, don hk kada ki min kuɗin goro da sauran maza" waɗan nan kalami na sa ina ganin tun da nayi wayau shi ne karo na farko da na ga mai sona a yadda nake bayan iyayena..., kun san yadda nake ai ba jan ji na bashi damar zuwa ga mahaifina neman izinin zuwa gidan mu zance, nan muka rabu bayan mun yi exchanging numbar waya. Ban tabbatar da gaske ya ke sai da naji babanmu na zancen da Mamma and abin burgewar shi ne mahaifin sa tamkar babban wa ya ke ga mahaifina don ƴan gari ɗaya ne, wannan zance ta yi wa babana daɗi ya kuma yabi Alh. Muh'd ɗin akan halayyar sa ta gari... A takaice dai, zuwa biyar Khalilina (hakan nake ce masa) yayi aka ba shi damar turo manya, and Alhamdulillah yau suka zo tmby an basu an kuma tsaida ranar wata shida daidai na Fa'iza wanda yanzu an ci watanni huɗu...*********
Tsatstsaye su ke kamar wasu dakarun sojoji suna sauraren Uban gidansu da yake zazzaga musu fada akan yanzu kuɗi sun rage shi ga sbd su ma sun rage kawo abin kuɗin, shiru suka yi babu mai bakin magana sai can wani daga cikin su ya ɓudi baki ya ke "ayi mana aikin gafara, ynz yaran ne wahalar samuwa suke kuma hukuma na ta tsananta bincike game da ɓatan yara, shi yasa muka ɗan dakata ƙadan, amman a bamu lkc za mu kawo abin kuɗin nan babu jimawa" nan sauran ma suka haɗa baki suna cewa ayi hakuri. Sun ɗau lkc suna tsara yadda zasu canza salon satan yara da suka saba... (Ni dai nan na baro su, don ina da abin yi).*********
Mahaifan Qais ɗin Fa'iza ne su ka zo suka nemi alfarmar a dawo da bikin baya sbd shi Qais ɗin zai tafi wani course ƙasar Amurika kuma ya na son ya tafi ne da matar sa idan da hali. Jin haka yasa mahaifina ya nemi Khalil da iyayensa idan sun shirya, babu ɓata lokaci suka amince, wanda dama shi Khalil ya ce min a son ran shi bai so auren ya wuce wata uku ba, tohm jin wannan zance kusan yafi kowa murna don dama shi ya ce min a shirye ya ke, toh muma ba mu da zaɓi sai na fara shirin biki babu kama hannun yaro... Abdul kam ya fi kowa murna don wannan ne karo na farko da za ayi wani sha'ani a gidan tun bayan haihuwar sa, zumuɗi har ya sanar da abokin sa makaho cewa yayyunsa biyu za su yi aure kuma zai gayyace shi biki, shi dai makahon murmushi kawai yayi yace sai dai ka zo ka kai ni ko yace eh zan zo ai...
A yanzu halin da Abdul ya ke ciki da makaho ba babanmu ba har Mamma sai da aka shigo da makaho ya gaishe ta, shi kuma baba a masallaci suka haɗu har su kan yi hira sosai, yanzu ta kai ma kullum makaho na da kwanon abinci a gidanmu, safe, rana, da dare. Amma ni har ynz ba aminta na yi da shi ba.**********
*_BAYAN WATA ƊAYA_*.
Ya zuwa yanzu bikin saura wata ɗaya don haka tuni iyayenmu mata sun tabbatar sun gama gwangwaje mana kayan kicin ɗin mu masu kyau, ni kuma tuni an hana ni fita sbd gyara na musamman da Mamma ta ke min, ko da ta nemi yi wa Fa'iza, ƙi su kayi a cewar su wata ƴar Nijar ce zata zo ta mata... uhmm wai Mamma na iya mata mugun abu da sunan magani ko gyara...*******
Yau Abdul ke ta farin cikin dawowan makahon abokinsa gidanmu, don can gidan da ya kama hayar ɗaki ɗaya sun kore shi bai biya kuɗin haya ba , shi ne ya ke kwanan masallaci, Allah da ikonSa sai babanmu ya gan shi shi ne yayi masa tayin zuwa ya zauna a cikin ɗakin soronmu... Ko a jikina don nasan na kusa barin gidan, veryyy sooooon....**********
Ana saura kwana goma biki da sassafe Khalilina ya kira ni akan yana da daddaɗan lbr da zai bani pls na fito ko minti biyar ne ya ganni, nace mai ya faɗa min ta waya ba za a barni na fito ba, shi kuma ya ce sai ya zo na fito zai gaya min, toh kawai nace masa don wani sa'in rigimar sa tafi ta yaron goye, can anjima ya kira ni akan yana waje, na fito saɗaf saɗaf sai ga anty Yagana, gani na da hijabi ya sa ta san fita zan yi ai kuwa ta kora ni ciki ta kuma buga min gargadi kar na kuskura na fita waje, dole ba yadda zan yi na kira shi na bashi hakuri akan an hana ni fita, da kyar na samu ya tafi bayan ya gama ƙorafin goben na zai kawo sadakin sa yadda ba za a hana shi ganina ba, dariya kawai na yi ni dai na koma bacci na...*********
A cikin bacci na, na ji kamar salati ake da sallallami kamar ba zan fito ba amma na taso na fito falon, nan na tadda Mamma da Hajiya a tsaye tare da babanmu, fitowa ta tasa suka kallo ni da tausayi, sai babanmu ya juya yana faɗin bari yayi sauri ya samu jana'izar don karfe 10 suka ce za a yi jana'izar. Abu ɗaya wannan da na fahimta shi ne wani ne ya rasu, kuma an sanshi a gidan mu... Bayan fitar babanmu sai na taho wurin Mamma wacce ta ke share ƴar kwalla daga idon ta "Mamma lfy? Waye ya rasu?" Kallona ta yi cike da rauni sannan ta ja ni zuwa ɗakinta, Hajiya kuma ta wuce ɗakin ta. Da shigar mu ɗakin Mamma ta zaunar da ni a bakin gadon ta, ta kama hannaye na tace "Rahmatullah wa ye ke rayawa da kashewa?" "Allah" na bata amsa "wa ya fi kowa son mu?" "Allah" na bata amsa sannan cikin ƙosawa da son jin waye ya rasu nace " Mamma na san idan lkcn mu ya kai babu mai hana mu tfy, kuma kowa lkcnsa ya ke jira, kawai ki faɗa min waye ya rasu? Na ƙosa na ji don tun ina bacci nake jin kamar za ayi gagarumin rashi, waye pls Mamma?" "Rahma ki yi hakuri, Allahn da ya fi mu son bawansa Ibrahim ya karɓi abinSa" "Allah Ya jiƙansa da Rahma, halan cikin ƴaƴan su Kawu ne ko? Don ban ma san shi ba ko?" Mamma ta kalle ni cike da tausayi sosai ta ce "Rahma Ibrahim ɗin da za ki aura nan da kwanaki kaɗan ne ya rasu" na girgiza kai na ce *Khalil ɗin da ya kira ko awa biyu ba a yi ba, shi ne za a ce min ya rasu? Mamma duk wanda ya kawo wannan lbrn to karya ce tsurar ta" na faɗa hawayen da ban san na meye ba na gangaro min a fuska.... Rungume ni Mamma ta yi ta na faɗin yi kuka Rahma rashin masoyi babu daɗi... Banda wannan ni kam ban kuma sanin mene ya faru bayan nan ba, amma tabbas nayi fatan bin sa can inda ya tafi ɗin....#reality
#rahmatullah
#marriage
#mairabo
#familyaffair
#makahonabdul
#AAwazata
#destinyPlease comment and share...
🌼🌼Oumm Arfah🥰

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Historia CortaMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...