[5/25, 4:54 AM] Oumm Arfah: 🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah🥰
Wattpad @oummarfah20
Page 18
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Yaa Allah Ka gafarta ma magabatan mu, Ka kyauta namu ƙarshen. Ameen_
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
Yau makaho kwanan sa uku bai zo gida ba, and na damu sosai, ba wai don bai taɓa yin kwana uku bai zo ba a'a har kwana bakwai ya kan yi kafin ya zo amma wannan karon gani nai kamar shekaru uku ne ban gan sa ba kuma ban ji shi ba ko a waya bai kira ni ba. Kaina na ɗaga na kalli agogon ɗakin huɗu da rabi, ajiyar numfashi na ajiye da niyyar idan har biyar ta yi bai kira ni ba toh Ni kam zan ajiye pride ɗina na kira shi.Haka nan nai zaune ina jiran biyar ta yi amma kai biyar ɗin ma ta ƙi sauri, da ƙyar na ƙara minti takwas akan huɗu da rabin nan na ɗaga waya ta a karon farko da niyyar kiran shi, ringing ɗin da wayar ke yi tare suke da bugun zuciyata, tunanin abin da zan ce masa na ke idan ya ɗaga, ban yi tunanin hakan ba na kira da ba zan kira ba, ynz ma sai fatan kada ya ɗaga wayar nake, kuma ni na kasa kashewa daga nan wuri na ...
*******
Zaune yake a wani ɗakin sirri da ke a sashen sa wanda babu wanda ya san da shi sai shi mai sashen, nazarin wasu videos ɗin da wasu cameras ɗin sa suka naɗa ya ke, don duk inda ya ke yawan zama yana da ɓoyayyar abin naɗar hoto kuma ko amintattun yaran sa ba su san da su ba, shi yasa wani lkcn idan yayi abu suka masa kirarin da suka shirya masa _Master hatsabibin hatsabibai, hatsabibanci kan sa tsoronka ya ke_...hnklnsa ya tafi sosai kan abin da ke gaban sa har bai ji vibrating ɗin wayar sa ba don shi ba mutum ne mai son hayaniya ba shi yasa kullum wayarsa a silent ta ke, sai vibration na biyu sannan ya ji ya ɗaga wayar ma ba tare da ya duba mai kiran ba...
"Hi baby!" Aka ce daga ɗayan ɓangaren, bai tanka ba don jin muryar ya san mai kiran, Madinah ce his so called wife to be..."ina ka shiga ne, na zo baka nan gani yanzu a bedroom ɗinka amma baka nan kuma ga motar ka a gidan, pls baby kana ina?" jin hakan ne ya sa ya ciro wayar daga kunnen sa ya kalla ya ga numbar Nigeria ce alamar ta dawo kenan. Can cikin ransa a ɓace ya ce "kamar na hana ki shigar min ɗaki anyhow, ko?" Wani sanyin daɗi ne ya kashe ta jin sassanyar muryarsa ta doki dodon kunnenta, "baby ɗakin mijina ne fa ba komai don na shiga ai kamar ɗaki na ne". Ya ja tsaki ya kashe wayarsa bayan ya tabbatar mata da idan bata bar mai ɗaki ba zata gane kuren ta. Bata fitan ba sai da ta gama ƙare ma ɗakin kallo tana imagining ita da shi a ɗakin, a duniya bayan kanta ba wanda ta ke so kamar AA Wazata, he's just perfect for her, gwara ta aure abin ta ya zama na ta ita kaɗai, ta fice tana ayyana yadda zata sa mahaifin ta a gaba da mgnr auren nan kafin wani abin ya ta so, tunda ta san halin kayanta...*******
Har wayar ta katse bai ɗauka ba, sai kuma na gode Allah da bai ɗauka ba tunda bai da ido bare ya ga na kira, sai dai idan wani ya duba masa...Nagode Allah amma kuma raina na a ɓace akan dalilin rashin ɗaga wayata da bai yi ba... Kamar zan fashe haka nai ta kumburi na kaɗai a ɗaki da na ga hakan ba mai ɓullewa ba ne sai kawai na kama azkar ɗina na maraice ganin shida ta buga, na kuma shiga kicin, ina addu'o'i na ina girki, tuwo zan yi daman nayi miya ta tun ɗazu da suka kawo wuta, ana kiran sallahr magriba na gama tuwona na mulmule a leda na bar kicin ɗin bayan na gyara inda na ɓata, na sake alwala na miƙa sallahr magriba ina jira isha'i...
*******
(Bari mu leƙo Fa'iza mai kyau).
A ynz rayuwar auren mai kyau ba kamar sauran rayuwar aure ba ne ,don ynz tsakanin ta da mijin nata haihata haihata, abin har da duka, tun sanda ya ruɗe ta da magani a cikin abinci ta daina cin komai na hannun sa, hakan ya samar mata da tsira daga mugun aikin sa, bata ƙara tsinkewa da lamarin sa ba sai da Allah Ya sa ta kama shi yana ɗura abu a cikin goron ruwan da ke cikin fridge ɗin falonta, da syringe, tun daga wannan lokacin ta daina shan ruwan ko'ina sai wanda ta ɗebo daga famfo direct, ta rame ta lalace kamar ba mai kyau ba, a da yana ɗan lallaɓa ta ganin kamar bata san abin da ya ke aikatawa ba sai da ta fara masa ƴan wa'azizzika da nasiha akan ya canza Allah zai yafe masa ya tuba ya koma ga Allah, ai kam ranar ta gane shayi ruwa ne, don uƙuba mai suna uƙuba ya gana mata, ya kuma tabbatar mata da idan ya ji maganar a waje, ba ita kaɗai ba kaf danginta zai ƙarar da su ɗaya bayan ɗaya... Sosai wannan barazanar ta tsoratata kawai sai ta koma ga Allah tunda ta gane Shi kaɗai ne gatanta a ynz.
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Cerita PendekMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...