3

50 3 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
     _*RAHMATULLAH*_

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼Oumm Arfah🥰.

3.

  Da gudun gaske Abdul ya nufi makahon nan ya tadda da shi a bakin masallaci, ina iya hango irin farin cikin da Abdul ke ciki daga nan in da nake tsaye, bana jin mai suke zantawa amman na ga Abdul ya juyo yana kallon in da nake tare da nuno ni, sai kuma na ga Abdul ya kamo hannunsa zuwa in da nake tsayen, tun daga can ɗin na kafe ƙanina da kallo ina mamakin wannan abin don sai hira yake ta zuba wa mutumin nan shi kam ƴar dariya mai kama da murmushi kawai ya ke yi. Can idanuna suka isa ga ɗan makahon nan ban san sanda na ƙara zato idanuna waje ba, ina ƙara mamakin me ya haɗa Abdul abota da wanda ya kusa sa'an ubansa ko da yake haɗuwar jini ce. Wato dai makahon nan dogo ne kamar daren sallah har ƴar doro yayi kadan saboda tsayi, sannan ƙafarsa daya bata kai wa ƙasa sai ya ɗingisa ta, daga nesa ban gano fuskar sa ba sai da suka zo dab...wani baƙin tabo ne gefen fuskarsa kamar ta ƙuna sai kurarraji a fuskar ta sa kamar feshin jikin garu(bango), a takaice dai wannan mutumin bai da fasali mai kyau ko na anini.
Da sauri na dauke ido na ba tare da na ƙara marmarin ƙara kallonsa ba, isowar su yayi daidai da isowar Salisu saurayina a cikin motarsa civic one door, ta ke murmushi ya yawaita a fuska ta har ban ji maganar da Abdul ya ke min ba akan gaishe ni da makahon nan ya ke yi ba, sai da ya taɓo ni, na kalle sa sannan na kalli makahon na amsa gaisuwar sa, ya juya yana dogara sandar sa ni kuma na karasa jikin motar Salisun da shi ma ya ke kasheni da salon kallonsa mai ƙara dulmiyani cikin kogin sonsa ba tare da haufi ko jinkiri ba balle shakka... Salisuna karfaffan saurayi ne mai tashen ƴan canji da kyau, don Allah Ya sani kyansa da farar fatar sa na daga cikin dalilin da ya sa nake son sa, and na sani son da na ke ma Salisu ta fi wacce shi ya ke min, amman still ina sonsa, don na san idan na auresa har muka samu zuri'a tare ƴaƴana za su tsallake gorin muni da Ni nake sha ɗin kuma duk da sanin son da na ke mai ta fi tasa, ina tunanin nawa son ya ishe mu har zuwa kan ƴaƴan mu...
'' aslm Alkm Yayana'' na fada cikin ƴar shagwaɓa ta, ya kalle ni da ƴar murmushi a fuskarsa '' na'am ƴammata, y kk, an taso daga mkrnt?'' ''Eh yayana'' na ba shi amsa kana na ɗora da faɗin "jiya na jiraye ka ba ka zo ba, hope lfy?'' ''eh'' kawai ya ce min ba ƙarin baya ni '' zan wuce ki gaida gida'' ''tohm gida ya ji, amman dai yau zaka zo ko?'' Na ƙara tambaya cikin wata kalar murya mai sanyi, ya kalleni kadan yace ''ban sani ba sai kin ganni kawai'' ''toh ka kula'' ya ja motarsa ya ƙara gaba bayan ya amsa gaisuwar Abdul wanda yanzu ya iso ni bayan ya raka abokinsa inda ya ɗauko shi...(imagine mutumin da nake so...babu ƴar kulawa irin ta masoya🥺) na kalli Abdul na ce mu tafi. Muna hanya ya ke gaya min wai makahon yace kina da kirki saboda ke yayata ce... ''uhmm'' kawai nace ba tare da na fahimci ma abin da ya ke fada ba, duk hankalina na kan addu'ar Allah Ya nuna min ranar da Salisu zai soni, SO...mai hana natsuwar zuci har sai ya iske abar son...
Yau ma kamar da koyaushe Fa'iza ce tsaye yau kuma da wani daban, na kasa gane wa shin Fa'iza maza nawa ta ke da niyyar aura ne?  Though, ba laifin ta ba ne laifin Hajiya Babba ne da ta bari kyaun Fa'iza ke ruɗar da su, ko da ya ke Hajiyar ma har tutiya ta ke kan cewa zamanin ta ta tara maza sunyi sha biyar, sbd kyanta kafin ta zaɓi babanmu a matsayin mijin aure, akan hakan ta ɗora Fa'iza kuma ta ɗauru sosai don yanzu ina ga samarin Fa'iza ban ma san yawansu ba, don alkawari ne, duk fita ba ta yi samari bane tayi biyu ko uku, na girgiza kai na kawai na shige gida ba tare da na kalle su sau biyu ba, Abdul ne ma ya je ya gaida ta sannan ya shigo ciki...da shigar mu ciki Abdul ya tari mamanmu da zancen makaho da sakon gaisuwar sa, itan ma biye mai tayi...
Washegari na tashi na ga ana fitar da kayan dakin Hajiya Babba alamun zata sauya wasu kenan, daman na fada muku wannan ita ce gasar gidanmu don dukkanin su suna da sana'arsu, mahaifiyata ƴar ƙamshi wasu ke kiranta don ita kam harkar turaruka ta ke da gyaran jiki, tana da beauty parlour ɗin kanta kuma ciniki ta ke bil hakki da gaskiya don yanzu mata sun koma ƴan ƙamshi da gyara, ita kuma Hajiya sana'ar kaya ta ke yi su laces, shadda da kuma materials kaya dai kala iri daban-daban, wani bin ma har kwangilar hada lefe ake ba ta, don haka suka samu damar yin gasar da kyau duk da na lura kwana biyu mahaifiyata kamar wani tunani ya ɗan shige ta don yanzu kayan ta kusan shekarar su biyu kenan ba ta canza ba yayin da Hajiya wannan ne karo na uku da za a canza bayan wanda suka yi kusan tare da mahaifiyata, girgiza kai kawai nayi ina gode ma Allah da fatan Allah Ya sa mahaifiyata ta bar wannan gasar ne da babu in da zata kai su, na wuce kicin abina daman na fita rage wa mahaifiyata aiki ne don yau ita ke da gida, ko da na shiga kicin ɗin aiki nake amman tunanina na kan abin da ya hana Salisu zuwa jiya, ba zuwa ba sako balle aike... amma duk da hakan cikin rai na uzuri nake ba sa cewa akwai dalili...
Sallamar maigidan wato babanmu ne ya fito da ni falon cikin murnar ganinsa wanda tafiya yai zuwa can ƙauye inda yake da gonakin da ƴan dabbobin sa, satin sa biyu a can sai jiya cikin dare sosai ya dawo don haka sam bamu haɗu ba sai yanzu, da ƴar sauri na ƙarasa gareshi ina mai yi masa shagwaɓa wanda shi ya bani lasisin yin sa ''babana shi ne ka je ka dade ko?" Bai bani amsa ba face zaunar da ni yayi a gefensa yana ƴar dariya ''yi hkr ƴar babanta, ga shi yanzu na dawo ai, korafi ya ƙare ko?" Na yi dariya nace ''ya wuce babana tunda ka dawo lfy, na ji daɗi sosai....ya hanya ya ka baro su?" ''Lfy lau kowa na gaishe ku" "muna amsawa, baba bari na kawo maka ruwan zafi ka sha tea" na mike shi kuma yana tmbyt ina mutanen gidan ne? Daga cikin kicin ɗin na bashi amsa ina hado masa tea set ɗin sa na musamman na fita mai da shi zuwa falon... Ina nan tare da shi muna hira cikin nishadi don babanmu yana sona sosai a cewarsa ni kaɗai ce copy ɗin sa, don haka dolen sa ya so ni... Wannan na daga dalilin da yasa nake ƙara gode ma Allah da yadda Ya yi ni ɗin sbd shaƙuwar ce sosai a tsakanina da babanmu. Can sai ga mahaifiyata ta fito daga ɗaki tana kallon mu tace "nan gaba dai idan ka dawo turata zan yi gidan Ya Binta har sai mun gan ka ya ishe mu kafin ta dawo, haba ina dalili?" "Iyye da ƴar tawa kike kishi" "aww ai ban sani ba, ka dawo jiya ba ka nemi Babangida ba, yau ma haka, yana auta guda? Sai wannan shirgegiyar kake biyewa, wacce bata sanin ta girma ko?" Dariya sosai babana yayi sbd kullum sai Abdul ya masa ƙorafin shi ne auta ba ni ba, ya kalle ni yace "af ashe fa akwai babana ko? Ina yake ne ban ma gansa ba" Abdul da ya fito tare da mamma ya fito daga bayanta yana turo baki shi nan shagwaɓa zai yi tun kafin ya buɗi baki yayi magana babanmu ya tare sa "kaga babana, baban kowa a gidan nan, kai ka haifi mai gida don haka kai ne uban masu gida, Abdullahi bawan Allah, ina uban wasu ga nawa!" Sau tari na kan yi mamaki idan babana ya fara zubo kirari yadda kuka san wani maroƙi...yanzu ma kamar kullum murmushin jin dadi Abdul yayi a dole shi ne uban masu gida... Ya taho da sauri ya shige jikin babanmu ya nai masa sannu da hny.. dariya kawai mamma ta yi ta na zama kusa da babanmu sannan nai mata Barka da fitowa sai na shige na bar su nan zaune mamma ta haɗa masa shayin yana sipping kaɗan da kadan. Idona yayi ja ina ta kokarin hada mana breakfast na ja tsaki, ba komai ya sani tsakin fa face zancen makaho da na ji Abdul ya bai wa baban mu lbr, har da cewa zai rako sa ya gaida babanmu...babanmu kam cikin farin ciki ya amsa da yana maraba da shi ko yanzu....
Da gama breakfast ɗin na fito da shi a baza babbar shinfidar da muke cin abinci a kai, sannan na je na kirawo Hajiya da Fa'iza. Peacefully muka ci abin karin muka gama, Fa'iza ta taya ni kashewa wanda hakan umurnin babanmu ne, da fitar mu Abdul ma ya fito aka bar iyayen mu su duka, don daga kicin Ni ma dakin mu na koma daman akwai mai mana wanke wanke da shara haka abinci ne kawai bata dafawa. Da isa ta daki, na tarar Fa'iza na waya da wannan saurayin ta da naji yanzu ta na cewa "haba my Qais, saurin me kake ne? Za mu yi auren nan soon, kaji?"... Ban ƙara bin kanta ba na nufi wayata ina kokarin kiran Salisu don ni kam shi ne damuwata, na kira yafi biyar bai ɗauka ba can na shidan ya kusa katsewa ya daga kamar dole "ya akai?" Abin da ya fito bakinsa kenan, na yi dariyar takaici nace "kana lfy dai ko?" Ya ce "eh lfy ta lau, akwai wani abu ne?" "Ba komai ka huta kawai" Ni na kira amman shi ke kashe min waya.... Shiru nayi ina tuno farkon haɗuwata da Salisu har muka fara son juna....

#rahmatullah
#family
#hubbifillah

_Almost there_...
Page 4 is loading...
Comment and share Please

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now