🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 27
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Radiitu billahi Rabba, wa bil islami dinan, wa bi Muhammadin (S.A.W) nabiyan warusulu_
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
"Assalamu Alaikum" Sallamar Mammy ya karaɗe falon, hakan ya tilasta masa dakatawa da maganar da ya ke yi, duk juyawa su ka yi suna kallon ta bayan sun amsa sallamar don babu alamun natsuwa tare da ita sam, sai kuma ta yi turus tana bin mutanen ɗakin da kallo har idon ta ya sauka kan Haj Shema, nan mamaki ya rufe ta, don yanzu ta ke ji a bakin Master wai har da matar Yayanta a cikin waɗanda za a rataye, shi ne ta taho da sauri don taya ɗan uwanta jimami, sai kuma ta tarar da Shema, kallon yayan tayi da tmby fal bakin ta tace "yaya to wacece na ji har da ita aka kama za a rataye?" Ya san daman hakan zata faru, sai ya tashi kawai ya jawo ta ya zaunar da ita ya ce "duk za mu ji komai a yau ɗinnan In Shaa Allah, yanzu dai kin zo a daidai ga sirikin ki na ba mu tarihin sa" ta yatsine fuska tace "sirikin ka dai, ina kan baka ta na raba auran, wallahi bana so". Shi dai Baba bai ce komai ba ya mata alamar ta yi shiru kawai ta saurara, sannan ya kalli Abdurrahman ya mai alamar ya cigaba.
Shiru yayi kamar ba zai cigaba ba don bai so a ce Mammy ta na wurin ba don ya kula kamar rashin son sa a jinin ta ya ke, yana gudun abin da zata yi idan ta ji waye shi, numfasawa ya yi sannan ya cigaba "sunan da ta ke kira na da shi sai ya zama kusan kowa ya ɗauka, wasu su ce Saifullah wasu su ce min Babangida, duk wanda aka kira ni da shi kuma amsawa nake don ina son duk wani abu da mahaifiyata ta ke so, ku yi hakuri da yadda na zo muku, amma magana ta gaskiya..." Sai ya sa hannu ya cire gilashin idon sa "ni ina gani ko babu gilashi" sotoro duk kowa ke kallon shi musamman Mammy da ta ƙura masa ido ganin yadda ta ke kallon sa sai ya saukar da kan sa ƙasa ya cigaba tun kafin ma wani yace wani abu a cikin mu "yanayin aiki na ne ya sa dole na zo a makaho don ni jami'in ɗan sandar farin kaya ne!" Ba san sanda Mammy ta isa gare shi ba sai dai muka gan ta tsaye a kan sa tana masa kallon 'na gama gano ka'. Hannun ta sa ta ɗago kan sa ta ƙura ma ƙwayar idonsa ido za ta yi magana Baba ya ce "kin ga Rahmatu zo zauna ya gama mu ji tukunnan abin da ya ɗauke mu da har ya zo mana a hakan" ba ɗauke idon ta a kan shi ba tace "cire abin da ka sa a idon ka". Babu musu ko wani gardama ya sa hannun sa cikin idon sa yana ɓare wani abu, sai ga wata ƴar kwalba zagayayye dai dai girman baƙin da ke cikin ido, wato wannan kwalbar ita ya sa a tsakiyar idon sa duk cikin ɓadda kama. Idan na ce muku a cikin mu akwai wanda mamaki bai kashe sa ba, to shakka babu ƙarya na yi kar ma a zo kaina a lbr, don ni kam ban ma san meke shirin faruwa ba, sannan ban san tunanin da zan yi ba, kawai abu ɗaya na sani idan har yanayin da na hanga a fuskar Mammy da kuma hasashe na suka tabbata gaskiya, to na sani ƙarshen farin ciki na ya zo...
Yana gama cire wa Mammy ta yi wani murmushin ɓacin rai yadda ya yi wasa da hankulan su a matsayin su na iyayen sa, ta waiga ta kalli inda na ke zaune, ai kam dama ido na na kan su ne, sannan ta juya ta kalli kowa da ke ɗakin, kamar abin kirki ta kalle shi ta ce "ka raina ma uwarka Bilkisu wayau amma ba ni ba" ta zari jakar ta za ta fice daga ɗakin ya yi sauri ya riƙe ta ya ce "don Allah Mammy ki yi hakuri ki saurare ni wallahi ba niyya ta ba ne ɓoye muku amma yanayin aiki na" "aikin ka? Har da mu ahlin ka? Ko kana tunanin za mu tona asirin ka ne ko kuma kana tunanin muna aikata wani irin mummunan abu ne, ka je tunda yanayin aikin ka ne, zan yi tunanin hukuncin da zan yanke maka" yunƙurin ƙwacewa ta ke amma ya ƙi sakin ta, kuma ƙoƙari ya ke su haɗa ido amma ta ƙi ba shi dama domin kuwa tana gangancin haɗa ido da shi to zancen fushi da shi ko yanke masa hukunci ya ƙare. Ganin dai da gasken ba sauraren sa za ta yi ba, sai ya juya ga Baba yace "baba don ka tsayar da ita, wallahi ina da dalili mai ƙarfi na zuwa a hakan" kallon sa Baba yayi, bai san mene zai ce ba amma kuma bai gama yarda wannan Babangida ba ne, sai ya tashi da kan sa ya kamo hannun ƴar uwar sa ya ce "idan rai ya ɓaci, hankali bai kamata ya ɓaci ba, kuma ni ban gama yarda wannan Babangida ba ne kamar yadda kike zargi ba, kin ga ko da ace shi ne ki bari mu saurare shi mu ji ta bakin sa". Girman yayanta ya wuce ya nemi ta yi abu ta kasa, sai ta fuzge daga hannun Abdurrahman ta nufi kujerar da ta tashi ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jijjiga shi.
Ajiyar rai yayi sannan ya kalli inda nake ganin yadda kawai na saduda da alamar ƙwalla da ya gani a idanuna shi ya ƙara masa tausayina a ran sa, daman ya san ko meye zai faru ita ce zata fi jin abin, don ita ya yaudara sosai fiye da kowa, ɗauke kai yayi sannan ya sa hannu ya cire mask ɗin da ya sa a fuskar sa, shakka babu fuskar Ya Babangida ya bayyana, ya ƙara sa hannu a bakin sa ya cire haƙoran da ya sa "ka yi hakuri Baba da yadda na yi maka ƙarya tun daga farkon haduwa ta da kai har kawo wa yau, hakan ya faru ne dalilin zargin matar ka Haj Shema da mu ke a cikin masu garkuwa da kuma satan yara, to amma duk wanda muka sani a matsayin ƴan uwanta babu wanda ya san halin da ta ke ciki, sbd yadda ta ke abin da wayau, hakan ya sa a matsayi na na wanda case ya ke hannu na na yi nawa dabarar don kamata, tun daga gayyato Qais da tayi ya auri ƴar ta wanda ainihin sunan sa Ɗan Talle ne a garin bincike na ne na gano hakan, sannan na gano Fa'iza ba ƳARTA BACE! Amma abin mamakin kuma ƴar ka ce Baba hakan ya ɗaure min kai shi yasa kawai na san yadda nayi na samu damar shigowa cikin gidan don na samu damar yin bincike na da kyau don tabbatar da abin da nake zargi. Sannan da na tsananta bincike ne na gano auran Fa'iza da mijin ta auren manufa ne da so-called mahaifiyar ta ta haɗa sbd biyan buƙatar ran ta" ɗago kan sa ya yi ya kalli ƴan ɗakin har mahaifiyar sa sai ya cigaba "na san idan na zo a yadda nake ko da na rufe fuska murya ta ita ce abu na farko da za ta tona ni a wurin Mamma da Baba shi yasa na sa wannan haƙoran robar mai canza amon murya ta idan nayi magana, sannan auran Rahma na ɗauke shi a matsayin ƙaddara ta don ban zo da niyyar auren ta ba, amma ganin yadda su baffa Ado suka watsa ma Baba ƙasa a ido ya sa na karɓi da hannu biyu, kun ji dalilin da ya sa na ɓoye muku kai na kuma Alhamdulillah haƙata ta cimma ruwa, mun yi nasarar kama dukkan mai hannu a wannan ɓarnar, an kuma yanke musu hukuncin da ya kamata da su" shiru yayi alamar ya kai ƙarshen zancen sa. Zuwa wannan lkcn na koma jikin kujera ne kawai na jingina ina ma Annabi salati a raina. Sheshsheƙar Haj Shema ne ya sa na ɗago kaina na ga kowa ma ita ya ke kallo musamman Fa'iza da ke fata da addu'ar Allah Ya sa ƙaddara ce kawai ta haɗa ta wancan azzalumar, wannan ta kasance ita ce silar zuwan ta duniya. Baba ne ya katse ta ya ce "ba kuka za ki yi ba, na so a ce na barki ki ƙara samun ƙarfin jiki kafin na tmby ki, amma ina ga idan da hali ki faɗa mana abin da muke son ji ɗin don ga dukkan alamu, ke ce zaki warware mana abin da ya shige mana duhu" Mamma da Mammy suka gyaɗa kai cikin yarda da abin da ya faɗi ɗin. Ta share hawayen idon ta tace "dole na faɗa muku ko dan share ma ƴa ta baƙin cikin da aka ƙun sa mata tsawon shekaru..." Zaman ta ta gyara sannan ta fara "kamar yadda kowa a nan ya sani, sunana Shema'u Basiru, ni kaɗai iyayena suka haifa mace, sai maza, mamana tana da wata ƴar uwa wacce suke uba ɗaya Azumi, ko da suka isa aure sai Allah Ya sa babana ya nuna ra'ayin auren babata wadda dama duk gari ɗaya suke, ashe Azumi ta jima tana son babana Basiru amma sai ta danne kamar ba komai har akai yi auren iyaye na, sosai Azumi ta yi zazzaɓin ƙarya da sunan na kewar yayar ta ne, hakan ya sa babata cikin tausayi ta nemi alfarmar babana ya bari Azumi ta zo ta zauna da su, bai ƙi sbd tsananin son da ya ke ma babata, ba ɓata lkc Inna Azumi ta dawo gidan mu da zama, zuwan ta babu jimawa Allah Ya albarkaci babata da samun ciki, cikin sai ya sa ta kyau sosai daman kuma ita ɗin mai kyau ce, hakan ya ƙara wutar tsanar ta a zuciyar Azumi. To har dai aka haife cikin nan aka samu Salihu ashe Azumi tunanin yadda zata fitar da babata ta ke daga gidan sai dai Allah bai bata iko ba, kuma ta yi duk dabarun ta don ganin babana ya mu'amalance ta da lalata (zina) amma ba nasara sai ta bi hanyar da ƙawar ta ɗaya tal ta bata, wato neman sa'a ta hanyar tsibbu, hakan kuwa ta sami nasarar samun babana yadda ta ke so har babata ta gagara gane kan sa, rabon samuna ya daidaita tsakanin iyaye na don kuwa babata tsayuwa ta yi sosai kan addu'a babu kama hannun yaro, amma fa duk haɗin kan da ta samu daga baba, Allah Ya tsare shi, bai taɓa shiga gonar da ba ta sa ba, ganin babata da ciki na sai ta koma wurin bokanta, daga nan ba a kuma jin ta ba sai bayan da na zama budurwa sai ta zo da wata budurwar ƴa ta ce ƴar babana ce, sanin bai da hujja ya sa dole ya karɓe ta, sai dai nan ma ba barin ta ta yi ba ɗaukar ta tayi suka tafi, tafiyar da ta ɗauke su tsawon shekaru, har mun manta da su, sai dai kafin rasuwar babana ya tabbatar mana da ba ƴar sa ba ce, kuma ba mu san sunan ta ba, don har suka bar gidan mu ƳAR SO ko RIBAR SO maman ta ke kiran ta da shi.
Ba mu sake ganin juna ba sai ranar da na haihu a asibiti, a cikin ɗakin haihuwar ta shigo ta same ni, bayan abin da ta hura min a fuska ban san mene ya faru ba, kawai na san ina ta ambatar 'barakallahu fiki Fa'iza' ban dawo hankali na ba sai satin can da ya gabata, abin da na aikata tsawon shekarun nan ban sani ba" sai kawai ta fashe da kuka, ita kula Fa'iza kuka, mu ma duk da ƴan matasan ƙwallan mu don tsoron Allah na gaske ya kama mu... Bayan an ɗan natsa Mammy ta ɗago ta kalli Master ta ce "back to you, ina kan baka ta na sakin ƴa ta da zaka yi, idan ka manta na tuna maka auran ka saura sati uku, don haka...." Sarƙewa ta shi ya hana ta ƙarasa maganar ta yi kai na a guje tana "sannu baby, ku ban ruwa..."Za mu numfasa a nan, don na tafi ɗebo ruwa, mu haɗu a page na gaba. Sai mu ji dalilin wannan sarƙewar. Shin meye dalilin Master ko in ce Abdurrahman Makaho ko Arc. AA Wazata za mu ce ne ma? Ko ma wane suna kuka ba shi ya ce zai amsa duka sunan sa ne, amma me ya kai shi aikin ƴan sandan farin kaya idan har yana da shaidar ƙwarewa a harkar zane? Ga Mammy ta rantse auran nan sai ya mutu tunda aure zai yi nan da sati uku. Mene zai biyo baya za a yi auren ne ko sakin mata ƴar ta za a yi kamar yadda ta dage, ko hakura zai yi da auren ya zauna da ƴar Mammy kaɗai? Ku faɗi ra'ayoyin ku.
#familyreunion
#marriage
#rivalry
#love
#romance
#comment,vote&share🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...