24

71 4 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
  *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
   Wattpad @oummarfah20

Page 24

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

   _Subhanallah, Wal-hamdulillah, Wa La ilaha illallah, Wallahu Akbar._

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

********
    Addu'o'i sosai Mammy da Abba su ka sa aka duƙufa yi babu kama hannun yaro duk akan Allah Ya ba ɗan su nasarar da ya ke nema Ya kuma kare sa daga sharrin masu sharri. Ganin yadda suka saki bakin aljihun su kawai sai aka kama addu'a babu kama hannun yaro (kuɗi ke magana). Daga nan gida suka komo suka dasa nasu addu'ar, don sun san duk addu'ar da za a yi musu ba kamar wanda za su yi masa ba a matsayin su na iyayen sa.

*******

    Duk ƙoƙarin ganin ban ɗaga hnkl ba na yi amma abin nema ya ke ya ci tura don ban yin komai sai tunanin mijina, zamowar abu ɗaya kamar wata gubar son sa ya zuba min sai na koma ina roƙon Allah Ya tsare min shi tare da ƙara masa so na a ran sa fiye da wanda na ke masa , don a halin yanzu ji nake kamar ina gab da rasa hnklna a kan son mijina, tunanin zancen auren sa kawai ma ɗazu sai da ta sa na ƙware da miyau, uhm to ranar da ya yanke auren zai yi fa? Ni kuma ina zan sa raina? Ƙila ƙarshen rayuwa ta ne ta zo, da dai na kula abin ba na ƙare ba ne sai kawai na lallaɓa na ɗau counter na fara hailala da tasbih...

*******

    Zaune ta ke a kusa da baban ta sanye da wasu irin kayayyaki kamar ba ƴar musulmai ba, Ms. Madinah ce. "Dad, wai ya batun auren mu da arc. Wazata ne? Ni fa na gaji gaskiya, kasan da ya nake bacci kuwa idan dare yayi tsabar sha'awar sa? Ai dai ka san na gaya maka ni maza ba su bani sha'awa ko, to amma ban san mene ne a jikin Wazata ba idan ina kallon shi ji nake kamar na je na haɗiye shi kawai na huta, so nake kawai a yi auren na ɗanɗana sa na ji meye ya ke taƙama da shi" ta faɗa tana ƙara kwanciya a jikin baban ta, baban ya yi dariyar jin daɗi, ya ce "Munauwara kenan! Ai bari nan da kwana kaɗan zan ɗaura muku aure da shi in ga ƙaryar tsiyar uban nasa, kin ji ɗiya ta kwantar da hnkln ki, kada ki sa damuwar komai a ran ki" ya faɗa da lallama tare da shafar kan ta. Kallon sa ta ƙara yi tace "dad ni fa kafin azumi na ke son a yi auren fa, na ji ana saura kwana hamsin azumi kamar" ya ce "ko yau kike so sai a ɗaura ai, ke ce fa". Tunanin da ya zo raina shi ne wannan wane irin ahali ne?. Allah Ya kyauta...

********

     Ko da su Master su ka isa tsaunin da majami'ar su ta ke wanda ya kasance shi ɗaya a wurin, babu gida gaba babu gida baya balle mai taimakon ka. Daga can nesa sosai suka yi parking ɗin motocin su sannan suka firfito su ka durfafi tsaunin cikin bin umurnin da Master ke ba su da hannu ba tare da yayi magana ba. Rarrabuwa suka yi kashi kashi. A tsarin, Master shi zai fara shiga da nasa tawagar, bayan kamar mintina goma ya aka sai sauran su biyo bayan sa inda sun ji shirun yayi yawa. Hakan kuwa aka yi, su ka shiga ciki suna sanɗa irin yadda aka san ƴan sanda na yi amma ban da Master shi kam tafiyar sa kawai ya ke yi kan sa tsaye ya nufi ƙofar ɗaya da ya ke da tabbacin nan ne mashigar majami'ar. Ƙofar ya kai ma bugu da ƙafa, ta ke ta buɗe ya tura kai ciki, sai dai abin mamaki ko ɓera babu a wurin, daman ya san a rina, don bai yi tunanin kama su da sauri haka ba yasan sai sun wahalar da shari'a tukunnan. Ƴar killer smile yayi sbd hango wani tarko da aka ɗana don sun faɗa, da gangan ya nufi wurin yana dube dube kamar ban san da abin ba, ai kam kwaraf sai ga shi ya faɗa cikin wani ɗakin ƙasa inda a nan ne duk ya ga mutanen da ya ke son tarar wa kam, manyan su da ƙananan su, har da Qais da Na Manzo, hhhhh ya ji an saki dariya, sai kuma dukkan ƴan ƙungiyar suka ɗauka abin da ya ba shi mamaki shi ne har da mata ake wannan lalacewar. Hnklnsa bai kusa barin kan sa ba sai da ya hango matar kawun sa na nufo inda ya ke tana wata iriyar tafiya ta ƙwararrun ƴan barikin da suka ga jiya suka ga yau, koda ya jima yana zargin ta ya zaci abin a zargin sa kawai zai tsaya, amma ya zama gsky. Kallon ta ya ke yadda ta ke kallon sa can ta ce "ko da a ke mgnr hatsabibancin ka ban san kana da tsaurin idon zuwa har nan ba, sai kuma gashi da ka tashi zuwa ba ka zo kai ɗaya ba, daman muna neman wanda zai samar mana da enough abin da muka gagara samu a gun yaran nan, sai ga shi ka kawo kan ka da kanka har cikin ramin kura hhhhh" ta ƙara fashewa da dariya sauran ma suma taya ta.
    Ko ɗar babu a ransa ya ce "idan kun isa ku sake ni, sannan sauran kada ku musu komai na san ni kuke nema da jimawa, ku min duk abin da kuke so, amma wallahi duk wanda yayi ganganci taɓa min yara wallahi sai dai ya buɗe ido ya ji sa a cikin ƙasa, kuma na san kun san ba na rantsuwa na yi kaffara ko" kallon isar da ya ke magana da shi suke su duka, suna mamakin abin da ya taƙama da shi. "Ku sake shi" suka tsinci wata murya ta faɗa, murya ta yi kama da ta wanda ya sani amma bai tabbatar ba don mutumin ya rufe fuskar sa da wani abu mai kama da yadi. Hakan ya hana sa ganin fuskar sa amma ya san tabbas ya san muryar nan. A bayan mutumin wani ne ko wata ne bai san me zai ce ba amma da alama ita ce shugabar su, don dukkan su ya ga yadda suka rusunar da kan su alamar girmamawa. Har tsakiyar su ta iso aka samar da masa da abin zama. Buɗar bakin wannan mutumin da niyyar magana suka jiyo alamun dirkowa ta katangar gidan. Da sauri ƴan matasan ƙungiyar suka fita bayan sun ɗau kayan ƙarafan su har da bindigu wanda tun sanda Master ya fara bibiyar su, suka fara shirya ma wannan ranar.
    Kafin kace me an fara ba ta kashi tsakanin ƴan sandan da ƴan ƙungiyar, sosai su ke jigata kawunnan su, ƙarshe Allah Ya ba yaran Master sa'ar kayar da gwanin su, shi kenan kuma sai nasara ta zama ta su, don daman da wannan ɗayan suke takama, to an harbe shi a kafaɗa da ƙafar sa babu damar harbi kuma, su ma sauran ganin hk, sai su ka fara neman hanyar guduwa, sai dai kafin su yi yinƙurin matsawa sauran team ɗin da ke waje sun shigo, nan suka kama su suka yi waje da su zuwa cikin wata babbar motar da suka zo da ita don kwasar su.
    A can ciki kuma jin shiru babu alamun harbi ko ihu ya sa mutum leƙawa waje, ai kam da sauri ya dawo yana faɗar abin da ke faruwa. Nan suka miƙe har da shugaban su, nan ta sa a kwance Master a nan ne ya gane mace ce sbd murya ta da ya ji. Kwance shin aka yi kuwa, ta sa suka kawo shi gaban ta "ina ka kai min jama'a ta?" Ta tmby shi, bai amsa ba, sai da ta nanata sau uku bai tanka mata ba nan zuciya ta ɗebo mutumin da su ke tare yana zuwa ya shaƙo shi akan sai ya faɗi in da ya kai su, amma ko ɗar Master bai yi ba sai ma wani shegen murmushi da ya ke sakin ma mutumin, ai kam hakan ya fusata mutumin ya ya jefar da Master gefe ta kalli ƴan wurin ya ce "ku fitar masa da jini har sai ya faɗi inda ya kai su" duk wannan abin da ake, Master ko yinƙurin ramawa bai yi ba, suna fara dukkan sa suka jiyo jiniyar ƴan sanda, nan suka zabura za su gudu, sai dai kafin su kai ƙofa, Master ya yi wani irin tashi ya jawo shugabar ta su ya ɗaura mata wuƙa a wuya da gargaɗin suna ƙara motsawa zai yanka ta, sun zaci wasa ne sai da wannan mai mayafin ya fara takowa zuwa gare sa, yana matsowa, Master ya sa wuƙar nan ya karci kafaɗar ta, sai ga jini ya na bin jikin ta. Nan duk suka dawo hnkln su, yana riƙe da ita, babu damar ƙwacewa, ya ja ta wurin kujerar ya zauna "duk abin da ku ka yi ɗazu, ban tanka ba, to yanzu lokaci na ne, duk ku dawo nan" ya faɗa ya na nuna gaban sa. Ba su motsa ba don ba su da niyyar bin umurnin sa, sai da ya kuma wuƙar a gefen cikin ta za yanka, nan suka taho suna kallon fuskar shugabar su, uwargijiyar su, wacce ke ta kokarin yin siddabarun ta na tsafi amma abin ya ci tura, yadda suka ƙura mata ido ne, ya sa Master hasashen wani abu na faruwa, ai kam ya duba hk, ya ga yadda idanun ta suka juye, babu baƙin sai farin kawai tana ta motsi da bakin ta. Ba tsoron komai ya dage ta bayan ta, ya tsinka mata mari, sai ga idanun sun dawo yadda su ke. Ta ɗago ta kalle shi, shi ma ya kalle ta ya ce "kuna tunanin ban shirya ba na zo nan, yanzu ni wannan abin mai shan jinin mutane na ke son ku nuna min" kallon sa ta ke, ta ji labarin hatsabibancin sa amma ba ta yi tunanin ya kai hk ba. Ganin kallon da ta ke masa ne ya sa ya ce "oh kada ki damu kawai ganin girman sa ya kai yanzu zan yi, don yaran da kuka kashe zuwa yanzu ya ci ace girman sa ya girmi wannan gidan" sakato suka yi suna kallon yadda ya ke abin sa babu tsoro ko shakka, da dai ya kula ba za su tanka mai ba sai ya kalli shugabar ya ce "ɗan gwada murza zoben mu gani ko za mu ɓace yadda ake yi a littafai da finafinai" kallon sa ta yi cikin sarewa da miƙa wuya tace "yanzu mene kake so yi?" Ya kalle ta cikin dariyar shaƙiyanci ya ce "yauwa ƴar gari, kin fahimci inda na ke mu kai" ya faɗa ya na ƙara shaƙe wuyan ta da hannun sa har sai da tai ƴar ƙara "so na ke na ji bayan ke, waye babban mai bada umurni a nan?" "Ni ce shugabar su, daga ni babu ƙari, sannan zan roƙe ka wata alfarma... Ka bar mu, ni kuma nayi maka alƙawarin daga yau za mu bar garin nan gaba ɗaya, kai idan ma ƙasar ne ka ke son mu bari ba zaka ƙara jin ɗuriyar mu ba" ya ɗan yi shiru cikin gamsuwa da abin da ta ce ya gyaɗa kai yace "kin tabbata idan kuka tafi ba za ku dawo ba har ku mutu? Idan ke kin yarda sauran ba su yarda ba ai" ya faɗa yana kallon sauran yadda suka yi tsuru tsuru ganin yadda uwargijiyar su ta saduda sun san ta su ta ƙare, kafin ma ta yi mgn sun ce sun amince. Jin haka sai Master ya ce "ya za a yi na tabbatar idan na sake ki ba za ki min wani mugun abin ba, dubi yadda yaran ki su ka ƙura min ido kamar za su cinye ni" da ido ta musu alamar su fita. Haka suka juya su ka fice. Cikin gidan shiru kamar ba yanzu aka gama cin wasan rai da ƴan sanda ba. Suna fitowa duk su kai cirko cirko kamar ace musu arr su fece da gudu.
    A ciki kuwa Master da idon shi ya ba ma yaran shi umurni, nan suka juya baya suna sake bincika ɗakin zuwa ɗakin saman, ai kam sai ga tarukucen kayan tsafe-tsafen su nan birjik sun fito da su. Master ya sake ta ya ce "ki yi sauri kafin backup ɗin da na kira su iso"  da hanzarin gaske kuwa ta nufi matakala zata hau sama, tana ɗaga ƙafa ta ci saukar harsashi a ƙafar ta, ta na juyowa ta ga Master riƙe da bindiga ya ce "oops suɓutar hannu ne sannu" kafin ta yi wani motsin ta ji ƙarar shigowar motoci da kuma ƙarar durowa, a zabure ta yo kan Master sai dai kafin ta iso yaran sa sun hana ta isa gare sa, hakan yayi dai dai da shigowar sauran yaran sa da ya bari a hq duk a cikin shirin sa akan su ke za su kawo ma sa back up. Nan aka kame sauran matsafan har da Alh. Sammani wanda shi ne ya rufe fuskar sa, ganin sa ya sa Master murmusa wa ya musu alamar su ta fi da su inda ya tsara za a ajiye su har sai an gano mai fitar da sirrin su tukunnan, sai a miƙa su hukuma. Nan aka fice da su zuciyoyin su cike da tsanar Master tare da alwashin ɗaukar fansa, duk daren daɗewa.

*********

    Daga sallah ban yi komai ba, har magriba, amma shiru ba mijina ba labarin sa, tun ina tunanin abin wasa ne har na fara fita hayyaci na da tunanin ko lfy? Waya ta na ɗauka na kira shi har ya ƙaraci ringing ɗin sa ba a ɗaga ba, sai can har na fidda rai sai ga kiran sa, na ɗaga sauri "Aslm Abiey ina ka ke?" Ajiyar numfashi ya ajiye wacce na ji fitar ta har raina don sosai ya ke a wahalce "Bae yi hkr, kin ji ni shiru ko, riƙe ni su ka yi wai ni ma sai sun bincike ni sannan za su sake ni, na so su ban wayata na kira ki amma hakan ya gagara, yanzu ma wani bawan Allah ne ya ba ni wayar, bayan ya ga kiran ki...ya jikin ki, da sauƙi ko" cikin tausayin kai da na abin da ka ke so na ce "uhm.... ynz cikin sauron zaka kwana?" Ya ce "Toh ya zan yi, sun ce sai gobe tukunnan, kada ki damu na saba ai in dai cizon sauro ne. Kin yi abin da na ce kiyi da ruwan?" Na ce "eh" "da sauki sosai yanzu?" A kunyace na amsa "uhm" maganganu na fara ji a background ɗin da sauri ya ce "sai da safe ki ci abinci ki kula da kanki, zan dawo gobe, In Shaa Allah" ɗif ya kashe wayar. At least na samu sa'ida tun da na ji daga gare sa. Nan nayi abin da ya umurce ni kamar yana nan har zuwa sanda na ji bacci, na kwanta da ɗokin ganin wayewar garin gobe. (Asuba tagari bae ɗin Abiey)

*******
    Da magribar fari baba ya dawo daga tafiyar da yayi ta kwana biyu kamar yadda ya faɗa tun kwanan baya. Yana dawowa bayan gaisawa da suka yi da Mamma ya nufi ɗakin Haj. Shema sai dai ɗakin a rufe, ya fito yana tmbyr Mamma inda ta ke ta ce bata sani ba. Yana tsaye yana mamakin inda ta je ba ta faɗa masa ba, Fa'iza ta fito daga ɗakin Mamma da mamaki baba ke kallon ta yace "Fa'iza?" Ta mai sannu da zuwa tare da gaida shi, ya amsa yana tmbyrt yaushe ta zo? Nan ta shaida masa tun jiya ta zo kuma Haj tun jiyan bata nan. "Ikon Allah" baba ya faɗa cikin jinjina girman abin da zai fitar da Haj har ta kwana a waje ba ta faɗa masa ba. Kauda tunanin yayi da tmbyrt "mijin ki fa, halan tfy yayi?" Ta ɗago ido cike da hawaye ta girgiza kai, cikin damuwa baba yace "zo zauna faɗa min mene ne, faɗa ku ka yi da mijin ki ki ka zo gida?" Nan ma girgiza kai ta yi, ya ce "to faɗa min mene ne?" "Baba...Haj da Qais suna tare" kallon ta yayi "suna tare kamar ya? Ban gane ba, yi min bayani mai gamsarwa"  ta share hawayen ta za ta yi magana kenan kira ya shigo wayar Baba, baƙon numba ne ya ɗaga da sllm, a can ɓangare aka amsa tare da cewa "kai ke Alh. Maizare mijin Shema'u Basiru?" "Eh ni ne" ya amsa "idan Allah Ya kai mu gobe, ka zo ga matar ka ta farfaɗo tana son ganin ka" da mamaki baba ke tmby "wace ce ta farfaɗo? mene kuma ya same ta? A ina ta ke?" "Ga ta nan a asibitin Mailafia na garin Kaduna" "KADUNA?" ....

Kaduna? Mene ya kai ta Kaduna? Guduwa ta yi daga wurin ƴan sandan ko me? Mu hadu a page na gaba In Shaa Allah, amma kai na fa ya fara kwancewa. Me kuke tunani? Comments below.

#sisters
#victims
#sirri
#lovebattle
#comments
#voteandshare

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now