14

34 2 2
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
  _*RAHMATULLAH*_

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
    Wattpad @oummarfah20

Page 14

   _Allah kada Ka bar mu da iyawar mu_.

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

  _Wannan lbrn tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

********

   Interrogating ɗin sa suka yi sosai amma ya ƙi furta koma, duk uƙubar da su ke gana masa ya ce bai san komai ba, duk juyin duniyar nan zancen ɗaya ne bai sani ba.
   Waya suka ɗaya suka kira Master su ka bashi feedback daga cikin wayar suna jin murmushin sa, yace ku kulle shi ku fito zan turo muku address ɗin da aka kai yaran ina fatan mu kama babban su a wurin. Daga hk ya kashe wayar, kallo suka bi juna da shi, hatsabibanci Master wani lkcn tsoro ya ke basu, ya kan yi komai don cimma nasara, ya akai ya san address ɗin oho?     Ahmad ya kalli abokin aikinsa Ashir ya masa alamar su je don dama wayar a speaker ya sa ta don su ji tare.   Kulle Kwaɗo suka yi kamar yadda ya ce sunansa sannan suka fice don cika umurnin shugaban su.

**********

Da salati na farka sbd mummunan mafarkin da nayi a kan mijina, wai yana tafe da sandarsa, sai ga wasu kalan halittu sun dunfaro inda ya ke zasu cinye shi ko kafin na kai masa ɗauki... na farka. Ji nai hnkln ya tashi na gagara natsuwa gani na ke ko me ke nan, toh mijina na cikin wani halin ha'ula'i, bani da wata mafita face tashi da na yi na ɗauro alwala na fara yin nafila sannan na miƙa sallahr da lkcnsa ke nan, sosai nayi addu'o'i ma mijina kan Allah Ya tsare min shi da tsarewarSa. Na jima sosai kafin na jiyo ƙarar ringing ɗin wayata wanda ynz ƙaramar Nokia ce na ajiye babbar, ko da na duba Mamma ce mai kiran na ɗaga da sallm na gaida ta ta amsa, nan ta ke sanar da ni ɗazu ta aiko Abdul amma ban buɗe ba, daman wasu ƴan islamiyar mu ne suka zo ganin ɗaki na, suna zaune nan falon gidan, shiru nayi ina tunani iya sanina babu abin da ke haɗa ni da ƴan mkrnt mu, tsakanina da su sllm ce kawai amma wai sun zo ganin ɗakina, ni nasan lbr ne ya kai musu shi ne suka zo su min dariya, jin nayi shiru yasa Mamma kashe wayar tana cewa ga Abdul nan zai kawo su, na sauke wayar daga kunne na tashi, daman akwai wata igiya da aka sa min da labulaye  wacce ta raba ɗakin biyu ban taɓa zuge labulen ba don ba wanda ya taɓa shigowa, yau dai dole na ja na rufe katifar da ƙofar bayin sai inda na ke sallah, sai ya zamana kujerar da tv da kicin suna nan cikin kamar falon kenan... Ina gama zugewa na jiyo knocking, na tashi na buɗe, Abdul ne a gaba sai su biyu wanda ban taɓa san su amma na basu hny suka shigo har Abdul, suna shiga na rufe ƙofar na shiga na same su zazzaune aka kujerar, Abdul ya gaishe ni na amsa suna muka gaisa na tashi na kawo musu ruwan sha da kayan fulawa na biki da aka mana, nawa nan don babu masu ci, bayan na kawo na zauna na bar su akan zan shiga kicin in zo, nayi hakan ne don na basu damar kallan da shigo tarar suna satan kallo, ai kam nan suka buɗe ido suka gama kallon ɗakin, da na daidaici sun gama kallon sai na fito na zauna nan kan Carpet ɗina sannan nace "kuyi hkr, amma ban gane ku ba".     Kallon juna su ka yi sannan ɗaya ta ce "ni ƙanwar ƙawar Fa'iza ce jiya na rakata gidan Fa'iza shine na tmbyi inda kike tace ai kina nan gida, yau kuma sai ga wannan ajinku ɗaya a islamiyya ta zo gidan mu ta ke min zancen ki na ce na san gidanki, shi ne ta ce na rako ta, ta ga ɗakinki, shi ya sa muka zo" ta yi shiru alamun ta gama zancen ta ba, da mamaki na ke jin wannan salon gulmar da neman zancen yaɗawa, na waiga na kalli wacce aka ce ajinmu ɗaya, ni dai ban santa ba, ganin kallon rashin sani na ke mata sai tai ƴar yaƙe ta ce "ba lallai ki gane ni ba, a ajin Mlm. Musa nake nasan kin san Zulfa Sagir, to ni ce" na kalle ta na gyaɗa kai wato a 'B' ɗin ajinmu ta ke kuma kowa na mkrnt ya san Zulfa idan baka san fuskar ba kasan sunan kamar ni ban san ta ba amma na san sunan don radiyo ce mai jini duk wata zance daga bakin ta yake fita, ni ma kuma nasan yanzu ban tsira ba... Daga nan shiru ne ya biyo baya, ana haka na jiyo sllmr Abdul makaho wato mijina, na amsa ya shigo da sauri suka ɗaga kai suna ƙare masa kallo don tabbatar da zancen da suka ji yana yawo a gari, da saurin murna Abdul ya tare shi ya rungume yace "na zo baka nan"  ya shafa kanshi na yace "eh aboki, na je nema ne, yaushe ka zo?"   Yace "ƙawayen anty Rahma ne suka zo na rako su, amma baka nan".   Makaho ya nufi wurin katifar yana cewa "uwargidan baƙi aka yi ne?" Gudun kunya ta shi ya sa na amsa sannan na tashi don masa jagora kada ayi abin kunya tunda yau nasa labulaye, sai dai abin burgewar hannu yasa ya fara duba inda zai zauna sai ya ji labule, zai ɗaga ya shige kenan suka gaishe shi, ya juyo inda ya ke jin muryarsu ya amsa fuska ɗaure, wanda ban taɓa gani ba, iya sanina shi mutun ne mai fara'a sosai amma yau naga saɓanin haka, daga amsa lfy ya juya ya shige ta cikin labulen, ban yi yunkurin bin sa ba, don na san yana buƙatar sirri ko shiga bayi, sai dai abin mamaki ji nai yana faɗin "Bae.... Bae zo kiji" duk ban kawo ni ya ke nufi ba sai wacce ta amsa Zulfa ce ta ce "Rahma ba ke yake kira ba, ki je mana mu ma wucewa za mu yi" ban ce komai ba na tashi na shiga ciki, yana jin motsina ya ce "yauwa Bae ɗan ban ruwa da abin taɓawa kin ga da yunwa na dawo" na kalle shi ina mamakin Bae ɗin da ya ke kirana da shi sai na ce "gsky ban yi abinci ba fa"   "ko ma mene bani zan ci ai laifi na ne da ban faɗa miki yau zan dawo ba daman surprise zan miki, duk da ma kamar baki yi murnar ganina ba ko ƴar rungumar nan ta oyoyo babu....uhmm samo min abin da zan sa a baka kawai idan anjima sai nayi ƙorafi da kyau, je ki yi sauri pls"   mamaki neman kashe ni ya ke yi, ban ce komai ba na fito sai dai abin mamaki gani nai Zulfa na ƙawar ta sun yi kasaƙe suna sauraren tattaunawar mu amma Abdul ya fice, gani na yasa suka miƙe suna inda inda "uhmm daman fitowar ki mu ke jira mu yi sallama, mu je Saima" nan ina kallon su suka fice ni kuma nayi kicin don nemo masa abin da zai ci ɗin.

******

    Suna fita Zulfa ta taɓo Saima tace "ke tashe ni idan bacci nake" ai ko Saima ta dage ta danna mata tsunguli "kin yarda ba bacci ba ne?" Tace "na yarda, kin ji makaho da salon so? Wai Bae? Oh Ni yau Zulfa naga abin da ya fini!" Cike da mamakin wannan abin suka ci gaba da tfy har Saima tace "ni kam mene ne ma'anar Bae ɗin ne?" "Before Anyone Else, ko Before Anyone and Everything" Zulfa ta bata amsa....

********

   Koda na kai mai ruwan sha da kayan fulawar da nake da su, sosai ya ci sannan ya shiga bayi ya watsa ruwa, sannan ne ya ke gaya min hanya ce ta biyo da shi nan shi ne ya shigo ynz zai koma. Kaya ya canza ya min sllm ya fice kuma akan sai zuwa jibi zai dawo, nai masa fatan tsarewar Allah da nasara ya fice ya bar ni da juya kalmar _*Bae*_ da ya kira ni da shi...

*******

  Sun yi nasarar kama wasu biyun bayan kwaɗo wanda suna nan kira ya zo musu akan zai faɗi gskyr abin da ya sani, wannan yasa suka bada umurnin a buɗe a bashi abinci mai kyau kafin su zo, basu samu isa ba sai a washegari bayan sun tseratar da yaran da aka sace, sun kuma sada su da unguwarsu sannan suka nufi headquarters ɗin su... Suna isa tun kafin su zauna Master ya kira su akan su binciki kwaɗo tukunnan biyun kuma a kai su baƙin ɗaki. Hakan ko aka yi suka kulle su sannan suka nufi wurin kwaɗo, sun tarar an kawo masa abinci yana ci don hk suka dakatar ya gama ci, sai dai me? Yana gama ci ya sha ruwa kuma shi kenan ya faɗi sai bacci, sun zaci ma mutuwa yayi amma sai suka ga bacci ne mai ƙarfi ya ke yi, mamaki ya kama su suka nemo ruwa suna zuba masa amma maimakon ya farka sai ya ƙara gyara kwanciya ya ci gaba da baccin sa, ana haka chief ɗin su ya shigo yana tmbyr mene ke faruwa? maida masa abin da ya faru suka yi, ya matsa kusa da kwaɗo ya kai hannunsa hanncin sa tsawon kamar mintina biyu sannan ya cire, ya tashi daga kansa ya ce "idan ya tashi ku kira ni, ni zan yi interrogating ɗin sa da kaina" "okay Sir" suka amsa masa ya fice. Fitar sa da kamar mintina biyar su ma suka fito bakin ƙofar suna ƴar hira sama sama tare da jiran Master domin ya ce su jiraye shi kada su matsa ko nan da can ne...

   Sai dai kash! Ko kafin ya ƙaraso mai aukuwa ta auku, sai gawarwakin su aka gani su duka ukun... Abin mamakin shi ne babu wanda ya shiga ɗakunan da suke, infact kwaɗo kawai aka san da zaman sa a nan, amma kuma ynz dukkan su ukun sun mace....

Mene kuke tunanin ya faru? Share your thoughts....

#rahmatullah
#baenamakaho
#master
#kidnappingandassault
#hubbifillah.

Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now