🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*RAHMATULLAH*_.Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 13
_Yaa Wahaabu Hablana_
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Wannan lbrn tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
****** Kwanan makahon mijina huɗu da tfy ya kirani akan zai dawo amma a ranar zai koma, komai ban ce ba bayan toh na kashe wayar. Can bayan azahar ya iso, da sallama ya shigo ya samu wuri da lalube as usual ya zauna, bayan sannu da zuwa ban ce komai ba sai shi ne ya tmbyi lfyta da gidan, alhmdlh kawai na ce na tsuke bakina. Ganin ban da shirin ba shi komai ya sa shi tmby "Uwargida nace ba abinci ne? idan babu abincin ko ruwa a bani na ɗebo gjy". Na kalle shi a raina ina raya wani ya saka? na dai tashin na kawo masa ruwa. Ban masa tayin abinci ba don ni ranar ma taliya nayi da mai da yaji, sosai ya sha ruwan kuwa yayi hamdala. Sai kuma na kalle shi na ce "ni taliya da yaji ce da ni ban san ko za ka iya ci ba?"
Na tashi na ɗauko masa, da laluben da ya saba ya ci sau ɗaya, ya ce "Oh Ni ba ɗan gata bane, amma ace in yi tfy in dawo ba a yi min tarbar mai kyau ba, an haɗa ni da taliya da mai da yaji, uhmm ba komai"
Kallo wannan ban masa ba, jin ban ce komai ya kuma takalata da zance "amarya baki tmbyi inda na je ba" bai jirayi amsa ta ba ya cigaba da cin abincinsa sai kuma kamar wanda aka tsikara ya ɗago daga cin abincin ya kalli ɓangaren da ya ke iya jiyo muryata yace "..ni kam na tmby ki mana"
Nace "Allah Ya sa na sani". "A ina ƴar uwarki ta haɗu da mijinta ne, muryarsa tana min kama da ta wani da na sani" "ni ma ban san inda suka haɗu ba" na amshi amsa. Ya gyaɗa kai, can kuma ya ce "amma sana'ar me ya ke yi ne, don wanda na sani ɗan kasuwa ne" tmbyyn nasa sun fara isa ta don haka nace "me zai hana na raka gidan na su ka tmby? Ko in kira maka ita Fa'izar a waya ka tmby ta" "Allah Ya baki hkr" "Ameen " na tashi na shige bayi.... Kafin na fito har ya gama ci ya ɗauki plate zai kai kicin sau ɗaya na kalle shi na cire kai tare da kabbarta sallahr la'asar da aka kira. Ina jin motsin shigar sa bayin da fitar sa na kuma san alwala yayo ya fice masallaci....
*******
Wani irin girgiza dakin ya ke kamar ana jijjige tushen ginin, duk tsoro ya kama su, tunanin su wani mummunan abu ya faru ko zai faru amma shugaban nasu ko a jikinsa, hasali ma abu ya ke sha cikin kwarya... Can bayan wani lokaci girgizar ta tsaya, sai sannan hnkln su suka natsa har suka tmbyi shugaban dalilin faruwar hkn? Ya kalle su ya ce "dodo na fushi da ku, sbd hk gab asirinku yake da tonuwa, tunda kun daina biyan masa buƙata, shi ma zai bar ku da halin ku, wannan duk warning ce ya ke muku, idan kun ji....kun tsira, kuna iya tfy, daga yau babu taro har sai kun cimma burin dodo" daga hkn ɓat ya ɓace daga wurin, cikin sanyi da mutuwar jiki duk suke fitowa daga wurin kowa da burin sa a ransa ta neman mafita kawai....
********
Ana idar da sallah ya shigo ya ɗauki wata riga ina gani ya shiga bayin ya watso ruwa ya canza kaya ya fito ya min sllm akan zai tafi nema...na mai addu'ar nasara ya fice na bi ƙofar da ya fita da kallo..... "Ina son sanin tarihin sa, da dalilin makantar sa da garin su....infact, komai na ke son sani game da shi". Shi kuwa makaho yana fita ya zarce gidan aikin sa... Da isar sa ya tadda gidan kamar da baƙi amma bai gigin wuce iyakar sa ba, kuma ba ya jin me suke cewa, don hk ya cigaba da zama a wurin ya na ma Annabi salati....
*******
Can cikin tsakiyar dare ya fito da wata ƙwarya yayi bayan gidan da shi... Yana daga tsaye yana ƴan surutun tsibbun su kafin kace me? abin da ke cikin ƙwaryar ta ɓace kamar iska, ya ɗauki ƙwaryar sa ya koma ciki hankalinsa kwance ganin ya tasar ma cimma burin dodo...******
A hanzarce suke komai ƙoƙarin su su isa wurin da Master ya ce musu akan za a kai farmaki wato unguwar yalo. Abin mamaki amintattun sa guda biyu yace su ɓadda kama su je can ɗin sannan kada kowa ya san inda za su je, don Master so ya ke da gaske ya san waye yake fitar da sirrinsu waje?. Ɗayar wayar hannunsa ce ta yi vibrating alamar kira, bai ɓata lkc ba ya ɗauka don idan kira ya shigo wayar baya tsayawa tunani kawai ya ke ɗauka don issues na family affairs ɗin shi ne kawai ake kiran sa da wayar.Ya ɗaga wayar ya kara ta a kunne tun kafin yayi mgn ya jiyo muryar yaronsa Zailani na mgn "Master akwai mtsl fa" bai ce komai ba ya cigaba da sauraron sa jin shiru ya sa ya cigaba "yallaɓai ne da hjy suka yi zuwan bazata wai sun gaji da jira sai ka je, ynz hk suna a part ɗin su na gidan ka, amma suna ta tmbyr dalilin canza komai na part ɗin Ms. Madinah, ni dai ban ce musu komai ba tukunnan, ina jiran jin ta bakin ka" ajiyar zuciya mai nauyi sosai ya sauke sannan ya ce "komai suka tmby kace baka sani ba, zan shigo zuwa gobe da yamma ko jibi, ynzn aiki ya ɗan rufe ni ka kula da su, har Bibidy aka zo ne?" "Eh Master" "toh sai na zo" daga hk ya kashe wayarsa ya na ɗan dafe goshinsa da hagunsa cikin tunani kafin ya watsar ya cigaba da abin da ya ke yi kafin kiran ya shigo...
*********
Ko da suka isa unguwar ɓadda kama suka yi ɗaya ya zo da keken guragu ya shigo ta farkon anguwar shi kuma ɗayan ya zo a kuturu ya shigo ta ƙarshen anguwar duk suna sanye da wasu yagalallun gajiyayyun kaya, sosai suka ɓadda kama ba za ka taɓa tunanin sun san me ake ce ma mkrnt ba.
Zuwan su kuwa kamar da mintina ashirin zuwa talati...sai ga ɓullowar wata baƙar sienna da tinted glass duk a ɗage, isowar motar da tsayuwar ta yayi dai dai da fitowar wasu yara almajirai bayan su wani yaro ne wanda babu alamun wahala ko gajiya a tare da shi, don akwai banbanci yanayin suturar jikinsu. Ganin yaran yasa mutum biyu daga cikin motar fitowa tare da kiran yaran wai za su basu sadaka, daman yunwa ta gama da yaran don hk babu wani tunani suka nufi motar, da zuwa wurin su ka yi yunƙurin tura su cikin motar, da hanzarin gaske yaran Master su ka kawo musu cafka, ganin an yo kansu da gudu ya sa mutanen nan tada motar don guduwa, sai dai ba su yi nasarar tfy da almajiran ba sai wannan yaron da ke bayan su har kwanon hannunsa alamar aiken sa aka yi...
Ɗaya cikin mutane biyun yayi nasarar faɗawa motar, amma ɗayan garin sauri yayi kuskuren taku, ya faɗi, su kam ganin za a kama su kawai sai suka ja motar su ka yi gaba tare da barin ɗayan a nan wurin wanda babu ɓata lkc yaran Master su ka yi nasarar kama shi.Daga nan ofis suka wuce da shi don yi masa ƴan tmbyy....
Wow!
Next page is loading.....#vote
#comment
#share
#kidnap
#master
#marriagelife🌼🌼 Oumm Arfah🥰
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...