🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 23
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Subhanallah, Wal-hamdulillah, Wa La ilaha illallah, Wallahu Akbar._
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
Haj. Shema'u kam tun fitar da a jiya da safe bata dawo daman baba baya gari don hk sai ta kwana can tana harkar ta ba tare da tunanin komai ba. Wannan ya sa Fa'iza kwana a ɗakin Mamma a kan gadon Mamma ɗin kuma. Don tsoro ne sosai a ran ta shi ya hana ta zuwa tsohon ɗakin na su. Kwana ta yi tana mamakin irin uwar da Allah Ya bata, shi yasa ashe ko an faɗin laifin Qais ba ta yarda ashe halin su ɗaya ne. To amma me yasa ne Haj ta yarda ta aurar da ita ga ɗan ƙungiyar asiri masu illata yara ƙanana, ba ta mantawa sanda ta faɗa mata ta baya Qais ke zuwan mata, buɗar bakin Haj sai cewa tayi tabbacin bai taɓa sanin mace ba kenan, kada ta hana shi kanta a hnkl zai gane hnyr, kuma kada ta faɗa ma kowa don sirrin mijin ta ne. Da haka ta yaudare ta ta hana ta faɗa ma kowa abin da ke faruwa sai dai ita da ta ɗau matakin hana shi kanta. Kusan raba dare tayi tana waɗannan tunane tunanen ba tare da ta san lkc ya ja, kuma duk motsin ta Mamma na jin ta don ita bata da nauyin bacci, ganin abin ba mai ƙarewa ba ne sai Mamma ta tashi ta shiga bayi ta yi alwala ta fito ta kabbarta sallah, ganin haka sai Fa'iza ta ga dacewar ta nemi taimakon Allah don Shi kaɗai ne yanzu mai taimakon ta. Hakan kuwa ta tashi ta yo alwala ta fito ta kabbarta na ta sallahr. Ba su yi bacci ba sai da su ka yi sallahr asuba wanda da ƙyar Fa'iza ta iya yin sa don wani irin gajiya ne da bacci suka rufe ta sosai, don haka azkar ɗin ma akan gadon ta kwanta tana cigaba da yi wanda ko kafin ta gama bacci ya ɗauke ta...
*********
Ban san da yare ko harshen da zan kwatanta muku daren jiya ba. Daren da na fita daga sahun budurwa na koma sahun MATA, matan aure. Jinjina ga dukkan mata, don idan na ce muku daga daren jiya zuwa yau na roƙi Allah dama namiji ya yo ni ya fi sau shurin masaƙi. Na ƙara tabbatar da wannan karin maganar ta Hausawa da suke cewa "bar raina allura, ƙarfe ce" ni ynz a yadda na ke jin azabar da na sha, gani nake kamar sai an ɗinke ni kamar ƙwarya, don ban muku ƙarya ba idan nace ina jin iska na shiga da fice ta wurin sannan gani na ke ko bayan gida zan yi sai dai ya faɗo kawai, yadda nake jin wurin ya haɗe da baya (tabɗijam! Mata sun ji jiki🤣🤣😂).
Harara kuwa kaɗan ne idanuna ba su faɗo ba ko ruwan cikin su ya ƙare ba sbd hawayen da na yi ta fitar wa babu kuka tsabar azabtuwa. Dukkan wani taimako da ya kamata ya min, makahon mijina da ya zame masa dole shi ɗin ne yayi, taimakonsa ɗaya akwai ruwan zafi a famfon banɗakin, tun ina dauriya har dai na gagara na fita cikin ruwan. Da ƙyar dai da siɗin goshi aka yi wankan farkon tun cikin dare na koma bacci da ƙyar, sai dai ban tunanin na yi awa biyu da bacci, laluben sa ya tada ni baccin wahalar da na ke yi, ba ɗagin ƙafa yayi abin da ya ke ganin shi ne ya fiye masa. Azaba kan azaba. Wannan karon ne ya ɗanɗana kuɗa ta, don na shaida na zama mace. Amma fa na tabbatar na bar masa abin da zai dinga tunawa da wannan ranar shi ma. Ai jiki bai fi jiki ba 😏.
Baccin da na yi cikin natsuwa ita ce ta bayan asuba, don a nan kan Carpet ɗin na kwanta ban ma hau katifar ba balle a ce ni na kai kaina. Ban farka ba kuwa sai misalin shabiyu saura, ina buɗe ido na tarar da kwanukan gidan mu, amma Mal. Abdurrahman ba ya ɗakin. Da ƙyar na tashi sai kuma na fara tunanin yaushe na tashi na kan katifar don ban tuna ba. Ina cikin addu'a da miƙa sbd ciwo da nauyin da jikina na min na ji ƙarar waya ta, ko ban duba ba na san mijina ne don na jima da canza mai ringtone. Kai Zuciya? Sai dai a bar ta da abin da ta ke so. Duk uƙubar da bawan Allah nan ya gana min za ku yi mamakin idan kuka ga yadda fuska ta ta wadatu da farin ciki da annashuwa, na ɗaga wayar a sanyaye da sallama murya ta can ƙasa sosai "Aslm Alkm" "Wslm Alkm wa Rahmatullah wa barakatuh, matar Abdurrahman" ina iya jiyo natsuwar da ke cikin muryarsa, bai jira ba ya cigaba "hnkl na ya kasa kwanciya fitar dole ce ta kama ni, maigidan da nake gadi ake zargin sa da satar yara shi ne ƴan sanda suka kira ni na faɗi abin da na sani, ki yi hkr, ina gamawa da su zan dawo gare ki kin ji Bae" ya kuke ganin fuska ta zata kasance? Tuni na manta ciwo na yi wani juyi mai ƙarfin gaske don nishaɗi ai kam na fama ciwo ba shiri na sa ƙara take ya ruɗe "mene ne? Jikin ne sannu ko duk laifi na ne ko? Sannu, don Allah ki ƙara shiga ruwan zafi kafin na zo kin ji?" "Uhm" kawai na iya cewa. Ina son tmbyr sa, amma ban son magana ma "na fito zan tafi ina ta tunanin abin da za ki ci sai na ga Abdullah da abinci wai Haj ƙarama ta aiko da shi kunun tsamiya da ƙosai, shi ne na ajiye miki, pls ki ci kin ji, ki shiga ruwan zafin ga ƴan sandan nan su na nema na, zan kuma kiran ki kin ji, ki kulan min da kan ki" ƙit ya kashe wayar sai dai kafin na ajiye ya kuma kira ina ɗagawa kawai na ji "ki sani ko me ya faru ko zai faru Ina Son Ki, ko ban dawo gare ki ba, ki sani za ki zama a raina har abada" bai ma bani damar magana ba ya kuma kashe wayar, na yi yunƙurin kiran sa amma wayar bata shiga, a kashe. Me ke shirin faruwa?**********
Azabar da suka gana ma waɗan da suka kamo shi ne ya sa ɗaya cikin su ya ambaci sunan ubangidan su ɗaya wato Alh. Na Manzo, nan kuwa su Master suka ba zama neman Na Manzo sai dai abin ya ci tura, har sun fara cire tsammani sai tracker ɗin da Master ya samu damar mannawa jikin wata mota ta yi ƙara, ko kafin ya ɗauko tablet ɗin sa ya fara jiyo maganganu ta earpiece ɗin da ke maƙale da kunnen sa "ka ji abin da ke faruwa kuwa Na Manzo? Sai muryar Na Manzo ya ji yana cewa ai in faɗa maka da safen nan na samu waya daga can hukumar ƴan sandan, hmm kasan ashe yin abin su ke ba tare da sanin shi ɗan leƙen asirin na mu ba, tun da na ji na gagara natsuwa har can majami'ar na so zuwa amma da kace kana zuwa sai na ga gwara na jira ka ɗin, ynz ina mafita? Nan ɗayan mutumin ya ce kai ynz Meye shawarar ka? Sai ga muryar Qais yana cewa "ai Alh babban abin tashi hankalin ma babu wanda ya san in da shi Mastern ya kai yaran don an tabbatar ba su a nan station ɗin, sannan a cikin yaran akwai idon sani, don akwai yaron da aka samo ɗan unguwar su matata ne kuma ya san ni farin sani, ina ganin kawai a hnzarta zuwa majami'a duk abin da zai yiwu kawai ayi don na ji hatsabibanci shi Mastern nan y shahara, ordinary mataki ba zai kai shi ƙasa ba, kuma kasan ai ɗan gwaggon matata ne fa... nan Qais ya yi shiru, muryar farko ta ɗauka... yanzu kai Na Manzo kira min Musa da wayar ka mu ji" da sauri Master ya yi ma yaran sa alamar su shirya mota, ba ɓata lkc kuwa suka yi shirin gaske don sun san harkar sayar da rai ce amma sun yarda da Master. Shi ma Mastern tablet ɗin sa ya kunna yayi connecting nan ta ke ta fara karanto musu location ɗin da suke suna tattaunawar nan, ba ɓata lokaci su ka ɗau hanyar da za ta kai su inda su ke.....
*********
Shiru ta yi kawai tana tunanin halin da ɗan ta ya ke ciki a yanzu don ɗazu ya yi musu text message ita da baban sa akan su taya shi addu'a idan ya ci nasara wannan karon zai ajiye aikin da ba su so. Tun sannan hnkln ta bai ƙara kwanciya ba, har mijinta ya shigo Amb. Wazata bata sani ba, sai da ya dafa ta sannan ta kula da wanzuwar sa. Zama yayi kusa da ita ya ce "Mi Amour, ba abin da ya kamata ba kenan, kamata yayi ki yi masa addu'a ba ki zauna kina ta tunani haka mai zurfi ba, yanzu je ki sanyo mayafin ki mu je ayi ta masa addu'a a masallatai da makarantun islamiyya In Shaa Allah babu abin da zai faru sai alkhairi, kin ji" b ta komai ba face bin umurnin sa, suka fice don ayi sadaka da addu'o'i don samun nasarar sa akan abokan hamayya.
********
Hnkln Fa'iza ƙoƙari ya ke ya bar jikin ta ganin har an yi azahar amma babu Haj sannan babu kiran Qais tabbacin bai je gida ba kenan balle ya sa bata gidan, fatan ta.... Kai ba ta ma san fatan me zata yi ba bayan abin da ta ji da kunnuwan ta...ba ta san ma daga inda zata faro ba. Wai ace UWA mahaifiya? Da ta san hakan ƙaddarar ta ta ke da ta nemi canjin uwa tun kafin zuwan ta duniyar, sai dai ba ta da wani zaɓin face na rungumar abin da ya zamo ƙaddarar ta.
Har yanzu kuma Mamma ba ta nemi jin abin da ke faruwa ba, tana ganin kamar Fa'izar na da nata sirrukan, rashin tmbyrt kuma ya kuma ɗaga darajar Mamma a idanun Fa'iza...*******
A rarrabe su ke tafiya sbd kada a gane ina suka nufa, kuma har suka bar hq ɗin Allah bai sa wani ya fahimci ina su ka yi ba, don da biyu, uku, ɗaya haka suka fice zuwa inda suka tsara ya zama m.point ɗin su. Duk suka shiga motocin suka kama hanya, motar da Master ke ciki ita ce a gaba tunda shi ne mai tracking ɗin sauran duk ƴan jiran umurni ne.
Tohm an zo wurin. Ya kuke gani, shin za a dace kuwa ko wannan karon ma an fitar da sirrin nasu waje? Da alama kuma wannan karon Master da gaske ya ke sai ya kawo ƙarshen waɗannan azzaluman. Ina makahon mu ya tafi, ya bar mu da jinya? Rahma na buƙatar masu jinya fa. Ya labarin auren Master ne? Duk wannan za mu ji a cikin shafi na gaba da yardar Allah.
#bittertruth
#marriageaffair
#masterwazata
#makahoabdul
#maizarefamily🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...