15

18 1 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
    _*RAHMATULLAH*_

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

Page 15

   _Yaa Gaffar Igfirlana zunubana... 🤲_

   _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

***Sosai hnkln Master ya tashi, don a son ranshi da kansa zai bincik biyun da suka kamo da kansa har sai ya fidda wata maganar kamawa daga bakunan su amma kash! ya rasa waye yayi wannan ɗanyar aikin...gashi dai an shaida musu a asibiti biyun babu poison ko kaɗan a jinin su, toh idan ma poison ne, wa ya basu? bayan babu wanda ya san suna wurin a kulle? Gwara ma Kwaɗo shi an gano poison a jinin sa amma ba a san inda ya samo ta ba, don babu a cikin abincin da ya ci ko ruwan da ya sha....abin ɗaure kan kenan kuma ban da chief ɗin su babu wani bare da ya shiga gun sa...hnklnsa ya tashi fiye da tunanin mai tunani, tashin hankali ne mai haɗe da ɓacin ran rashin cimma burin da ke ransa, sosai ya so ace ya cika alƙawarin sa na bayyanar da masu hannu a cikin satar yaran da ɓata musu rayuwa... A fusace ya fito ya nufi motar sa ya wuce gidan sa in da yasan nan ma wani case ɗin ke jiransa.

     Da shigar sa gidan sashin sa ya wuce ya watsa ruwa tare da rage ɓacin ran sa sannan ya nufo sashin iyayen nasa.

    Kamar yadda ya zata kuwa yana shigowa ya tadda mahaifan nasa biyu zaune a falon suna kallo, da sallama ya shiga ya gaida su, da lfy kawai suka amsa, wuri ya samu a ƙasa ya zauna kan shi ƙasa tabbacin bai da gaskiya kenan...

   "Sannu gwani" cewar mahaifiyar sa..."A kan wane dalili ne zaka canza tsarin part ɗin Madinah ba tare da sanin ta ba? Eh? Me ya sa ne kai sam baka tsoron bakin mutane? Kamar ce maka nayi komai yadda take so zaka mata and a zauna lfy, yau auran ku dududu saura ƴan watannin ne fa, da zaran ta kammala course ɗin da ya kai ta Spain ta dawo sai mgnr aure da tarewa, amma shi ne tun kafin ta dawo ka canza tsarin sashen ta? Bayan gari ya Canada ta ɗauko tsarin yadda take son a tsara mata sashin ta amma ka canza? Tukunnan ma meye dalilin ka na canzawa?"

        Kan sa ƙasa kawai yace "a yi hkr". Rufe bakin sa babansa ya ce "daman nasan zancen kenan, ayi hkr, amma dai tunda ka girma ya kamata kasan ka girma, ynzn Bibidy ta ga ana maka faɗa, gobe idan ka mata faɗa kana ganin zata ji? Pls ka daina Mamienka mgn ka ji takwara" ya ɗaga kai ya ce "In Shaa Allah zan kiyaye" shi kenan zancen dalilin canza tsari ya tashi aka shiga wata hirar, kiran sallah ce ta tada su daga hirar inda ya samu lbrn Bibidy ta tafi gidan Uncle Mu'azu yayan Daddy ne kuma baban Madinah.

*******

   Yau a wahalce na yini ga dare kuma ya kai still ciwon bai lafa min ba, menstrual cramp ne, daman sabo na ne in dai ciwon nan ne amma ba a sabo da ciwo kuma kullum duk wata sai na kusa kwana biyar ko bakwai ina jinya, na rasa mai taimaka min da ko paracetamol ne, kuma ban son shiga cikin gida, da ƙyar na ɗauko waya ta na rasa me zan yi ko na kira Mamma ne ko na shiga gidan? Idona rufe na wayar na ringing, na ɗaga a wahalce don wannan karon abin na neman fin ƙarfina don ya zarce na kullum...

   Ina ɗaga wayar mara ta tayi wani kalar murɗawar da ta sa ni sakin ƙarar azaba tare da ɗauke numfashi na zube wurin ba tare da na san in da kaina ya ke ba....

So sorry yau page ɗin kaɗan ne, da kyar na yi squeezing sbd kada na bar ku jira....

#comment
#rahmatullah
#wazatafamily
#hubbifillah
#vote
#share

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now