28

34 1 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
  *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
   Wattpad @oummarfah20

Page 28

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

   _Radiitu billahi Rabba, wa bil islami dinan, wa bi Muhammadin (S.A.W) nabiyan warusulu_

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

********
    Za ku yi mamakin idan na ce muku ban san dalilin sarƙewa ta ba, kawai ji na yi zuciya ta na tafasa kamar zata faso kirji na ta fito. Babu wanda yayi yunƙurin kawo ruwan face shi dai don kowa na fama ne da abin da ya dame sa, sai da ta harare shi sannan ta amshi ruwan daga hannun sa ta kafa min kofin a baki tana sannu baby, sha ruwan ya lafa miki. Kaɗan na sha ruwan ban iya sha da yawa ba, don tarin yayi yawa. Sai can dai da taimakon Allah da taimakon Ya Babangida da ke shafar bayana na samu ya lafa. Yana lafa min na ɗago na kalli falon, Baba ya jingina kan sa da kujerar ko tunanin me ya ke oho? Mamma kuwa na kusa da Haj tana ƙara ba ta baki ita da Fa'iza, sai Mammy da ke tare da ni sai gwaskan. Janye jiki na nayi daga kusa da shi na sake shigewa jikin Mammy, ganin haka kuwa ta riƙe ni sosai tana tmbyr ko da wani abu ne? Girgiza kai kawai na yi ban ce komai ba, amma zancen gaskiya shi ne ban san gani a kusa da ni, don wani zafin da zuciya ta ke yi ji na ke kamar na shaƙe kai na na shaƙe shi mu huta dukan mu, amma babu hali.
   Baba ne bayan wani ɗan lkc ya ɗago ya kalli Master ya ce "me ya sa da ka gane ba ka faɗa ba?" Gyara zaman sa yayi bayan ya koma inda ya taso ɗin ya ce "ban faɗa ba sbd ina son na kama su a hannu, don san da na fara binciken, da asibitin da ta haihu na fara, har Allah Ya sa na sami wata nurse ta yarda za ta faɗa min yadda aka yi don ta ji su a lokcin, sai dai ko kafin washegari kamar yadda ta alƙawarta za ta zo ta same ni a wani park ta faɗa min don kada wani ya ganta tunda gargaɗi sosai su kayi mata, sai dai ba ta zo ba ƙarshe na samu labarin mutuwar ta wai ta sha guba, bayan rubutacciyar wasiƙar da aka ga ta bari wai da ta fallasa su gwara ta kashe kanta, ni dai ko a lokcin na san kashe ta aka yi, don ta na da ƴa, ba zata kashe kanta ta bar ƴar ta ba. Bayan nan sai na nemi footage ɗin CCTV ɗin wurin security guard ɗin sai dai zai bude min  kenan, mu ka ji wata tsawa, abu na gaba kawai ganin sa na yi a ƙasa a mace, hakan ya sa ban ƙara neman taimakon kowa ba, sai na ke yi da kai na a ɓoye kawai, wannan shi ne dalili" Baba ya yi shiru yana tunanin tsawon lkcn da ya rayu da wancan matsafiyar a matsayin mata, waigawa yayi ya kalli yadda Fa'iza ta rungume mahaifiyar ta...so ya ke ya ji meye dalilin Atumbulash na zama da shi da cutar masa da ƴa. Miƙewa kawai mu ka ga yayi yace "prison zan je dole na ji dalilin ta na aikata mana abin da ta yi ni da iyalina, laifin mene muka yi mata haka da ba zata iya yafewa ba?" Yayi ƙofa kawai zai fice, Haj ta miƙe ta ce zata bi shi, Mamma ma hakan ganin haka sai Mammy ta ce na tashi mu je a yi komai da mu, daman Fa'iza na jikin mahaifiyar ta, ta ƙi sakin ta ko nan da can, ban musa ba na miƙe za mu fita, Master da har fita tuni ya dawo ɗaukar wayar sa da jakar sa ta wanzami wanda a ciki ya sa duk wani kayan tablets, wayoyi, da duk kayan kwalliyar sa ta basaja. Kallo na yayi ganin na nufi ƙofa bai ko kalli Mammy ba ya ce "ke! Koma" na ji shi sarai amma maimakon na juya ɗin sai na ke kallon wacce ta isa da shi ɗin, ai kam kai tsaye ta ce "ni nace ta bi mu, ba za a bar ta 8ta ɗaya a gidan ba, tunda Abul na can idan an kwana biyu sai su dawo... mu je ke" na bi ƙofa na yi waje. Kafin na kai ƙofar na jiyo Mamma na cewa "da dai kin bar ta gidan tunda mijin ta ya hana ta" Mammy da daman neman wanda zata sauke fushin da Master ya ƙunsa mata na ɓoyon gskyr, ai kuwa da wa Allah Ya haɗa ta "af! Daman jira nake na san bayan sa za ki bi, toh ba zan bar ta ba, miji kuma ku kuka san shi, don ki ji ma auran nan sunan sa matacce, yauwa na faɗa na ƙara ba zata zauna da shi ba, ni wallahi idan na ga yadda ki ke nuna ko in kula akan baby tunani na kan bani ba ki damu da ita ba ne, haba!" Mamma dai sai shiru ta yi, shi kam daman yana ce min na komo ya fice abin sa.
     Ina sanya ƙafa ta waje saƙo ya shigo waya ta kamar ba zan duba ba, sai kuma na buɗe, ganin wanda ya turo saƙon ya sanya ni harɗewa kamar zan faɗi Mammy ta taro ni jikin ta "baby lfy dai ko zaki faɗi, sannu" "Mammy jiri na ke ji ina ga zan zauna gidan kawai gobe ko anjima driver sai ya kawo ni" da kulawa Mammy ke shafar bayana "ayya baby ko na zauna da ke ne?" Na murmusa na ce "ba komai Mammy, zan rufe ƙofar har su dawo" "kin tabbata?" Na ce "eh Mammy" ba dan Mammy ta so ba ta bar ni bayan ta tabbatar na rufe ko ina.
   Ɗakin mu na shiga ina kumburi don na kula wannan Babangidan sai na nuna masa Ni ma ba kanwan lasa ba ce sannan za mu zauna lfy. Baccin da ban samu na yi ba jiya sbd damuwar rashin mijina shi ne ya kama ni yanzu ba tare da na shirya ba.

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now