19

69 4 3
                                    

[5/30, 10:07 AM] Oumm Arfah: 🌼🌼🌼🌼🌼
    *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
   Wattpad @oummarfah20

Page...

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

_Allah Ka gafarta mana laifukan mu da mu ka yi a gare Ka, lallai tabbas Kai ɗin Mai Gafara ne_

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

*********

Sun ɗauki tsawon lokaci suna horn a  gate ɗin kafin a zo a buɗe, wani tsoho ne tukuf da bai ma gani da kyau ya buɗe ƙaramar ƙofar ya fito ya same su don jin ko lfy.
   Da isar sa wurin su ya tmbyi wanda suke nema, suka shaida masa matar gidan su ke nema, nan kuwa ya shaida musu ta tafi Habuja, baba bai ji ba sai ya ƙara tmbyr ina ta je, sai tsohon ya ruɗe ya manta me ya ce da farko don haka sai ya ce ta je kwatakwal. Makaho da ke gaban mota ya riga baba mgn in da yace "ai kun kira ta, tace mu zo tana gida" jin haka sai maigadin ya kalle su da kyau, ya tabbatar lallai ba ƙarya su ke ba da alamar ƴan gida ne. Sai kawai ya juya ya koma don buɗe musu ƙofar su shiga...
   Driver ya kalli makaho da burgewa ya ce "ya akai kasan ƙarya ya ke?" "Baki biyu yayi shi yasa kawai na gane ba gsky tare da shi" Makaho ya ba shi amsa, dai dai lokacin aka buɗe musu gate suka shiga ciki.
    Fa'iza na ɗakin ta ta ji shigowar mota, hawayen takaici suka zubo mata, inda sabo da ta saba amma kullum mamakin Qais ta ke, tun safe suka ƙule a wani ɗaki a ƙasa shi da wasu abokan shashacin sa, kuma tun sannan basu fito ba, har kawo yanzu da ake shirin yin azahar, ynz kuma ta san ƙila sai dai ya fito ya neman musu abinci su ɗora daga inda suka tsaya, wasu hawayen da suka zubo ta share ta miƙe don shiga ta yo alwala, ta miƙewa ta ji wayar ta na ringing tana dubawa taga hajiyarta ce, ta ɗauka tana ƙoƙarin cire damuwar da ke ranta don har wa yau hajiyarta ba ta san wane hali ƴar ta ke ciki ba, idan ta tmby sai ta ce lfy kawai, ba ta son a yi wa hajiyar ta dariya... Da ƴar murmushin da iyakar ta bakin ta tace "hajiyata, kamar kin san ina kewar ki" ta ƙarasa ta na mai jin raunin zuciyar ta. Yadda Haj Babba ta ji muryar ƴar tata ne ya sa babu jan zancen ta ce "mene ke damunki hakan? Maza zo ki buɗe mu muna waje da babanki" tana gama faɗa ta kashe wayar tana tunanin ƴarta babu lfy, tuna dalilan da ke mata rashin lfy da kuzari a ɗakunan mazajen su ya sa wani farin ciki da annashuwa lulluɓe ta, tana mai fatan Allah Ya sa hasashen ta ya zamo gsky, d ta fi kowa murna kam...

    A can ɓangaran Fa'iza kam jin zancen Haj ya tashi hankalin ta sosai, ba ɓata lkc ta ɗauki hoda da kwalli ta ɗan gyara fuskar ta da fatan ko hakan zai ɗan rage yanayin da ta ke ciki, ba ta son tun yanzu babanta ya fahimci da mtsl a gidan auren ta, don ba ta mantawa sosai ya nuna rashin amincewa da auren don yayi bincike amma ba lbr mai daɗi a kan Qais ɗin, amma ita da Haj suka rantse sai shi, ta nemo wani babban mayafi mai kauri sosai ta rufa tun daga kai don kada a ga ramar ta, gashi bata da hijab ko ɗaya, sallahr ma da alkyabban ta ta ke sawa ta yi. A hnkl ta buɗe kofar ta fito don ta jima da dawowa ƙasan, ta isa kofar falon ta buɗe kanta ƙasa, a ƙoƙarin ta na guje wa kaifaffun idanun mahaifinta. Tana buɗe kofar ta matsa tana ba su damar shiga cikin falon sosai, ƙamshin Mamma da ta ji ya sa ta ɗago tana kallon ta, ganin da gaske ita ce yasa ta yi gaggawar aro ma kan ta natsuwa ta sa ma kanta, duk rintsi ba zata taɓa bari maƙiyansu su yi musu dariya ba. Ba ta ƙara shiga natsuwar ta ba sai da ta ji baba na cewa shige mu je mana Rahmatu, abin da ya fara zuwa ranta kawai gulma ce ta kawo su don a ga halin da ta ke ciki, wannan zuwan nasu ma yasa shaiɗan na raya mata wataƙil su suka jefi mijinta da baƙin asirin su na gado...
   "Me kike jira ne ki kai tsaye a kofa" muryar baba ya katse ta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta faɗaɗa laɓɓan ta wai tana murmushi...ƙarasowa tayi ciki ta gaida iyayen nasu, suka amsa sannan Rahma ta gaida ta, ta amsa kamar babu komai har da tmbyr ya mijinta. Ta shi tayi ta ɗebo musu drinks da ruwa, akan su sha kafin ta ƙarasa dafa abinci. Nan baba ya ce su zasu sallah su dawo kada ta damu, ya tashi ya fice daman makaho a waje ya tsaya bai shiga ba. Baban na fitowa su ka nufi gate suka fice zuwa farkon layin inda suka ga masallaci da zasu zo, suna tafe baba na jan makaho da hira da jan shi jikin sa cikin hikima yana ƙara karantar makaho da yaba natsuwar sa sosai.

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now