🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼Oumm Arfah🥰.
'''Wannan shafin dukkansa sadaukarwa ce gareku masoyana da bani da tamkar ku, ina godiya irin sosai ɗin nan💯'''.
'''*_Domin tunawa da marigayiya Rahma_*''' Muna fatan Allah Ya sa kina a kyakkyawar masauki tare da sauran ƴan uwa Musulmai baki ɗaya Ameen Yaa Rabb...
4️⃣
Ranar wata asabar ce mun je bikin wata ƴar ajinmu a unguwar da ke gaba da mu, kusan zance wannan bikin shi ne biki na farko da na fara zuwa a rayuwata, don har na ƙare secondary school ɗina ba a taɓa bari na naje wani abu wai shi biki ba, don haka wannan bikin shiri nayi sosai kamar bikina ne na ƙure adaka, na dau kwalliya mai suna kwalliya babu karya na ɓoye munin fuska ta, a cikin abokan ango Salisu ya ke, yana kyalla ido a kaina, hodar ta ruɗar da shi ya furta min kalmar so, ni kam da daman yunwar mai so na na ke babu ɓata lokaci na amsa tayin sa, murna kamar zai yi me? Mun ɗau tsawon lokaci ta waya kawai muke haduwa don sannan bamu da lasisin kawo saurayi gida, sai daga baya Fa'iza ta fara hira da samari sai ya zamana ta buɗe min hanya ne, nima sai na gayyaci Salisu zuwa gidanmu wanda a lokacin sosai ya ke kashe ni da hirar soyayya a waya, yana kuma nuna min ya ɗokantu da gani na kuma babu ɓata lokaci idan an amince masa aure za mu yi baya son ɓata lokaci...amma me?... Tun ranar da Salisu ya zo gidanmu aka samu matsala, ya aika na zo sai na fita babu kwalliya a fuska kamar sanda muka haɗu, mun gaisa lfy lau sai kuma ya kalle ni "amm ina ƴar uwar ta ki ko bata nan ne?" Wata kalar faɗuwar gaba na jin dajin wannan kalami nasa, nace "ni ce fa Ya Salis ba ka gane ni ba?" Ya kalle ni da kyau sannan yace "sorry ban ankara da muryar ba, so y kk?" Tun daga wannan lokacin sosai ya canza min idan ban kira ba, shi ba zai kira ba, zuwa wurina ma sai na roƙe shi ya ke zuwa, ni kuma na kasa zuciya na rabu da shi, don shi kaɗai gare ni kamar RAI! a hakan mu ke har kawo yanzu da mu ke kai har kawo yanzu da muke shekara da sanin juna...****************
Ajiyar zuciya na sauke cikin tausayin kaina yadda NAMIJI ke wasa da rayuwata kuma a hakan shi na ke son aura idan an bani damar fitar da gwanina, fatana dai zuwa sannan ya gane irin SOn da nake masa ya so ni ko kwata ne... Ban san tsawon lokacin da na ɗauka ina tunani ba, Abdul ne ya shigo ɗakinmu ya ke faɗa mana sakon baba na kiran dukkanmu. Babu ɓata lokaci mu ka isa falon nan muka zauna a ƙasa daga gefen iyayen mu mata, muna mai musu sannu... Baba ya kalle mu yace "nasan kowacce ku ta na da wanda ke zuwa wurinta zance, tohm saƙon shi ne ku faɗa musu su turo iyayensu a yi maganar aure don bana son ku ƙara shekara ɗaya a gidana,ina fatan kun gane? Yauwa kuna da damar turo su daga nan zuwa watanni biyu zuwa uku" daga hakan babanmu yayi shiru alamar ya gama zancen sa kenan "tohm" kawai muka ce muka mike zamu tafi babanmu ya ce na kawo masa lemun tacacciyar itatuwa wanda na masa da safen bayan na gama abin karin kumallo, na ɗauko masa na nufi ɗakinmu ina tunanin mafita, da shiga ta ɗakin na ji Fa'iza na ba wa saurayin ta albishirin cewa addu'ar sa ta karɓu an ce ya turo manyan sa, daga inda na tsaye ina iya jiyo ihun murnar da ya saki yana faɗin "baby na gode, I will call you back, bye" ya kashe wayarsa, na kalle ta muka haɗa ido ta min kallon 'idan kin isa ki yi abin da yi' ban biye ta ba na ɗau waya na kira mutumin nawa, lucky enough ringing biyu ya ɗaga "ina waje, ɗan fito" abin da yace kenan kawai, na miƙe, na gyara fuskata na sa hijabi na na fita kofar gidan bayan na faɗa ma Abdul ya ce ma Mamma na fita Salisu ya zo.
A ɗan gefen gidan mu ya tsaya na fita na shigo da shi zauren mu, muka gaisa lafiya lafiya, na buɗe baki na faɗa masa saƙon babanmu akan ya turo manyan sa. Ya kalle ni bayan na gama mgn ya ce "daman zancen da zo mu tattauna akai kenan"...ya cigaba "gaskiya ina ganin lokacin da zamu raba hanya ya kai, don yanzu haka jiya aka samin ranar aure watanni shida masu zuwa zan yi aure, ina fatan ki samu wanda zai soki fiye da son da kike min, sannan na gode da soyayyar da kika nuna min, ina miki fatan alkhairi..." Ni dai har ya kai ƙarshen maganar sa ban san mai ya ke cewa ba bayan an sa mai rana da na ji, hawaye kawai ido ne ke fitarwa mai fitowa daga cikin zuciya mai zafin gaske, ɗaga kai nayi kawai na hango bayan sa ya na tafiya...jiki a sanyayye na koma ciki, ban faɗa ma kowa abin da ke nan ba, na ci kuka na na koshi na share hawayena bayan na ba kaina hakuri kan cewa hakan Allah Ya ƙaddaro min, and Alhamdulillah...***********
"Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un, yaushe ne abin nan zai ƙare ne, jiyan nan aka kawo mana wani yaro ba a hayyacin sa ba dalilin shigar sa ta ƙarfi da aka yi, kaca-kaca aka yi da duburar sa, har yanzu bai dawo hayyacin sa ba, yau kuma ga wani, kuma duk kusan shekarun su bai wuce goma zuwa sha ɗaya, ni abin nan ya fara bani tsoro fa, Sir" biron da ke riƙe a hannunsa ya ciza yana mai rasa mafita, duk sanda suke tunanin sun kusa kama masu hannu a ciki kafin su kai ga attacking an yi leaking information ɗin wanda kullum babban su ke accusing ɗin sa da ƴan team ɗin sa akan su ke leaking information ɗin. Shi kuma babu ƙarya ya shaidi ƴan team ɗin sa ba zasu taɓa fitar da sirrinsu ba, toh amma waye mai fitar da sirrinsu? Ajiyar zuciya ya saki yana mai kallon team ɗin sa su huɗu sai shi cikon na biyar, kuma ƙwarrare ne akan computer, kowa fuskarsa ɗauke ta ke da damuwar yadda ake fitar da sirrinsu..."ina da shawara" cewar ɗaya daga cikin su, duk suka kalle shi suna jiran ji daga gareshi " me zai hana duk wanda ya kawo idea ɗin sa kawai yayi sharing ɗin sa da kai ne kawai ba tare da sauran ƴan team ɗin sun sani ba, ta hakan za a iya gane idan mai fitar da maganar waje a cikin mu yake" cikin gamsuwa da shawara Musa Bello, Master ɗin su ya gyaɗa kai yace good job Mr. Bello, wannan shawarar am in for it...akwai mai wani idea ɗin?" Ya faɗa yana kallon sauran members ɗin sai dai kowa da alamar ya goyi bayan shawarar Mr. Bellon. Nan suka cigaba da tattaunawa kafin kowa ya watse aka bar Master da tunanin next step ɗin da zai ɗauka yanzu tun da ga yanda abin ya ke juyewa ya koma...****************
Kwana biyu tsakanin sakon babanmu iyayen Qais suka turo kuɗin tambaya da na sa rana gaba ɗaya, aka tsayar musu da wata goma duk da tunanin kafin nan nawa saurayin ya ƙara shirya wa... Bayan tafiyar masu tmby ni da mamma sai da muka ji kamar mu bar gidan, don kuwa habaici kala irin daban-daban babu wanda bai shiga kunnen mu ba, don Hajiya yadda kuka san ranar ne ranar auren yadda ta gayyaci ƴan uwanta har suna faɗin "ai a komai mai kyau ake fara daukewa" Ni dai yi nayi kamar ban san habaici su ke yi ba, da yammacin ranar ma na yi wucewa ta islamiyya ni kaɗai ba tare da Abdul ba. Na baro shi kwance wai baya jin daɗin jikinsa. Ina dawowa gida Abdul ya tare Ni da zancen ko na ga makahon abokinsa, haushi ya kamani na bi shi da ranƙwashi daman da haushi a raina sbd can ina dawowa na ga Salisu da wata kyakkyawar mace a motar sa, wadda ko ba tmby na sani mai wannan a matsayin wacce zai aura, mai zai yi da ni?_So Dearies! Ya kuka ji tafiyar?_
_Mai kamar zuwa kan aika right?_#rahmatullah
#fa'izamaikyau
#makahonabdul
#maizarefamilyaffair
#marriage
#kidnapandassault
#hubbifillahPlease comment and share...
🌼🌼Oumm Arfah🥰

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...