10

23 3 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
  *_RAHMATULLAH_*.

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah🥰.
   Wattpad@ oummarfah20

Page 10.

  _Yaa Rahman Ka fi mu sanin matsalolin mu, Allah Ka yaye mana. Ameen._

******* Cikin sanyi nake komai wanda daman Ni ɗabi'a ta ce wannan kam, na ɗauko plate na juye bin ledar da ya turo bayan ya ji dawowa ta.

  Balangu ce zazzafa sai wata madarar hollandia na juye naman na tura gabansa...karon farko na ɗago na ƙare mai kallo waɗannan ƴan kurarrajin fuskarsa na nan sai ɗan raguwa da suka fara...alamun ya samu magani ko kuma sauyawar man shafawa mai kyau da wurin kwana mai kyau... Tabon ƙunan da ke a gefen fuskarsa ta fara ɓacewa.

Ɗauke kai na nayi na tura plate ɗin gabansa har sai da ya taɓa ƙafarsa nan ya gane na zuba kenan, tashi yayi ya fita kofar ɗakin ya wanke hannu ya dawo, jin yawan naman ya sa ya laluba har Allah Ya sa ya taɓo ledar da na cire madarar a ciki, ya jawo ledar ya ɗebi ɗaya bisa ukun naman, ya turo sauran gaba yace "taimaka ki ci kada ki kwana da yunwa, wannan ya ishe ni" wata harara na watsa masa ina kallon gefen fuskarsa ina raya ma raina meye nasa idan ban ci ba.

Ban ma tanka shi ba nai zaune a cikin kujerar har ya gama cin nasa ya tashi ya shiga bayin ya watso ruwa ya wanke baki ya fito, kamar jira yana fitowa naji ƙarar Nokia daga cikin jakan wanzaman nan na shi, a hnkl ya tako ya lalubi jakar ya fito wayar, ta sha ɗauri da roba, ya ɗaga wayar da wata natsuwa ya ke maganar da ta sani kallon shi babu shiri, da waye ya ke waya haka? Hakan ne ya ke magana ko kuwa iya yi ce irin ta makafi?

**********

   Kwance ta ke a kan kujerar falon nata, ta yi wata kalar rama da ta sani kallon ta sau biyu, wannan ba amaryar kwana goma bace, ta jeme gaba ɗaya kamar mai cutar yunwa. Fa'iza mai kyau kenan.

  Kallon ɗakin nake ba ƙarya an ci mutuncin dukiya kamar ba a san zafin su ba, Lallai wannan falon ko gidan gwamna iyaka kenan. Gidan ta mai kyau mai bene hawa ɗaya, kayan gidan sun dace da gidan. Mashaa Allah.

Ƙarar saukowa na ji daga benen, ko da na ɗaga kai sai na hango Qais angon mai kyau, da damuwa sosai kan fuskarsa ya iso inda ta ke kwance ya ɗago ta jikinsa "beauty am srry, kin ji, ba zan ƙara ba, ruɗewa nake har ban sanin yaushe ne nake canza hanya, abin ki da sabon shiga, har ynz ban gama sanin hnyr ba" wani kallon da ta mai ya sa na fara tunanin ko dai daman ba auren so ne a tsknn su ba, ture hannun sa ta yi daga jikin ta ta ce "Qais na gaji, kullum hakan kake cewa, kuma kullum sai an kuma, idan ba ka sani ba ka tmby mana, idan kana jin kunyar tmbyr abokai ka tmby malamai su ba zasu maka dariya ba, amma duk ka ƙi jin shawara ta, ta kai ban iya zama da kyau, toh ynz shi ne na ke ga gwara mu  ɗan bari ka san hnyr tukunnan"

  Wata dariya ya saki sannan ya ce "tohm beauty duk yadda kika ce hakan za a yi amma kin san zan ƙwaru ko?"  "Eh shi yasa ya kamata ka sani da wuri" ta faɗa tana kallonsa ganin yayi shirin fita "wai fita za kayi ne? Na ga ka yi sabon shiri"  "eh zan je wurin Kawu Musa ne, shi ya kira ni, ba zan jima ba zan dawo kin ji? Zan taho miki da favourite ɗin ki" Ya bata sumba a goshin ta ya fita. Da kallo ta bi shi har ya fice. Ita dai bata san mene zata kira auren da tayi ba, domin har yau ba ta san ya ainihin rayuwar auren ya ke ba, domin Qais ɗin bai san hnyr ba sai wata daban...

**********

  Jingun jingun su ka yi suna tunanin wata mafitar don da can almajirai ake ɗaukewa amman ynz yara da iyayensu ake ɗaukewa a fake da garkuwa da su ko kafin a dawo da su an lalata rayuwar su, kuma abin haushin hukumar bata ba su gudunmawa wajen tsananta bincike, wanda kaf headquarters ɗin nan an san duk aikin da ya gagari Master da ƴan team ɗin sa toh wannan kam babu wani team da zasu iya komai a kai. Ynz zaman da su kai jiran isowar Master su ke don jin me zai ce...

***********
Amb. Wazata zaune tare da matar sa tun ta lalle kuma uwar ƴaƴan su, hira suke cikin jin daɗi da nishadi tare da ƴar autar su bibidy suna zancen lkcn komawarsu gida Nijeriya ne, Bibidy ke ce musu ita su bar ta a nan don sau ɗaya ta taɓa zuwa hutu wurin yayanta amma da kyar ta yi kwana shida ta koma don zafin garin sosai ne ita kam bata saba da zafi ba, don haka ta ce su bar ta a nan ta gama secondary school ɗinta. Shi ne Amb. Wazata ya ce "ai aure zai mata suna komawa can" To shi ne fa ta ke juyi a gaban su wai su kalle ta bata isa aure ba, she's just ten yrs fa, za su yi child abuse ne...shi ne suke ta ƙara tsokanar ta suna dariya....

**********

  Qais na fita ya nufin gidan shaqatawar Alh. Musa, ya tarar baya falon yana sama, zama yayi ya jira sa, can bayan kamar wucewar mintina 30 sai gasu sun fito shi da wasu matasan yara su biyu wanda shekarun su bai wuce 17 ba, idanun ɗaya yayi ja sosai kamar ma kuka yayi kuma yana tfy yana ware kafafu kamar ɗan kaciya... Shi kam ɗayan da alamar bai da mtsl.

  Ganin Qais zaune ya sa shi sallamar matasan ya kalle sa "brk da wnn lkc Alh" "yww brk dai, yaya ake ciki ne". "ai Alh abin ne ynz whlr samu ake, kuma jama'a sun ankare don ma muna da magoya baya daga sama da abin ya ɓaci" Alh yayi shiru sannan ya ce ka shirya gobe za mu je wani wurin".   "Toh Alh Allah Ya kai mu goben". Daga nan suya spot ɗin da ya san Fa'iza ba ta hkr da shi ya biya ya sai mata take away ya nufi gidan. Da shigar sa cikin gidan ya buɗe naman ya zuba wani mgn kamar yaji haka ya rufe ya kai mata ciki.  Wannan karon bata falon tana sama nan ya hau ya bata naman tai godiya ya wuce ɗakin sa wai zai huta....

     Gama cin naman nan da wuya, ta ji a duniya idan ba namiji ba bata son komai, a buƙace ta ke sosai don hk ta nufi dakin Qais tayi knocking, yana jin knocking yayi kamar bacci ya fara, babu jan aji ta faɗa kansa kawai tana bashi sumbata ta ko'ina. Da wannan damar Qais yayi mata abin da ya ga dama duk a zuwan cikin mayen SO ne...(Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un, Allah Ya tsare mana imanin mu, Ameen).

*********

  Yau kwanana uku da tarewa kuma yau ne zan fara girki don jiya Mamma ta ce a gaya min na fara dafawa mijina abinci.

Wannan yasa yau tun safe na shiga kitchen na sarrafa mana Irish da kwai sai tea mu ka karya, kafin na tsara time table ɗin dafa abinci.

Can misalin kamar karfe 10 na safe ina zaune ina karanta azkar ɗina ya tashi ya shiga bayi, bayan kamar awa ɗaya da rabi da shigar sa bayin ya fito a shirye cikin ɗaya daga cikin kayan da aka masa na fitar biki, ya na lalubar inda ya ijiye sandar sa don ban taɓa ganin zai shiga bayi ya shiga da shi ba.

Sannan abin da ke bani mamaki da shi shine, mutum ba ido ba amma alkawari ne duk sanda ya shiga bayin a bai jima ba yayi awa ɗaya, toh na kan rasa mene ya ke wankewa, kuma da kayansa ya ke shiga a cikin jakar sa ta gado. Ganin da gaske ya gagara neman sandar ya sa na miƙe na ɗauki sandar na miƙa masa, ya karɓa yayi gdy sannan yayi hnyr waje bayan ya ajiye kayan da ya cire a bayin, sai da ya kai ƙofa ya juyo "toh amaryata zamu tafi nema a mana addu'a" sai da na danna mai harara sannan nace "Allah Ya bada sa'a" da murmushi sosai kan fuskarsa ya ce "Ameen", sannan ya fice, Ni kuma na tashi na ɗan kimtsa dakin.

  Nasan kuna ta mamakin mai yasa bana bori akan ban son auren kuma ban son makahon ba, toh a gaskiya ban da ma ra'ayin yin hakan don na yi tunani, duniyar duka nawa take? Sannan tunda na rasa Khalil na amince zama da kowaye, amman babu soyayya, don SO ɗaya ce kuma Khalil ya tafi da nawa...

#rahmatullah
#ASmakaho
#AAwazata
#Kidnap&assault
#hubbifillah
#oneluv

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now