🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah🥰.
Wattpad @oummarfah20_Allah Ya jiƙan magabatan mu Ameen._
Page 7-8
******
Yau kwana uku da rasuwar Khalilina, na fita kamanni na, You can imagine ya zaki ji wanda kika tsara kuma kika yarda ku yi rayuwa tare ya mutu kwana kaɗan kafin biki... Tun da na farko daga gajeriyar mutuwar da ni ma na kusa yi, ban kuma bin kan waya ta, gaba ki ɗaya ma duniyar ta fitar min a kai gani nake komai da kowa da ya ke nawa zai tafi ya bar ni... Bayan iyayena Khalilina ne kawai wanda ya soni sbd Allah ba don wani halitta ko launin jikina, na san daga iyayensa babu wanda ya kai ni jin mutuwar, na je nai musu gaisuwa a can nake jin bayan barin sa gidan mu ya hau kan titi bai kula ba ashe wata babbar motar siminti ta biyo ta wurin sbd kada ƴan FRSC su kama shi domin kusan overload ya yi wanda ya taka dokar bin hanya, kafin a ankare ya yi kan shi, don motar babu horn kuma babu birki, kafin kace me? Sai dai aka ga Khalil a ƙarƙashin motar... (Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un, Allah Ka sa muyi kyakkyawar ƙarshe. Ka jikan musulmai magabatan mu Ameen). Ance koda aka mishi suturar ƙarshe, duk jini a jikin likkafaninsa... Tun daga ranar ban ƙara marmarin komawa ba sbd tausayin mahaifiyar sa nake sosai, shi kaɗai ne ɗan ta namiji kuma mai lfyr cikinsu, daman su huɗu ne uku mata sai shi kuma shi ne babba sai matan, biyu sun yi aure saura ɗaya, ita ce kuma mai dayabitis sannan sikila ce..
Yau a lissafi bikin Fa'iza saura kwana shida, sannan a yau mahaifina ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa can garin sa wurin ƴan uwansa zumunci da kuma zancen aurena wanda daman Baffa Iro ya taɓa yiwa babanmu maganar haɗin zumunci a tsakanin mu, a lkcn babanmu ya nunar masa da yayi hkr ba shi ra'ayin yiwa ƴaƴansa dole, toh ynz da hakan ta faru, sai ya je ya same sa akan su shirya ranar aure a ɗaura kamar yadda aka sa. Alhamdulillah za a ce domin ya amsa masa da murna akan za su taho da shirin su... Da wannan daddaɗan lbrn ya dawo ya na faɗa ma Mamma, ita Mamma har zuciyarta so tai a bar ni na ɗora karatuna ko da catering ne kafin na dawo hayyacina, amma tunda hakan ya ke so sai bata ja ba tai sa albarka kawai ta shige, da yake ɗakin Hajiya ya ke...*****
Duk abinda a ke ciki ban sani ba, amma ni na yanke ba zancen saurayi ko wani aure kuma, why? Don nasan samun mai sona kuma sai hali...Fa'iza kam ido yayi ja ta zama busy tana ta faman tsara yadda ta ke son bikinta ya kasance duk da baba ya ce babu bidi'a amma ita kam sosai bidi'ar ta ke shiryawa, ni ce dai daman nace walima kawai zan yi, tun ana bikin saura kwana huɗu aka kawo lefen Fa'iza akwati biyar da ɗan kit shaƙe da kayan alfarma na sosai, haba nan fa aka fara yaɗa ƴan maganganu a kan kyau blah blah blah zance dai ga shi nan iri daban-daban... Abin mamaki washegari sai ga iyayen Khalil mata da akwatina biyar da kit irin na Fa'iza sai wata babbar Ghana must go daban, nan fa! Kallo ya koma sama... Ba a karɓi kayan ba sai da aka kira baba nan kuwa ya ce pat! Ba za a karɓa ba a mayar da kayan, sai dai zuwa dare Alh. Muhammad da kansa ya dawo da kayan yace "kaya dai da sunan Rahmatu aka haɗa su, kuma kamar marigayi ya san me zai faru, ya same ni kwana biyu kafin rasuwar sa yace Abba pls ko me zai faru a bai wa Rahma kayan nan na ta ne, yace bai yarda a cire ko zare ba, don haka ku yi hkr ku amsa, ba mu da wani ɗan bare mu ce za mu ijiye masa, tunda rabon ta ne kawai a bar mata" wannan dalili ya sa aka ajiye min kayan a zuwan an hutar da ko wa za a aura min Wanda har ynz ni ban san da zancen auren har da ni ba. Ƙiri ƙiri Hajiya ta nuna baƙin cikin kayan da aka kawo min harda zancen ta na ƙila wani abin aka mai ya sa ya bar wasiyyar a bani, amma ai wannan dukiyar ta yi yawa... And da gaskiyan ta domin tabbas akwatin kansu abin kallo ne bare kayan cikinsu....
********
Gobe aka auren, kuma babanmu daman tun daga kan shi har Abdul da makahon Abdul da ya dawo gidan mu da zama sai da aka yi mana ɗinkuna kala bakwai mu amaren, iyayenmu mata kala biyar biyar, baba kala biyu Abdul kala huɗu sai makahon kala bakwai don daman shi ba wasu tufafin gare sa ba... Saukar yamma sosai su Baffa suka yi amma matansu tun biki saura kwana huɗu su ka zo, sanin sun iso da gajiya sai baba bai nemi magana da Baffa Iro ba ya bari akan za su haɗu da safe ya ji waye mai auren nata....
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Короткий рассказMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...