🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 31
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Laa haula waa laa ƙuwatta illa billah_
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
*******
Ba ta tsaya jiran komai ba kawai ta fita waje da hanzari, har ta wuce mai taxi ɗin ma bata lura ba sai da ya mata horn, sannan ya lura da shi, buɗe jakar ta kawai ta yi ta ciro $100 guda biyu ta ba shi ta juya kawai ta miƙi hanya. Mai taxi kam ai kakar sa ta yanki sa'a, ya ja mota ya wuce, har yayi nisa ya dawo ya buɗe mata, ba tantamar komai kawai ta faɗa motar don gaba ɗaya ta manta a duniyar da ta ke ciki. Sai da suka yi try mai nisan gaske sannan y tmby ta, "HISBA" kawai ta ce masa. Bai tsaya ko ina ba sai hisba office, yana ajiye ta ya ja motar sa ya wuce wurin canjin kuɗi, don ya tashi na ranar.
Ko da ta shiga ciki ma bata yi ma kowa mgn ba sai suka yi tunanin ta ci kai ne, wata baiwar Allah ce ta kamo ta ta zaunar ta ce "ina zaki, sannan mene ke damun ki?" Kallon matar ta ke kamar ta ga sabuwar halitta, tace "na kawo ƙarar babana" jin hakan ba wani sabon abu ba ne sai suka hau yi mata tmbyyn da suke tunanin sun dace da damuwar da take ciki, ƙarshe dai ta ce musu "da ace aure baba na ya ƙi min, ba zan taɓa kawo ƙarar shi ba, kai ko a ce zina ya ke yi da ni, mafita zan nemar ma kaina, amma abin ya girmi kai na, shi ya sa na zo nan" jin hakan sai suka kira babban malamin da ya ke shi kwamandan hisba a lokcin, ba ya kusa amma ya tabbatar musu zai iso kafin mintina talatin.********
Kwana na uku a gidan ya ɗauke ni da sassafe muka bar gidan. A mota ya ja muka fice daga gidan, bayan ya bar ma drivern saƙo a ba Abba, daman Mammy idan ta dage akan abu, hanya ɗaya ne maganin abin shi ne ƙaurace mata, kar ynz da abin ya shafi ƴar gaban goshin ta. Tafiya suke yi kamar ma su barin gari, can kusan ƙarshen gari wata anguwa wai sabuwar GRA ya tsaya a gaban wani ɗan madaidaicin gida, ya fita ya buɗe gate sannan ya zo ya shiga ciki, ni dai nawa ido, don tun a hny na ke tmbyr sa amma bai ban amsa gamsasshiya ba. Gida ne mai kyau daidai zaman mace ɗaya, falo ɗaya, dakin baƙi, Master bedroom sai na matar gidan sai kuma ɗakin yara. Tsarin gidan ya min kyau, ga kicin ga store kai Mashaa Allah kawai, santin gidan nayi hakan ya tabbatar masa da tsarin ya min, ni kam daɗin nawa biyu ne sbd in dai wannan gidan sa ne to na san na tsalleke kishiya (😂joke). Ina zaune a falon ya bar ni ya shiga kicin samo mana wani abin taɓawa kamar kayan marmari, wayar sa ce a hannu na ina kallon wasu zanen hotuna wanda ni ce san da ina ƙarama, saƙo ne ya shigo wayar sa daga Mammy, saƙon na shigowa ina karantawa don wurin ido na yake.
_"Ran ka ne zai yi mugun ɓaci idan ba ka kawo min ƴa ta ba da takardar ta, an gaya maka ban san baby tana gidan nan ba ne? Na san kai zaka nuna mata isa, toh hakan ya isa, ka kyauta, kar ka bari na ƙara tuna maka"_
Me kenan? Takardar wace ƴar Mammy ke neman a ba ta? Amsar wayar ya yi daga hannun na, dubawa yayi ya ga sakon Mammy ne na gani, murmushi ya yi ya ajiye wayar ya zauna ya ce "kyale Mammy, don ta tmby ni ina son ki ne nace a'a shi ne ta dage sai na sakar mata ke in zauna da matar da aka aura min" kallon sa nake yana maganar ina tunanin irin sa'ar da na yi na samun sa a matsayin miji, amma jin yana zancen matar da aka aura masa sai na yi sakato ina tunanin ko ni ce ban ji da kyau ba, na ce "wace mata aka aura maka?" Ya ce "Madinah mana, ynzn haka tunanin yadda zan zauna da mata biyu na ke, kuma ban shirya ba, shin...." Zancen sa ne ya katse ganin na ɗau jaka ta na yi ƙofa, ikon Allah kawai ya tsaya kallo, ban ma san ya ake buɗe kofar ba, sai jijjiga kofar na ke ina ƴan matan hawayen kishi, hannaye na ya riƙo cikin nasa ya ja ni jikin sa yana ƴar murmushin jin daɗi, tun ba yau ba ya san ya kafa gwamnati mai girman gaske a zuciyar ta, kuma shi ma ynz bai san ya zai kwatanta yaɗuwar ta a zuciyar sa ba. "Kukan me ki ke yi, daga magana?" Kawai sai na sa masa kukan gaske, ina dukan ƙirjin sa "na san ba ka so na ba sai ka yi ta yayata ma mutane ba kowa ya san ni matar cushe ce da kowa ya guda ba, na sani ba sai ka tuna min kana da wata zaka aura ba, na sani ai" zantukan dai zallan kishi, bai katse ni ba sai da na gaji don kaina nace "ni gidan mu zai'n tafi, ka zauna da wace zaka aura ɗin, tunda ita kana son ta" don ya ƙara ƙular da ni sai ya ce "baki fahimta ba ne, nace miki an ɗaura ai, yanzu haka ba ta ƙasar ne idan ta dawo zata tare" haba kamar an sa min fetur na cigaba da abin da na fara, can na ɗau waya ta na ce Mammy zan kira ta turo min drv ya zo ya ɗauke ni. Ƙwatar wayar yayi hannu na ya kashe ya jefa a aljihun sa ya ce "yarinya ai kin kawo kan ki kenan, jibi iynzu muna cikin jirgi za mu kai ma amaryar ki ziyara" nan na hau bori ina cewa "Allah ba zan je ba, sai dai idan ɗaure ni zaka yi ka tafi da ni, amma ni ba zan je ba, kuma ka daina haɗa ni da ita" gefe ya koma ya ci gaba da cin fruits ɗin sa yana kallon dramar da na ke yi, idan na gaji da kukan da ni a karan kai na na san na taɓara ne sai na hau jijjiga kofar, hakan na yi ta yi sai da Allah Ya sa ya shiga daki sannan na lallaɓa na ɗau fruits ɗin na fara sha, ina yi ina waige, sai dai abin da ban sani ba, yana kallo na ta CCTV, dariya kawai yayi 'ƙuruci dangin hauka' tana so tana kai wa kasuwa, bai kuma bin kan ta ba sai da ya tabbatar baccin da ta ke yi yayi nisa sannan ya fito ya kinkime ta zuwa ɗakin ya shigar da su bargo ya ja musu ya rufa sai bacci, tunda yau ba su tsaya baccin safe ba.
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...