🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMTULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah🥰
Wattpad @oummarfah20Page 12
_Yaa Razaqu Ar-zuqna_https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Wannan lbrn tun farkon sa har ƙarshen sa, ƙirƙirarre ne suna, halayya, ko wani abu mai kamance, toh arashi ne._
**********Kusan a tare muka isa bakin kofar gidan, don hk ni sai na bar ta ta shiga tukunnan sannan na bita bayan na mata sallama irin ta addini ina mai farin cikin ganin ta, don Allah Ya sani sosai nake son ƴar uwata.
Koda mu ka shiga sai muka tarar baba yana nan bai je ko'ina ba yau kamar yasan za mu zo. Dukkan su suna zaune a falon gidan suna taya baba hira wanda dokar sa ce, nan muka yi gaisuwa mu ka zauna nan tare da su baba na mana ƴan tmbyy game da sabuwar rayuwar mu.
Can ana tsaka da hira, buɗar bakin Fa'iza sai cewa ta yi " ai ke kam Rahma kin ji daɗin ki, ga ki ga gida, ni ma baba da na san zaka bamu ɗaki da nakasasshe zan aura ko dan na zauna kusa da ku" baba yayi dariya kawai yana min kallo mai cike da tausayi da soyayya don ya jima yana dana sani bayan auren, amma a ƙasan ranshi ƙaunar makahon yake sosai kamar ɗan cikinsa, baba bai ce komai, nima kamar ba zan ce komai ba amma sai na ji cin fuskar tayi yawa don nasan Hausa ta yi kuma da ni ta ke sai nace "ai kuwa Fa'iza, kuma gwara ma mai nakasa mai tsoron Allah da tsayawa iya inda Allah Ya tsayar da shi, akan masu lfyr ido amma su ke saɓon Allah da shi, ni kam Alhamdulillah, makaho ne amma mai zuciyar neman na kai" daga nan na ja bakina nai shiru Ita kuwa Fa'iza mgnta ta buge ta da kyau kawai sai ta na tunanin ko kowa ya gane abin da Qais ke yi ne?
Can dai baba ya fita bayan ya tmbyi mazajen mu, nace masa yayi tfyr kwana biyu, yayi masa fatan dawowa lfy, ya fi e daga gidan. Yana fita Hajiya ta ce "ke Fa'iza raba kanki da zaman aure a gidan UBAN KI, lalacewar ba ta kai a ce mijin ki bai da muhallin ijiye ki ba har sai babanki ya baku gidan zama ba". "hjyta ai zan dinga ganin ki kullum ba komai idan a cikin gidan ne ma zan zauna" Hausa suke yi cikin Hausa, na kuma san da wa suke yi amma hjy ta ci darajar idon mahaifiyata don hk ban tanka ba na bi bayan Mamma zuwa ɗaki.
Nan na yini sai dare, sau ɗaya Mamma ba ta min mgnr mijina ba bayan tmbyr ba dai mtsl zaman mu ko? Na amsa mata da babu ta ce "Alhamdulillah, kiyi hkr, kowa da irin nasa kaddarar ta gidan aure, idan kayi hkr sai ya zama tarihi, Allah Ya ƙara muku fahimtar juna Ya kore fitina". Kunya ba ta bar ni na amsa ba amma a raina na amsa Ameen.
*********
Da kallo mai cike da ƙyashi da hassada Fa'iza ta bini da shi don ba hk ta so ganina ba na kwantar da hnkl ba, so tai ta ji na tada bori kuma na ƙi zaman auren, amma ta kula kamar hnkln a kwance ya ke har wani murjewar zama waje ɗaya fatun hannuna suka yi. Hannun ta hjy ta ja su kai ɗaki, suna shiga ta kalle ta "ciwo kike yi ko kika yi, naga kin lalace haka?ko ciki gareki ne?" Wannan tmbyr ta sa kukan da Fa'iza ta ke ƙoƙarin riƙewa ya fito hnkl tashe hjy ke kallonta, tana faɗin Inna lillahi a ranta...da sauri ta matso kusan ta tace "Fa'iza meke faruwa, faɗa min baki da kowa bayan ni da zaki faɗawa". Tana kuka ta zayyane mata abin da ke faruwa, ran hjy ya ɓaci, hnkln ta ya tashi sosai, dole ta san yadda zata yi kada mgnr nan ta fita waje, idan ba hk ba maƙiyanta za su yi mata dariya....
*********
Tun jiya yake yawo a unguwar yana Safa da marwa, don jiya ma bai yi baccin kirki ba, da safen ma sai wani shago ya nema ya sai biredi ya ci ya kora lemun kwalba, ynzn ma zaune ya ke a ƙofar wani gida yana neman mafita, can sai ga wata lafiyayyar mota mai numfashi ta zo shiga gidan kusa da inda ya ke, da sauri ya taso yana lalubar hny da sandar sa ya isa wurin mai motar, yayin da shi kuma mai motar ya fito da kansa don buɗe gate ɗin gidan don babu mai gadi a gidan. Yana isowa ya fara lalubar ɓangaren da ya ji an buɗe, yana zuwa ya fara "Alh. yadda Allah Ya taimake ka, ka taimakani, babu mai son bani ko wane irin aiki ne, kuma ni ina da iyali, ka dubi Allah ka taimaka min" shiru mutumin yayi sannan yace "toh kai ba ido ba wane irin aiki za ka iya kenan?" "Ai Alh makantar a ido kawai ta ke amma ina gani da zuciyata, ka bani ko wane irin aiki ne ni kuma ba zan baka kunya ba" "hmm toh zaka iya aikin gadi?". "Sosai Alh wallahi zan iya nagode". "toh za ka dinga min gadin gidan nan duk da ba nan nake kwana ba, zaka dinga gadi kana ɗan ban ruwa ko shukokin gidan, ka tabbata zaka iya?". "Alh idan na yi wata ɗaya kaga ban maka abinda kake so, wallahi na yarda ka sallame ni". "Toh kana iya fara aikin ka daga yau ko akwai damuwa?" ya ce "a'a Alh ngd" can ya ce "amma Alh zan ɗan roƙi wata alfarma" "ta me fa" inji Alh.
"Ina da ƴar mtsl a kunne na wanda bana jin zance daga nesa sai na zo dab sosai, shi ne nace don Allah kada kayi fushi idan kaga ka yi oda ban ji da wuri ba"
Cikin tausayi sosai Alhn ya kalle shi yana mmkn yadda mutumin nan ke rayuwa, ba ido babu kunne, amma ai shi kam dama ya samu, daman dalilin rashin ɗaukar maigadin sbd kar zancen abinda ya ke yi ya fita waje ne, toh tunda ga wannan bai gani kuma bai ji daidai kenan "babu komai, muje na nuna maka ɗakinka, na kuma nuna maka shukokin inda su ke" nan Alh ya buɗe gidan suka shiga ya nunnuna masa abin da ya kamata ya sani, sannan yayi abin da ya kawo sa gidan ya fice daga gidan bayan ya tmbyi sunan shi ya ce masa Audu Makaho,shi kuma makaho yana ɗan zagaye gidan yana ƙara tantance yanayin shukokin da zai ke gyarawa....
**********
Sai dare sosai sannan Fa'iza ta bar gidan ina jin fitar ta daga ɗakina, wanda tun bayan magriba Mamma ta ce na koma ɗaki don ba ɗabi'a mai kyau bace macen aure ta kai dare a waje matsawar ba mijin ne zai zo ɗaukar ta ba, na girgiza kai ina mamakin yadda na ga Fa'iza ta jeme kamar ba amarya ba....
**********
Kwanan makaho biyu a gidan, mai gidan ya zo da baƙin sa ƴam matasan maza, sanin makaho ba gani ya ke ba kuma bai ji ya sa tun a tsakar gidan ya ke ƙoƙarin rungumosu jikinsa yana shafa su...
Yana gab da shiga ciki, aka kira wayarsa, na ya tura matasan ciki akan bari ya amsa waya....
Hmmmm!
Next page is loading....
Drop your thoughts in the comments section, SBD in san mene kuke tunani?
#sirrinɓoye
#makaho
#master
#oneluv
#hubbifillah🌼🌼Oumm Arfah🥰

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Short StoryMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...