🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 25
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Subhanallah, Wal-hamdulillah, Wa La ilaha illallah, Wallahu Akbar._
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
Ana gama tafiya da su, Master ya fito ya nufi wata mota da ke waje na shi da ya sa aka zo masa da shi. Ya shiga ciki ya kulle kan sa a ciki. Wani wallet na ga ya buɗe ya ciro wani sabon sim pack ya buɗe ya sa a wayar sa, yayi dailing wata number, sai da ya tabbatar da number tana akan waya sannan ya kashe wayar sai ya tura message wa layin...
_Komai kake yi ka bari ka biyo Gama-aiki ga yi nan na turo shi da farar mota, sabuwa ce haka ma yaron sabo ne baka san shi ba, ka tmby shi sunan sa sannan idan ya tmby waye kai, ka ce masa kawai kai ne Alh. Sammani ya ce a ɗauko, ban so ya san sunan ka sbd tsaro, ka hanzarta, hatsabibin yaron nan ne ya shigo gonar mu. Sannan kar ka kira ni, sai ka zo._
Shi kenan abin da ya rubuta ya tura ma numbar sannan ya kira wani yaro ƙanin Ahmad abokin aikinsa. Ya sa shi zuwa gidan su ya ɗau motar sa ya je HQ ɗin su ya yi parking, sannan kada ya ma kowa magana. Ya kuma faɗa masa idan an tambayi sunan sa ya ce Gama-aiki. Ba shi da tabbacin abin da ya ke zargi amma yana fatan tarkon sa ya kama kurciya.*******
Da mamakin abin da ya ji ya ke kallon ƴar sa yace "kin ji wai mahaifiyar ki tana Kaduna, mene ya kai ta Kaduna?" "Kaduna?" Fa'iza ta tmby da ɗimbin mamaki, kana ta yi murmushin baƙin ciki ta ce "kada ka yarda Baba, raina maka hnkl kawai za a yi, amma Haj tana nan garin babu inda ta je, ina zuwa" ta juya da sauri ta juya zuwa ɗaki ta ɗauko wayar ta ta kunna masa wata recording sai ga muryar Haj Atumbulash nan da abin da suke tattaunawa akai tun daga inda Fa'iza ta tarar har iya inda ta dakata duk suna wayar ta naɗo, hnkln Baba ya yi ƙololuwar tashi da abin da ya ji ne, shakka babu wannan muryar matar sa ne Haj Shema, kallon ta Baba ya yi ganin ganin yadda hawaye ke tsiyayo mata ya ce "ya aka yi kika san in da suke?" Nan ta ba shi lbrn yadda ta biyo bayan sa ba tare da sanin sa ba kuma har kawo ynz shi da Haj ba su san ta san komai ba, sannan babu wanda ya kira ta a cikin su. Shiru Baba yayi cikin damuwa sai kuma ya ce "wane irin zama ku ke yi da Qais?" Rufe bakin sa yayi dai dai da shigowar Mamma ɗakin ganin su tare sai ta nemi juyawa amma baba ya tsayar da ita yana tmbyrt ina za ta kuma, ta zo ta zauna, bata musu ba ta zo kusan sa tace "gani nayi kamar kuna zantawa ne, shi ya sa zan ba ku wuri" kallon ta yayi ya ce "yana da kyau ke ma ki ji ko me kenan nan, ko har kin sani ne?" Ya faɗa ya na kallon Fa'iza, girgiza kai ta yi tace "ban faɗa mata ba na gagara faɗa mata" ta faɗa tana ƙara share hawayen idon ta. Baba ya kamo hannun ta yana mai jin tausayin halin da ta ke ciki, ya zaunar da ita gefen sa yace "idan ba zaki iya faɗa ba, shi kenan, duk san da kika shirya sai ki faɗa mana" ta share hawayen idon ta tace "zan faɗa". Nan ta ba su lbrn zaman ta da Qais tun daga farkon sa har ƙarshen sa. Salati kawai Baba ke yi ya na maimatawa, ita kam Mamma ai tsoron Allah ya hana ta cewa komai sai girgiza kai kawai ta ke yi, can Baba ya ce "me yasa baki taɓa faɗa min ba?" Tace "Baba ko na yi niyyar faɗa maka sai Haj ta hana ni, tace wai sirrin aure na ne bai kamata na yi ta yayata shi ba" Mamma ta buɗi baki ta ce "ban yarda Yaya Shema za ta aikata hakan ba, gsky ina ganin akwai inda aka samu rashin fahimta" ta faɗa cikin tabbatar wa, sanin yadda ta ke ɗaukar kowa da zuciya ɗaya ya sa Baba kunna mata recording ɗin nan ita ma ta ji....**********
Bayan ya bada umurnin nan Master can inda ya sa aka kai masa su Alh. Sammani ya je, ya sa aka buɗe masa ya shiga inda su Atumbulash su ke, yana shiga ya gan ta hankalin ta kwance kamar bata da mtslr komai a rayuwar nan. Cikin tsananin tausayin kawun sa ya kalle ta har ya buɗi baki zai yi magana kuma sai ya kasa kawai ya juya waje yasa aka basu abinci dukkan su d manyan da ƙananan su, zai wuce ne ya ji Alh. Sammani na cewa "idan ka isa ka mayar da mu station ɗin ku, ka ga ƙaryar tsiya, da ko kwana ba za mu yi ba amma nan ka zo ka zube mu salon sauraye na ci rabon su a jikin mu, amma ka sani, albishir ɗaya zan maka, duk daren daɗewa sai na wulaƙanta ka yadda ka wulaƙanta mu ni d jama'a ta, ka rubuta ka ajiye" wani shegen dariya Master ya sa sannan yace "to ko can ɗin zan maida ku, in ga wanda ya isa fitar da ku? Ka ke zancen wulaƙanta ni, kafin nan fa? Ka san in da kake ne? Idan ma ka kwantar da hnkln ka, daga can station ɗin na mu ma kotu za mu wuce a yanke muku hukuncin da ya dace, sannan idan a can ma kun nuna iko, wallahi da hannu na zan kashe ka, alƙawarin da na yi kai na kenan kafin na fara aiki, don haka ƙwalelen kare da hantar kura" ya ja jikin sa ya bar wurin Alh Sammani na dukan ƙarfen da su ke wurin kamar wanda ya ci kai. Abin tsoro ya fara ba su, duk tsawon lokacin da suka daukar suna sheƙe ayar su, Ali da wasa ba wanda ya taɓa zargin su balle a kama su, amma wannan ya zamar musu ƙarfen ƙafa, kuma ba su san mene suka taɓa masa ba...
Master na fita waje, ya ga motar da ya aika Hashim ƙanin Ahmad da shi, kai ya ɗaga ya tabbatar komai is standby yadda aya shirya sai kawai ya nufi motar ya buɗe ta yana cewa "sannu da ƙoƙari Gama-aiki, har kun iso kenan?" Hashim ya amsa tare da fitowa daga cikin motar, ya miƙa masa makullin sa, ya ce "a'a dakata yanzu zaka mayar da motar in da ka ɗauko ta" daskarewa na bayan motar yayi, idan har hasashen sa ya zama gaske, wato kenan tarko yaron nan ya ɗana masa, shi kuma ya faɗa ciki...
Fito wa yayi daga motar kallo na bi shi da shi ina mamakin ba dai shi ne ba?
YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Historia CortaMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...