🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah🥰.
Wattpad @oummarfah20Page 9.
_Yaa Fatahu Ka buɗa mana Ameen_.
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Wannan lbrn tun daga farkon shi har ƙarshen sa, ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance, arashi ne_
********* Murya can ciki yayi musu sallama ya shiga ciki ya same su, yau bai yi niyyar zuwa ba amma suka kira akan wani abin gaggawa ya taso kuma ana bukatar ganin sa, da shigar sa dakin tattaunawar na su kawai ya nemi ƙarin bayani, nan suka bashi duk wani lastest update ɗin da suke da shi akan case ɗin. Shiru yayi na ɗan lkc kafin ya numfasa ya ce "lkc yayi da zamu nuna musu cewa kifi na ganin ka mai har koma, lkcn ƙaddamar da wancan matakin ya kai, ku bar koma a hannu na zan baku kyakkyawan feedback in a week In Shaa Allah" daga hk ya tashi ya fice bayan ya musu sallama akan sai monday zai ƙara shigowa, suka mai fatan alkhairi ya fice. Da fitar da bai zame ko ina ba sai unguwar da aka tsananta satan yaran, cikin ruwan sanyi ya samo amsar tmbyr da yayi ya bar wurin ya wuce can farkon anguwar yana ƙara nazarin unguwar da hny mafi sauƙin ficewa idan an shigo unguwar. Yana gama nazarin sa ya bar wurin ya tafi sabgar gaban sa, ya na me ci gaba da tsara yadda zai fito musu....
*********
Kuka take kashirɓan babu mai lallashin ta don tun safe ta kulle kanta a ɗaki bayan ta fahimci abin da Qais ya mata, ta san kuka ba shi ne mafita ba face ta gaya wa Allah, sannan ta ƙudirta a ranta ta gama cin abin hannunsa, don sai ta ci ko sha abin hannunsa sannan ya ke samun galaba a kanta, don bata taɓa yarje mai a cikin hayyacin ta. (Fa'iza mai kyau).
***********
Tun da ya fice da rana bai dawo gidan ba sai ƙarfe tara, ina kan sallayata da na idar da shafa'i da wutiri ina ci gaba da lazimi ina kuma dakin dawowarsa, amma deep down na raya ma raina ba zan ɗauki zaman majalisa ba. Da sallama a bakin ya shigo bayan ina jin yana ta kiciniyar buɗe kofar, na amsa sallamar bayan shigowar sa, daga nan ban ce mai komai ba har sai da ya shiga banɗaki ya fito na tashi na ɗauko masa abin da na sarrafa mana na daren, stir fried cous cous ne, Abdul na aika ya sayo min kayan lambu kafin na yi list na aiki mai aikin gidanmu kasuwa. Sai da na bari ya ci yai gdy ga Allah sannan na matso kusan shi na buɗe baki na ce "amm don Allah wata magana zan maka amma idan ka ji haushi kayi hkr...." "Abdurrahman sunan" ya katse Ni da faɗar sunan sa, na maka mai harara a raina nace "mene ya dameni da sunan ka?" amma dai sai na cigaba kawai da maganata "daman zan ce maka ne idan ban takura ba, don Allah ka rage kai wa daren nan a waje". "Kin damu da ni ne kina tsoron zan ɓata ko me?". "ko ɗaya kawai ban son yin daren ne a waje" nace tare da juya kai, jira nake na ji ya ce ba zai yiwu ba, amma ga mamakina sai ji nai ya ce "tohm amarya an gama, ai komai kike so, za a yi" da sauri na kallo shi, rai na ɓaci ya ke idan ya ce min amaryar nan, cikin gunaguni nace "Ni a daina ce min amarya" ban yi tunanin ya ji ba don a hnkl na yi mgnr, amma sai ji nayi ya ce "toh uwargida an gama".......let's be sincere ba zan ce ina jin daɗin ina auren makaho ba amma a ƙasan raina ban da fargabar wata rana zai ga wata ta fi ni kyau har ya magantu akan halitta ta, wannan kawai ke sani jin na shirya zama na har abada da wannan ɗan makahon....
Muna nan kowa yayi zaman shiru can ya ce "ba ki tmby ni komai game da ni ba, ko baki son sanin wa kike aure?"
Kaɗan na kalle shi kamar ba zan ce komai ba sai kuma na ce "ko ban san ka ba, mahaifina ya yarda da kai ne ya aura maka ni, toh ni kuma ba zan bijire wa zaɓin babana ba" yayi ƴar dariya kaɗan sai ya canza mgnr da faɗin "ɗan kunna min tvn nan na ji lbrn dare" da gatse na ce mai "ni ban iya kunnawa ba". Komai bai ce min ba na ga ya tashi da lalube ya nufi tvn yayi ƴan taɓe taɓen sa ina kallon sa yana ƙoƙarin haɗa wayoyin wuta, ni kam ina gefe ina kallon ikon Ubangiji, can dai ya ga da gaske bai san in da socket ɗin ya ke ba sai ya hkr y koma ya zauna.
Tausayin rashin idonsa ce ta kamani har na tashi na haɗa masa tvn sai ji yayi mgn na fita, da murna sosai ya ce "Ngd". Nan na sa mai channels don su suna lbrn dare ƙarfe 10, ina gama haɗa mai na wuce bayi don watsa ruwa kafin na kwanta....
**********
Kwana biyu tsakanin nan, Abdurrahman makaho ya na gida bai je ko ina ba, sai dai yau da zai fita ya ɗebi kaya kala biyu ya ce min "uwargida, zan ɗan yi ƴar tafiya ta kwana biyu, zan je ƙauye" ya miƙo min ƴar wayarsa "ɗan sa min lambar wayar ki, idan na je zan kira ki" na amshi wayar ina mamakin wannan bawan Allahn, shi da bai da ido, ya za ayi ya san lambar da zai kira? Kamar ya san tunanin da nake sai ya ce "ki saita min shi yadda ina danna 1 lambar ki zata kira" hakan kuwa na sa mai na miƙa masa tare da addu'ar Allah Ya tsare, Ya kiyaye hny, Ya kuma bada sa'a" da Ameen ya amsa min sannan ya fice bayan na nemi iznin zuwa gaida iyayena, ya yarje min amma ba a ranar ba don hk na kwana da shirin shiga gidan mu bayan kwana takwas da tarewa ta......
***********
Shiryawa ta yi tsaf tana jiran ta ji fitar sa daga gidan don a yau ta yi niyya babu bashi gidan su za ta je, ƙilan idan ya ga ba ta nan a gidan yayi ma kansa karatun ta natsu.
Can bayan kamar mintinan da ba su wuce arba'in ba zuwa da biyar ta ji fitar motarsa da ga gidan, ta san wannan fitar sai ƙarfe 11 na dare... Tsaf ta fito ta yi shiga irin ta matan manya babu mai ganin ya ya ce tana cikin wata mtslr gidan aure, ta fara koyan tuƙin mota, amma ba ta ja ba sai ta fita bayan ta sallami maigadin da abincin ranar sa ta fita ta tari a daidaita shata ya kai ta har kofar gidan wanda yayi dai dai da rufo ƙofar da nayi ni ma zan shiga cikin gidan, shigar jikina normal shiga ce da hijabi har ƙasa na ɗan jawo shi fuskata kaɗan, kallon kallo muka yi a tsakanin mu, sannan na rufe ƙofa ta ita kuma ta biya mai a daidaita tana nufo gidan kanta tsaye nan muka yi clashing a ƙofar shiga gidan.....
Wow! Ga amarya Fa'iza ga amarya Rahmatullah, mene kuke tunani?
Mene zai zama makomar rayuwar auren mai kyau?
Wai shi wannan makahon, waye shi?
Shin su Master za su yi nasarar kama waɗanda suke aikata wannan ɓarnar?
Mene ne plan ɗin Master ne?
Jst keep following 🥰
#family
#sisters
#marriagelife
#angoqais
#angoabdulmakaho
#hubbifillah🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Cerita PendekMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...