21

22 2 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
  *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
   Wattpad @oummarfah20

Page 21

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

   _Allahumma Inna Nas'alukal Hudaa, Wat tuqaa Wal Afafa Wal Ginaa._

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

*******

    Da soyayya sosai mai cike ƙaunar uwa zuwa ga ɗanta ta amsa "lfy lau Babangida, ya aikin? Ka taho ne?" Ya ce "a'ah amma na kusa tahowa, ki kwantar da hnkln ki, tunda nace zan zo ai zan zo, kada ki damu" ta ce "Toh babana sai ka zo, kayi tuƙi a hnkl" daga ta kashe wayar ta daidai shigowar baba ɗakin daman ya fita bata tadda shi ba, da farin cikin ganin ƴar uwarsa ɗaya tilo ya nufi inda ta ke ba tare da ya kula su waye a ɗakin ba, ya zauna kusa da ita yana kallon ta cike da kewa. Ita ta katse shirun da faɗin "kai yaya wannan kallon fa?" Yayi ƴar dariya sai sannan ya kula su waye a ɗakin, na gaishe shi, sannan mijina ma suka gaisa. Bai tmby me  ya ke a wurin ba, don yasan tunda Rahmatu ta ce zata yi Toh ba ƙaramin abu ne zai hana ta yin ba, sai ikon Allah, ganin baba a zaune sai na miƙe zan shiga ɗakin Mamma don na basu damar ganawa da ƴar uwar sa, baba ya kalle ni kamar kullum ya ce "ke kin tashi, mijin naki ni zan ce masa kin tashi, ku je ɗakinku na da da shi kafin yayan naki ya zo ko?" Sai ya waiga ya kalli mijina ya ce "sannu Abdurrahman wannan matar ta ka kana fama, sai hkr, tashi ta yi maka jagora ku jirayi yayan na su" yana rufe baki Aunt Rahmatu ta ce "ita ke fama ko shi ya ke fama, Yaya kasan takwara bata laifi ko" ta faɗa tana turo baki kamar yarinya za ta yi shagwaɓar da ta saba masa, baba ya yi dariyar nishaɗi ya ce "af haka ne na manta takwararki ba ta laifi ke ma haka, toh kai ka ji fa, idan kana son ku zauna lfy da wannan surukar ta ka sai ka yadda ƴarta bata laifi, idan ba hakan ba babu ruwana" ya ƙarasa zancen sa yana kallon ɓangaren Abdurrahman, shi dai mijin nawa sai aikin murmushi kawai yana tsaye, ban san inda zai bi ba, ni kuma ban zo na kama shi ba, sanin ba zan kama shin ba yasa baba kiran ƴar uwarsa zuwa ɗakin sa bayan ya ƙara ce min na shiga da mijina ciki...ni fa kiran da baba ke masa na mijina fa kunya nake ji, me yasa ba zai kira shi da sunan sa ba? Na ƙarasa gare shi na ce "mu tafi idan ya zo sai mu dawo" har na yi gaba bai biyo ni ba na waigo na ce "muje mana" ya girgiza kai ya ce "ɗa na gari umurnin iyaye ya ke bi, ce wa akai mu jira a nan, ko ba ki don na ga ɗakin da matata tayi ƴan matancin ta ne" da dai na kula magana ya ke neman ja kawai sai na kai ma sandar gefen sa cafka da niyyar na miƙa masa ya kama na yi masa jagora zuwa ɗakin, hannu na bai sauka a ko'ina ba sai kan hannun sa da shi ma ya kai zai ɗau sandar... Da sauri nai yinƙurin cire hannu na sai dai na makara don da saurin gaske ya cafki hannu na kuma Allah Ya ba shi sa'a ya cafka ɗin, gam ko ya riƙe ya ƙi saki duk da yinƙurin ƙwace hannun da nake yi.
    Miƙewa yayi yana riƙe da hannun nawa yace "daman wallahi bai kamata ina gida kuma ki na nan ba na dinga neman hanya da sanda ba, kamata yayi ki zama idanuna idan na dawo gida, mu je to na san daman abin da kike so kenan" daina yinƙurin ƙwacewa na yi na koma kallon sa da mamaki, kawai sai nai gaba yana bi na a baya hannunsa cikin nawa yana mai kuma cewa "mu je ɗakin sai ki kalle ni da kyau nan wasu na iya shigowa" ban tsaya ba sai a ɗakin na jira ya shigo na tura ƙofar har lkcn bai saki hannu na ba, ya yi gaba yana nausawa cikin ɗakin, da kallo na bisa ina mamakin yadda ya ke ƙoƙarin neman wurin zama, ban san ya akai ba kawai ganin shi nayi ya faɗa kan katifa ta wanda shi kaɗai ne a ɗakin ynz, an ɗauke na Fa'iza, faɗuwar sa ta sa dole na bi shi tunda hannunsa na riƙe ne da nawa, aiko sai gani malemale a kan sa... Yunƙurawa nayi zan tashi ya sa ɗayan hannun sa ya rungumo ni sosai jikinsa, ya lalubi kunne na ya ce "tunda kullum kina min wayau ki yi ta kallo na, ni kuma ba ido gare ni ba balle na kalle ki ba ai sai ki bari na rama kallon ta wata hanyar ko" ba maganar kawai ya ke yi ba, a'a multitasking ya ke yi wato fiye da abu ɗaya a lkc ɗaya...
    Maganar na fita ne tare da wata sassanyar iska da nake jin sa tun daga tsakar kai na har ƙaramin yatsa ta, sannan hannun sa duka biyu yawo suke a jikina. Idan na ce ina cikin natsuwa ta na yi ƙarya, don wani yanayi na shiga, da har na yi fatan dauwama cikin ta. Yanayi ne da na jima ina hasashen sa da mijina abin so na. Tsayin wani lkc ban kula da abin da na ke aikatawa ba sai da na ji kamar ana ƙoƙarin zare min rigar jikina wanda ban ma san yaushe aka cire zip ɗin ba, ni kuma ashe tuni na ba shi haɗin kai ta hanyar shafar duk inda hannu na ya kai, ko da na yi tunanin ƙwace kaina kamar ya san me nake tu,,nani, ya ƙara nanuƙe ni jikin sa sosai ya faɗa da murya shaƙe "don Allah, yau ɗaya ki bar ni, na rage"   ban saurare shi ba na cigaba da yinƙurin ƙwacewa sai dai ya nuna min duk inda mace ta ke jin ta, bata kai ya namiji ƙarfi ba. Sai da ya samar ma kansa ƴar natsuwa sannan ya bar ni da kyar bayan na ishe shi hi da magiyar don Allah ya kyale ni kada a shigo".  Tsawon lkc ban kalli inda ya ke ba, don a karan kaina kunyar kaina nake balle inda na tuna abin da kunnuwa na suka dinga jiyo min daga bakinsa, zip ɗin riga ta na mayar don ba yarda an cire rigar ba, da ƙila abin sai ya wuce haka...  A hankali ya sauka ya na neman hanyar fita don an bar sandar a falo, fatan sa ya bar gidan ba tare da wani ya gan sa ba, Allah Ya taimaka glass ɗin da ya ke sawa mai duhu ce, ba lalle a fahimci halin da ya shiga ba. Da ikon Allah har ya fice daga gidan ya shige nasu ɓangaren bai ci karo da kowa ba, yana shiga ciki ya shige banɗakin kawai yana mai dana sanin aikata ganin ya na ƙoƙarin ɓallo ma kansa ruwa...duk tsawon shekarun ƙuruciyar sa har kawo ynz, shi mata ba sa gaban sa sanin bai da abin ba su, amma ga Rahmatullah Muhammad Abdullahi na shirin karya lagonsa...

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now