20

23 2 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
   *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20

Page 20

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

  _Astagfirullah wa atubu ilaihi._

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne, suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne_.

*******
Ba kowa ba ne face Alh. Na Manzo, ta tuna lkcn da ya gabatar da shi a gare ta matsayin kawun sa wato ƙanin mahaifiyar sa, toh meye haɗin kawunsa da harkar yaran nan, gashi da alama ba abin arziƙi ba ne duba da yadda hankulan yaran ya tashi su ke kuka, sannan idan ba ƙarya ta yi ba, kamar kallon sha'awa ya ke wa yaran, kai ba zai zama gaskiya ba, anya mene ya kamata ta yi, da sauri ta koma ɗakin ta ta ɗauki waya za ta kira, tana unlocking wayar hannun ta ya danna Radio ɗin da ke akan fuskar screen ɗin wayar ta, ba ta tsaya kashewa ba kawai ta fita ta shiga contact don neman wanda zata kira, sai dai kuma bata ma san wa zata kira ba, hakan ya sa ta dinga neman wanda zata kira, ba ta kai ga yanke shawarar wa zata kira ba, ta ji sanarwar ɓatan yara da roƙon Allah Ya kawo karshen mugun aikin su...
   Sosai hnkln ta ya ɗauku ga lbrn don ita ba mutum bace mai jin labarai ba sai ta natsu inda ta ji cigaban tattaunawar masu gabatar da shirin suna ƙara tir da masu aikata hakan ga yara har ya kai ga yin ajalin yaran. Jin yadda abin ya ke ne ya tashi hnkln ta fiye da ƙima, babu wani tunani kawai ta danna kiran mahaifiyar ta, tana fatan ta samu shawarar abin da ya dace ta yi don kanta gaba ɗaya ya kulle. Haj na ɗaga wayar ko gaisuwar kirki bata tsaya ba ta faɗa ma hajr abin da ke nan, jim kaɗan hajr ta yi kafin ta ce "kin ga natsu ki faɗa min ban fahimci me kike faɗa ba".   Natsuwar ta yi ta sake maimaita mata abin da ke faruwa. Hajr na gama sauraren ta ta yi yar dariya ta ce "har kin sa gabana ya faɗi, na zaci wani babban abu ne, yanzu ke sai ki yarda mijin ki na aikata hakan ne? Ƙarshen ta yaran nan ne da ake turowa aikatau daga ƙauye, ko an faɗi fasalin yaran ne a rediyon?" "A'a" ta bata amsa "Toh akan me zaki zargi mijin ki da aikata irin wannan mugun aikin? Kin faɗa ma wani ne bayan ni?" Nan ma ta ce "a'a"  Haj ta ce "Toh ki bar shi a mu biyu kada ma zancen ya fita ran mijin ki ya ɓaci, kin ji? Kuma kada ki sa komai a ranki, yaran nan aikatau su ka zo" da haka Haj ta kashe zancen yara daga bakin Fa'iza. (Kash Haj!).

*******
  Ban fito banɗakin ba sai da na tabbata ya fice, na yo alwala na fito jiki a sanyaye. Na kasa manta yanayin da na shiga a ɗan tsakanin nan, ni ba yarinya ba ce na san mene ne na ji a jikina, na kuma san idan aka cigaba tohm ina gab da kunyata kaina, don ni mace ce mai tsananin sha'awa, hakan ya sa ko labaran soyayya ban karantawa sai na horror da na faɗa, hakan yasa har yau na gagara gama krnt accidentally married to the CEO... Numfashi na sauke ina ƙara da na sanin shan abubuwan da na dinga ɗura min kafin aure don na san har da su a sanya ni a halin da na shiga...fatana kar ya kuma zuwa gare ni da irin wannan abin na san ba zan iya riƙe kai na ba kuma...

*******

   Master idon sa yayi ja amintattun yaran da za su iya masa aiki a sirrance ya ke neman bayan na group ɗin sa don a ƙalla yana buƙatar ƙarin mutum goma zuwa sha biyar bayan huɗun da ya ke da su. Yanzu ya samu takwas saura kusan goma, amma kafin nan ya yanke shawarar fara amfani da wanda ya ke da su a ƙasa. A keɓance ya gana da yaran kowa aka ba shi ɓangaren da ya fi ƙwarewa akai, nan kowa ya maƙala ɗan abin magana a kunnan sa don samu damar sanin halin da kowanensu ke ciki, nan ya fito ya bar su ya nufi gida don fito da kayan aikin da ke a dakin sa na sirri.
   Cikin wani irin dogon gini ya yi ma kansa da kayan aikinsa masauki da ƙudurin ba zai bar wurin ba sai sun cimma nasara da izinin Allah.
   Computer ɗin sa ya yi connecting ya kunna nan ta ke sai ga hotuna masu motsi wato video suna nuna cikin ɗakunan wasu gidaje, da ido ya bi su ɗaya bayan ɗaya har idon sa suka sauka akan wani gida da aka shiga da mota babu jimawa aka kuma fita bayan an ɗauki wani ƙwarya kamar na tsafi, da sauri ya kira batch A ya aika musu da address ɗin gidan suka tafi da hanzari. Can kuma ya hango wani gidan shi ma an shiga an fita an kuma shiga can an jima kuma sai aka fito, nan ma ya kira batch B ya tura gidan su bincike gidan duka ko za a samo wani hints a kan yaran... (Allah Ya ba da Sa'a)

******

  Fa'iza hankalin ta ya kwanta da jin zancen Haj, ita ma dai ta yi rashin tunani, me yasa zata yi tunanin mijin ta ta aikata wannan mummunar aiki ba, sai kawai ta natsar da hankalin ta ta cigaba da sabgar gaban ta. Uhmmm

******

  Tunda ya fice bai dawo ba sai bayan isha'i sosai, ni kam ina nan hnklna bai kwanta kawai ina kwance ne kawai sai da na jiyo sallamarsa, akwai alamun gajiya sosai a cikin muryarsa, har sai da na ɗago na kalle shi na ga jikin sa sanyaye, sannu nai masa, ya amsa tare da tmbyr ko ina da abin sa wa a baka? Tashi nai na zubo masa abin da na dafa fried spaghetti ya ji kayan lambu sosai don ki da kaina yau sai da na yabi girkin, ba kaɗan ba yayi daɗi sosai. Na haɗo mai da zoɓon da Mamma ta aiko min da shi bayan na kira ta ba Abdullahi veggies ya kawo min. Sosai ya ci abincin ya kuma sha zoɓon. Ina kallon sa ya kishingiɗa a kan kujerar, na zo na kwashe kwanon na kai kicin na wanke, kafin na fito har ya shige banɗaki, ban jira ba na kwanta abina amma ban yi bacci ba don zan ba shi saƙon baba na zuwan mu gobe su gana da Aunt Rahmatu.  Ba jimawa sosai ya fito ya zo bakin katifar ya zauna ya ce "ranki ya daɗe kin yini lfy?" "Lfy lau" na ja bakina nayi shiru, shi ɗin dai ya ƙara cewa "yau girkin yayi daɗi har da zoɓon, Allah Ya ƙara zaƙin hannu"  "Ameen". Nan muka yi shiru, can dai na ce "uhmm ɗazu baba ya aiko a tuna mana zuwan mu gidan ku gana da Aunt Rahmatu idan ta zo gobe idan Allah Ya kai mu" baki ya buɗe alamun mantuwa "kin san sam na manta zancen zuwan ta gobe, uhm tsoron haɗuwa nake da ita kada ta ce ban mata na sakar mata ƴa" ya faɗa cike da damuwa. Karo na babu adadi tausayin sa ya ƙara kwaranya cikin ƙirjina,  "Aunt Rahmatu ba ta da tsauri sosai ka kwantar da hnkln ka, tana son abin da nake so ko mene shi" na faɗa cike da tausasa harshe, wanda ban ma san yaushe na tausasa ba. "Da gaske kina son makahon nan?" Ya faɗa da rauni tare da tausayin kai. Sai sannan na tuna zancen da nayi sai na gyara zance na da faɗin "ba abin da kake tunani ba ne, kawai duk abin da nake ra'ayin sa, toh ita ma tana yin abin"  "toh shi kenan tunda hakan ki ka ce, Allah Ya kai mu goben da lfy" "Ameen" na amsa ina mai gyara rufar jikina. Jin bai motsa ba ya sa na kalle shi, kamar ya san ina kallon sa ya ce "don Allah ranki ya daɗe, yau ɗaya a bar ni na kwanta nan, yau na wahala ga jikina duk ciwo suke".
   Wannan karon ma zuciya ta ce ta tsarawa ƙwaƙwalwa ta abin yi, ji na yi kawai ina furta "in dai baka juye juye har da zaka ture ni, toh ka kwanta ɗin amma a can bakin gadon" da sauri ya kwanta yana faɗin "Nagode, ba za ma ki san ina nan ba sbd yadda zan natsu" ban tanka mai ba na ɗauko filo na sa a tsakiyar mu.   (ASUBA TA GARI... Abdur/Rahma).

******
Da safe bayan mu gama abin da za mu yi, na shiga cikin gidan shi kuma mijina na fita akan idan ta zo na kira shi zai dawo.... Sai bayan azahar Aunt Rahmatu ta iso gidan, zo ku ga murna wurina kamar an min kyakkyawan albishir. Bayan ta natsa an gama ɗan gaggaisawa ta nemi ganin mijin nawa, na sanar mata ya fita amma na kira shi yana zuwa, ta ce "ba komai kafin ya iso Babangida ya iso, shi zan sa ya tantance min shi, idan ya ce bai yi ba kuwa toh ki sani ƙafata ƙafarki"  sosai gabana ya faɗi don na san Babangida ɗan ta farin sani, ɗan sandan farin kaya ne kuma riƙaƙƙen mugu ne, na san baƙin halin sa na iya sawa na rasa mijina. Ba jimawa sosai mijina ya iso, na kawo sa har falon Aunt ta fito ya gaida ta, bata wani ɗaga masa ƙafa ba kanta tsaye tace "ka ji labarin ba a son raina ka auri ƴata ba ko?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta ci gaba "yanzu yayanta zai zo sai ka shirya haɗuwa da shi, sai abin da ya yanke, bari na kira shi na ji ina ya ke" ta ɗauki waya tayi dialing numbar Master. Ringing ɗaya ya ɗaga sai ka muryar Master tarwai ta cikin wayar "Aslm Mamana"....

    Ga Master ga Makaho! Saura me? Shin ya haɗuwar ta su zata kasance? Mene kuke ganin zai faru? Ku faɗi ra'ayoyin ku a cikin comments.

#master
#makaho
#rahma
#auntrahmatu
#kidnap&assault

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now