9

38 2 2
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
    *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

    🌼🌼 Oumm Arfah🥰.

   Wattpad @oummarfah20

Page 9

_Wannan labarin ƙirƙirarre ne, suna halayya, ko wani abu mai kama da na wani ko wata arashi ne_.

    Allah Ya jiƙan magabatan mu. Ameen.

*****Kamar a mafarki na ji maroƙiya na shelar auren Rahmatullah da Abdurrahman, na ɗan lkc sai da na manta suna na ne wannan domin tunanin ni ce ma bai zo min ba, sai da Anty Yagana ta shigo inda nake a sanyayye.

  Dafa ni tayi sannan ta fara shafar bayana alamun rarrashi.

Na kalle ta na ce "anty na hkr fa, nasan wanda ya fi ni sonsa ne ya karɓesa, kuma na san Allah na sane da ni bai manta ni ba".

Ganin yadda ta ci gaba da kallo na cikin tausayi ya sa wani tunanin ya zo min " anty mene ya faru?"

"Kiyi hakuri Rahma, hakika Allah Ya karɓi bawansa Khalil ne sbd wani baya auren matar wani, daman can ke ɗin ba matar wanin sa ce ba shi, kiyi biyayya ga sabon zaɓin Allah da na mahaifin ki, In Shaa Allah ba zaki yi nadama ba".

Sototo nayi da kai ina mata kallon ban fahimta ba...
"Rahma an ɗaura aurenki da wani wanda ba zai taɓa ƙin ki ba and karamcin Mahaifin ki" ji nayi kamar ɗakin na juya min sbd zancen da bai samu wurin zama a cikin kai na ba... Can na ji anty na kiran sunana ashe wai sumewa na yi....

**********
"Lokacin da zamu ƙaddamar da wancan matakin ya kai" "ba mtsl duk yadda kace hakan za a yi" aka fada ta cikin wayar... Ajiye wayar yayi yana tunanin idan yau bai fitar da abin da yi kwanaki bai fitar ba akwai damuwa, kuma wannan karon fatan sa a samo yaron da bai kai sha biyu ba, don akwai satisfaction sosai a tare da kananan yara fiye masu ɗan wayon. Wayar sa ya ƙara ɗagawa yayi dialing wata number, can aka ɗaga na jiyo muryar wani namiji "hello alhajina" "ka zo yanzu ina buƙatarka" daga hakan ya kashe wayar sa, ya hau saman ya jira wanda ya kira ɗin.
(Astagfirullah! Allah ka yafe mana ka shiryar da masu rabon shiryuwa, Ameen Yaa Gaffar)

***********
  Tafe ya ke yana tunanin halin da ya jefa kansa babu dogon nazari ko tunani, what if yarinyar ta ƙi shi? But, ya san shi kam cusa ma ran sa son ta ko dan yadda ƙaninta ke son shi da yadda baban ta ya ba shi ita ba tare da la'akari shi ɗin nakassashe ba, kuma nakasa mafi muni *makanta*. A daidai hanyar da ta raba layin biyu ya jiyo ihun kuka da kokawar ƙwace kai da wata murya kamar ta yara ke yi ya sa ya bi wurin da ɗan saurin gudu sai dai kafin ya ƙarasa har an ɗauke yaran cikin takaici ya ƙarasa can bakin hanyar amma babu ko motsin mutum bare dabba. Ciza yatsa yayi yana fatan ranar da abin nan zai zo ƙarshe, wato sata da garkuwa da mutane...

*******
  Yau Lahadi kuma yau ne aka shirin miƙa amaren dakin su ko nace amarya, don ni kam ba zancen inda za a ajiye ni, kai tun juma'ar da na sume sai a ranar jiya asabar na farko na ganni a asibiti.

*** sai dai abin mamakin maimakon abokan ango da aka sani da ɗaukan amarya, toh Fa'iza dai abokan baban ango ne suka zo ɗaukar ta harda so called uncle ɗin sa, duk motocin ɗaukar amaryar manyan alhazzai ne masu jan ta, haka dai duk ƙawayen amarya masu fatan samun dace da abokan ango suka mai da kwaɗayin su... Har a wurin siyan bakin amarya ma waɗannan alhazan ne suka siya bakin amarya suka biya sannan suka fita tare da qawayen amarya za a mayar da su gidajen iyayen su don sun ce babu mai kwana, Qais ɗin ne ya tafi rakiyar su daga nan ya rufo kofar ya dawo gun ƴar amaryarsa mai kyau... Babu zancen sallah daga cin kayan maƙulashen da alhazan nan suka taho da shi, shi kenan aka shiga babbar sabgar da ta sani jan ƴan matan ƙafafuna na koma gidan Alh. Maizare wurin amarya Rahma ta Abdurrahman...

***** An ɗaga nawa tarewar zuwa wani satin domin a bai wa makaho Abdurrahman neman wurin ajiye ni, wanda har yau ban sa shi a idona ba, amma tunda na ji shi aka aura min na tattara da shi da auran nasa na watsar a gefe kawai nasan ko ma me zai faru nan gaba ba zan haifi yara yadda na ke fata ba, don nasan aurena da shi tamkar na koma gidan ƙanin babana ne, don idan suna tunanin zaman aure zan yi uhmm mafarki su ke ko wata Rahmar daban ba ni ba.
Kullum zai shigo ya gaida iyayen na da safe da kuma yamma amma bai taɓa nemana ba, kamar ya san ban bukatar ganin sa.

Abdul ya fi kowa murnar auren nan gani ya ke ynz babu mai raba shi da abokinsa....

******
   Yau tsawon kwana biyar kenan, amma ya gagara neman gidan da zai ajiye ni wanda zai iya iya, don carbi da mafitai ya ke sari yana sayarwa a bakin masallaci...

Ganin lkc ya tafi bai ce komai ba ne baba babu shawarar kowa ya kira masu gini aka yi iyaka tsakanin ɗakin soron nan da cikin gidan mu, aka toshe kofar ɗakin da ya fito ta soro aka fada wani yana kallon waje, daman tsarin ɗakin akwai bayi, nan baba ya sa aka fitar da wani ƙaramin ɓangare nan aka zuba min ƴan tarkacen kayan cikin sauran aka bar su nan wurin Mamma.

A dakin kuma aka cire katifar aka sa wata wacce ta fi na farkon girma, sai kujerar 2-seater ɗaya kawai, ɗan ƙaramin plasma tv aka sa min aka bar babbar a cikin gida da ƴar ƙaramar fridge.

Nan ɗakin yayi gwanin sha'awa labulayen da Centre Carpet ɗin duk matching colours ne da kujerar da sallayata.

  Ana gama wannan gyara baba ya kira shi ya ce ya bar neman gidan ya zauna a nan kafin baban ya san abin yi nan gaba.

Bakin sa kasa rufuwa yayi, yana murmushi ya na hawaye, mene zai biya wannan mutumin da shi? A ba ka ƴa sannan a ba ka inda zaka ajiye ta? Me zai masa ban da kyautata ma wannan ɗiyar alfarma da aka ba shi?
   Sai da ya shiga yana lalube, ya ruɗe da kayan da ya ke da tabbacin gara ne a gefen kicin ɗin, zare gilashin idon sa yayi ya share hawayen idonsa...ya ɗaga kai yana gode ma Allah Ubangijin talikai...( Allah Ka taimakawa masu son su taimaka mana, Ka faranta wa masu son su faranta mana Ameen).

  Ranar lahadi sati ɗaya da tariyar Fa'iza aka miƙa ni gidan nawa mijin ko in ce ɗakin mijin... Ko da zai shigo da yamma shi kaɗai ya shigo sai jakarsa kamar ta wanzami da kullum ya ke rataye da shi sai Abdul da shi ne yayo mai rakiya bakin ƙofa kafin ya juya ba tare da ya shigo ba...

"Aslm Alkm" "wslm Alkm" kawai nace ya ja baki na na tsuke, ina kallonsa cikin takaici yana laluben hanya ganin zai bige da kujerar ne ya sa ta ɗauke kai, shi kuwa bai san da kujerar ba sai da ya buge sannan "Inna lillahi, subhanallahi" ya furta yana kama gefen kujerar, ko kallon sa ban yi ba bare yayi tunanin in ce masa ya hkr...

"Sannu ina wuni" na jiyo muryar sa, kallon sa nayi da kyau na ganshi zaune a ƙasa ya kallon inda ya ke tunanin nan nake zaune. Babu kunya na amsa
"Yauwa sannu" ya turo ledar gefen shi ya ce

"don Allah ɗan ɗauko faranti ki juye wannan ban saba da kicin ɗin ba tukunnan kada na miki ɓarna"

Kamar ba zan ta shi ba sai kuma na miƙe tunawa babu ruwan Allah idan ban ma mijina biyayya ba...

#Astagfirullah
#aurebautarAllah
#purelove
#geniuelove
#fakelife
#fakemarriage
#vote
#comment
#share

🌼🌼 Oumm Arfah🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now