2

37 2 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼🌼
          *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa...

🌼🌼Oumm Arfah🥰.

2.

    Yau ma kamar ko wacce ranar islamiyya, muna tafe da ƙanina mun taso daga makaranta wacce take nan ƙasan layin mu, don mu kan iya zuwa a kafa mu dawo. Yau dai mun yi dare don wasu masallatan har sun fara alwalar magriba, wannan yasa nake ta jan hannun Abdullahi don mu shiga gida kafin babanmu ya ankara cewar ba mu kai ga isa gida ba har magriba. Wani irin ihu Abdullahi yayi wanda ya bani tsoro ba kaɗan ba har sai da gefe a tsorace ina jan sa gefe, gudun abin da ya gani ya cinye mu.
   Wani shegen tsaki na ja dana ga abin da yake ma wannan ihun tsiyar, wani makaho ya gani yana tafe da ƴar sandarsa da wata kullin kayan a ledar gari yayi zafi yana gab da fadawa cikin kwatamin da ke nan kan hanya, da saurin gaske, Abdullahi ya kwace hannunsa cikin nawa yayi kan makahon nan ya taimaka masa ya dawo hanya dai-dai, ban san me mutumin ya ce mai ba na dai ga ya nufi masallaci da shi ya nema masa buta da ruwa ya bashi, sannan ya juyo ya zo ya same ni in da na ke tsaye ina jiransa, da zuwansa kawai jan hannun sa na yi muka nufi gida. Da zuwan mu kofar shiga gida mu ka tarar da Fa'iza a cikin motar kofar gidan tana zance da saurayin ta Idris, wanda motan ta sa ce. Ko kallo na biyu ban kuma yi musu ba, mai wucewa ta cikin gida da sallama a baki na. A bakin kofar shiga falon na tarar da Umminmu na san rashin dawowar mu ta ke da tsoron kar babanmu ya shigo gida ba mu nan.
  Gaisheta muka yi sanan mu ka shige falon, da shigar mu Abdul bai ko bari mun huta ba, ya fara bai wa Umminmu labarin makahon nan, girgiza kai Ummin ta yi cikin tausayin sa, na kalle su kawai don in da sabo to na saba da wannan halayyar ta su, Ummin mu mace ce marar hakuri idan an shiga gonar ta, amman deep down Wani irin zuciya ta ce da shi mai tsananin rauni, don karamin abu ka iya hanata bacci...cikin dakin mu na shige na canza kaya na, ina cikin canja kaya Fa'iza ta shigo ciki ta na waqar soyayya. Ko kallan juna ba mu yi ba ko wacce ta ci gaba da abin da ta ke ganin mai kyau ne, Ni dai shirin sallah nayi don an tayar kam ma, ita kam Fa'iza ina ganin period ɗin ta ne ya zo, don kwanciyar ta yi tana cigaba da dannan wayar ta.
    Sunan muna daki ɗaya ne kawai da Fa'iza amman sai mu yini a daki amma magana wannan ta fatar baki bata haɗa mu ba, tun ina bin ta har na gaji ni ma na daina. Ina iddar da sallah na yi azkar ɗina na maraice da sauran addu'o'ina zuwa sanda aka kira isha'i na miƙa ta wanda koyarwa ce ta mahaifiyata, ina idar da sallah na fita naci abincin dare wanda kowa ke haduwa a falo a shimfida ƙatuwar tabarmar cin abinci a ci tare dukkan gidan, wannan kuma doka ce ta maigidan.

***********
  Washegari da sassafe, Abdul ya zo yana buga kofar dakin mu tare da kiran sunana, na fito da ɗan hanzari na ina tambayarsa ko lfy? Abinda ya fada min ta sa na kusa mangarin shi a fuska...budar bakin sa ce min yayi "Anty nayi mafarkin wannan makahon". "Tohm da ka yi mafarkin shi sai aka yi yaya? Mal. Audu?" Ya kalle ni fuskar sa zar tausayi "ka ɓace min daga nan ko sai na kai maka mari?" Haka ya juya ya tafi yana jin kamar ya tafi ya nemi makahon nan, ni kam cikin takaici na juya daman yanzu na gama zikirin safiya nace na ɗan kwanta kafin 7, shi ne wannan ɗan albarkan ya taso ni daga kwancen, wayata na jawo na kunna data na shiga facebook ganin ba abin nishadi a nan sai na koma WhatsApp, shi ɗin ma ban jima ba na sauka ganin Salisuna baya online, don dama ni social media apps biyun nan kawai na ke yi kuma su kaɗai garan. Nan na shiga Wattpad na ɗan taɓa karatun littafin da na ke karantawa na turanci mai suna Accidentally married to the c.e.o... jin idanuna na rinjayata sai kawai na kifa wayar na baiwa idanuna abinda suke muradi wato bacci...

*********
    A cikin kwanakin da su ka biyo bayan larabar nan sai da na yi yunkurin marin Abdul ya fi sai ashirin. Don ranar Lahadi ma muna dawowa daga islamiyya ya dameni da zancen shirmensa wai bai ga makahon nan ba jiya yau ma haka, ko makahon ya tafi ne? Jin ban tanka mai har da jan hijabi na kan na jira shi ya je massalacin nan ya duba...ai kam yana rufe baki na bi keyar shi da mari, sai da yaji saukar hannuna a keyar ta sa ya dawo tunaninsa. Yau kam muna fitowa islamiyya na buga mai warning akan idan ya min maganar makahon nan sai na cire masa nasa idanun shi ma ya zama makaho irin sa, shi ne yau ya shafa min lfy ko yayi niyyar magana sai ya tuna kalamin ya fasa.
      Dai dai bakin masallaci na hango makahon Abdul zaune ya buga uban tagumi, kai na na dauke na cigaba da tafiya don tun daga nesa na hango shin yau ba rigar ranar ba ce a jikin sa ta yau na kasa banbance kalar kayan ne hakan ko datti kayan yayi kuma rigar ma a juye ya sa ta, ko duk rashin idon ne oho! Kamar wanda aka ta sa a mafarki da karfi Abdul ya ce "anty ga mal. Makaho can" ya fada ba tare da ya tuna gargadi na na sai na cire masa idanu ba, kawai dai na fahimci cewa Allah ne Ya sanya tausayi da kaunar bawan Allah nan a zuciyar ƙanina Abdullahi...

#hubbifillah
#maizarefamily
#onelove
#vote
#comment
#share

Mu hade a page 3 In Shaa Allah...

🌼🌼Oumm Arfah🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now