🌼🌼🌼🌼🌼
*_RAHMATULLAH_*Rubutu da Tsarawa
🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
Wattpad @oummarfah20Page 22
https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH
_Allahumma Inna Nas'alukal Hudaa, Wat tuqaa Wal Afafa Wal Ginaa, Ameen._
_Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._
********
Tmbyr da ya zo mata a rai kenan akan ta tmby shi amma sai ta fasa kawai sai ta ce "hajiyata na kira, kuma sai wata ta ɗaga ban ma ji mene ta ke cewa ba ƙarshe ta kashe, wata wai ko Haj Ambulash ko me oho ban ma kula ba" jin abin da tace sosai ya yarda a kan bata gane wacce ta ɗaga wayar ba sai ya ce " oh maybe network ne kin san wani lkcn idan ka kira waya sai ya nemo wani ya haɗa ku, sannan Haj Atumbulash ce wayar ta ta shiga kenan" Fa'iza ta kalle shi ganin wai ita zai raina ma hnkl da ya ke tunanin zata gagara gane muryar hajiyar ta, sai ta ce "wannan irin suna?" Sai ya ce "eh abokiyar hulɗar mu ce tare muke business da ita" daga haka ya ja bakin sa ya tsuke, tana zaune ta na kallon sa yana ta shirin bacci har ya gama ya matso kusa da ita yana wani irin killer smile ta yaudara wai nan zai burge ta "beauty yau dai ya kamata a bar ni na rage ruwan da na tara ko kaɗan ne, kin ji mai kyau tawa" karon farko da ta taɓa jin tsanar wata halitta, bata san alaƙar da ke tsakanin su da mahaifiyar ta ba amma tunda har ya mata karya akan ba ita ba ce a wayar ta ji zuciyar ta ta kasa yarda da shi, tare da zargin sa da aikata wani mummunan abu... "Yau dai hkr zaka yi don bani sallah, ina jini" ta faɗa tana murmushin ƙarfin hali kar ya ce zai duba da kansa asirin ta ya tonu, Allah da ikonSa sai bai nemi gani ba amma ya nuna mata ko ba ta nan ba ta ba shi dama zai bi da ita a natse. Kallon sa take cike da baƙin cikin sanin sa, har ma da tsoron sharrin sa, murmushin kawai ta ke tare da ƙara neman tsarin Allah daga sharrin sa. Haka dai ya gama magiyar sa ya hakura, don nuna masa tai gsky ita ma ta son hakan don ta kula ta inda ya ke zuwan mata ya fi gamsarwa amma ya bari ta yi tsarki tukunnan. Ta yi hakan ne don samun damar guje ma sharrin sa don ba yau farau ba ya nuna mata ƙarfi ya wulaƙanta ta, hakan da ta yi kuwa sosai ya gamsu da zancen ta har da cewa idan ta saba shi kenan ba su da wata mtsl sai su yi zaman su lfy lau ba tare da an ji kansu.
Tunda Allah Ya bata Sa'a ta samu ta bar ɗakin ko waiwayo ba tayi ba, ɗakin ta ta shige tare da datso ƙofar da makulli har sakata sbd tsaro. Kwanciya ta yi amma bacci ya gagari idon ta, ta saƙa wannan ta saƙa wancan, ganin babu mafita karon farko duk tsawon rayuwar ta tayi tunanin raya dare, bayan ta tuno yadda Rahma ke yi sau tari cikin dare... Salloli tayi tana roƙon Allah Ya ba ta sa'ar yin abin da ta ƙudira ma ranta yi a gobe cikin nasara (ko me ta ke shirin oho).*********
Bacin kada ace ban da hnkl da na ce auren makaho yayi a rayuwa, don za ki tsula tsiyar ki cikin dare ko duk lkcn da ki ka yi ra'ayi ba tare da tunani idan gari ya waye za ki yi kunyar haɗa idanu da shi ba.
Hakan ce ta faru a gare ni, don yau tun bayan sallahr asuba bai kuma fita ba saɓanin da da baya dawowa daga masallaci ya ke wucewa wurin nema. Yau dai na more kallonsa don raina, don gyara zama na ke don na ji daɗin kallon sa da kyau. Ba zan ɓoye ba, abin da ya faru tsakanin mu jiya ya sanya min kwaɗayin kasancewa da mijina, don ya lasa min zumar da ban shirya lasa, sannan abin ya haɗar min da soyayyar da na karanta cikin littafin da aka tura min...
Can dai ya katse min daɗin kallon na shi da na ke yi da tmby "jiya, yayan na ki bai samu zuwa ba ne?" Ban ma ji ba sai da ya maimaita "eh bai samu zuwa ba, sai wani lkcn". Ɗauke kai na yi daga kansa na lumshe ido ina hasaso abin da ya girmi ƙaramin kwanya ta, har ban sanda na buɗe ido ba don tserar da kaina daga tunanin sai dai ina buɗe idon na ga Abdurrahman durƙushe gab da ni, yadda na yunƙura ne ya bai wa fuskokin mu damar haɗewa da na juna....sai kuma lbr ya canza....hasashe na neman koma wa zahir...

YOU ARE READING
RAHMATULLAH
Storie breviMummuna ce ta gani a tanka, yunwar mai sonta ta ke ido rufe, while ƴar uwar ta kyau ne da ita kamar tsada. Wa zai so mai muni da kyakkyawa? Sai dai kuma akwai abin da ta mallaka wanda ba kowa ya sani ba, wanda kuma shi ɗin shi ne Mace! Find out mor...