16

56 4 2
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
    *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
    Wattpad @oummarfah20

Page 16

    _Yaa Allah kada Ka bar mu da zaɓinmu, mun bar maKa zaɓi, Ka yi mana zaɓi na alkhairi. Ameen_

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

*****
   "Wai ni kam ina ɗanka ya shiga ne? Ban gan shi ba tunda kuka dawo sallah, ko har ya kwanta ne?"
        Ta tmby tana mai zama a gefen mijin nata. Sai da ya sha leman dabino da ta ajiye masa kafin ya bata amsa "nan muke zaune da shi ya fita wai ana neman shi a wurin aikin su". Numfashi Mamie ta ajiye ta ce "gsky Abban yara na gaji da wannan aikin nasu, ina ga lkc ya kai da zai ajiye aikin daman ba so mu ke ba, shi ne ya nace sai ya yi aikin"   cikin nasa damuwar ya ce "ni abin da ya ke bani tsoro ma shi ne kada ya taɓo abin da ya fi ƙarfin sa, kin san ynzn mugayen mutane basu zaune hakan nan, zaki ga wasu da yawan su aikin asiri ne".  Ganin zai fita shiga damuwar ma sai ta ɗauke zancen da faɗin "ko da ma nasan yaron nawa ba dai azkar ba, koyarwar ka ce fa? mene zai baka tsoro? Kwantar da hnkln ka kaji ɗan tsohon mijina" yayi dariya shi ma ya biye ta suka canza hirar, amma tabbas kamar yadda tace  lkcn barin sa aikin nan yayi, don shi ma ya gaji....

********
    Cikin dare sosai na farka don kamar ma alfijir ya keto sbd irin ni'imar da ke shigowa ta tagar ɗakin, kallon ɗakin na ke har Allah Ya sa na gane ɗakin asibiti ne, daga gefe na naji wata murya tana zuba ƙira'a cikin suratul Rahman, a hnkl na juya kaina zuwa ɓangaren da nake jiyo karatun, Makaho ne! Da mamaki sosai na ke kallon sa, wannan ne karo na biyu da na ji wata  kalar murya daga bakin sa saɓanin wanda na saba ji, Allah kenan mai yadda Ya so, a lkcn da Ya ga dama, gashi dai Ya yi sa marar gani amma ya ba shi baiwar murya da karatun Alkur'ani wanda ta fi komai na duniyar nan...kallon sa ya cigaba yi har ya kai ƙarshen surar dai dai sanda aka kira sallahr asuba, tashi yayi ya nufo ni, still idanuna na kansa ban cire ba na kasa...jin murya sa kawai nai yana cewa "kin tashi, ya jikin?" Da sauri na rintse idona, ya akai ya san na tashi? na tmbyi kaina, jin ban tanka ba sai ya ce "na zaci ta farka ashe bata farka ba, naji a jikina ana kallona... gwara na je sallah na dawo kafin ta farka ba na nan" daga haka, ya fice ko bayin bai shiga ba, jin fitar sa ya sa na buɗe idona daman a matse nake da fitsari, a hnkl na sauko don na ji sauƙi sosai ba kamar jiyan ba, ina sauka daga kan gadon wata nurse ta shigo da sauri, da murmushi sosai a kan fuskar ta take min kallon mamaki da tu'ajabi tare da ƙara tsarkake Girma da Ƙudurar Ubangiji ganin wai ni wannan mummunar ce matar wancan mutumin, tun jiya take mamakin kulawar da ya dinga ba ta duk da babu idon amma kamar mai ido, hakan ya dinga bata kulawa ynzn ma, ta zo wucewa ta je zagayen safe, suka haɗu, ta mai sllm har zata wuce shi ya mata mgn wai ta je ta duba patient ɗin sa ko akwai wani abu da ke damun ta... daga hakan kuma ya shige ta ya wuce, har ranta ta ke admiring ɗin kulawar sa ga matar sa, har ta na fatan Allah Ya bata kamar sa... tunanin ta ya katse ne lkcn da na gaishe ta ta amsa min sannan ta kama ni zuwa bayi ta taimaka min na gama ta fito da ni, ina daga cikin matan da jinyar jinin al'ada ke musu kamar jinyar naƙuda, ta dawo da ni dakin ta cire min cannular tunda na dawo hayyaci na ganin ba wata mtsl sosai tace mu jirayi zuwan likita sai a bamu sallama.

******

   "Boss an samu mtsl fa" da sauri ya ɗago kan sa ya kalle shi sama da ƙasa "mtslr me" ya tmby shi. "boss an kama yaran da muka turo su samo yaran nan, tohm an kama su sun shiga hannu"  a gigice ya tashi ya fara safa da marwa  "garin yaya ka bari hakan ya faru? Daman yaran ba ƙwararru ba ne?"
    "Boss wannan karon ne kawai aka samu mtsl, don su ne suke kawo yaran"  bai tanka shi ba ya ciro wayarsa yana kira... magana ɗaya biyu zuwa uku kawai yayi ya kashe wayar tare da ajiyar zuciya yace
    "it has been taken care of, so ka natsu zamu canza salo, ka kuma tabbatar waɗanda za ka sake ɗaurawa a kan aikin sun san abin da suke yi" daga nan ya sallame shi shima ya shirya ya fice.

**********

   Ƙarfe 9 na safe likita ta ba mu sallama bayan ta duba ni har tana tsokana ta, muka fito bakin asibitin, sai a lkcn na san ashe ba karabitin asibiti ba ne, asibiti ne babba mai zaman kan shi. A bakin titi mu ka tsaya neman adaidaita sai dai duk wanda ya tsaya sai makaho ya ce su tafi, ni kuma na gaji da tsayuwar, kaɗan nake jira na faɗi, can na tsinci mgnrsa "kiyi hkr ban son mu shiga wanda akwai namiji ne balle su kalle ki, kin ga ai ni ba ido gare ni ba bare na kalli matan su, don hk ban son a kalle min mata" na kalle shi na kawar da kai a raina nace "mene za su kalla munin ko baƙar fatar?" Ban san a fili na yi zancen ba sai da ya ce "uhmm ki bar namiji kawai" sai zuwa can Allah Ya taimake wani abokinsa ne kamar ya tsaya da motar daidai mu ya sauke gilashin ƙasa ya leƙo "wannan kamar Audu Makaho mai mafici?" Makaho ya ce"eh shi ne kuma kamar Ado direba ko?" Yayi dariya ya buɗe mana baya yace mu shiga. Har ƙofa ya kawo mu ya mana sallama ya wuce bayan makaho ya masa tayin shiga ya sha ruwa amma ya ce sauri ya ke yi sai wani karon... Ni na buɗe mana muka shiga, daman ba mu je da komai asibitin ba, shiga ta ɗakin na ga waya ta yashe a ƙasa, daman mai button ne, na ga batir yayi gefe, kai kamar ma taka wayar aka yi na durƙusa na tattare shi daga ƙasa da niyyar zuwa anjima na haɗe shi na kunna, bayan ya zauna ne na kalle shi, tun bayan gaida shi da na yi asibiti magana bata ƙara haɗa mu ba... Y kauda shirun da faɗin "don Allah nan gaba idan baki lfy ki kira ni kin ji" na ɗauke kai gefe, sai kuma na kalle shi nace "ya akai kasan ban lfy?"..."kiran ki nayi naji y kk, tunda ke daman baki taɓa kira na ba, sai kuma naji kin saki ƙara shi ne na taho"  "Nagode da kulawa" na samu baki na da furta wa, wanda sosai ya ji daɗin hakan "haƙƙi na ne kulawa da lfyr ki" daga nan duk muka yi shiru sai ga sallamar Abdul ya shigo bayan na sama izini, ya ke tmby ta waya ta Mamma ta kira amma bai shiga ba, nan na ɗauko wayar na haɗa, ta kunnu amma fa screen ɗin yayi baƙi alamun ya ci screen, Abdul ne ya kula ya ce "Anty wayar ta lalace ne?" Kafin na ba shi amsa makaho ya ce"eh ni na taka ban kula ba, anjima idan na fita sai a gyaro ta" sai kuma na tuna ina da babbar waya wacce na ajiye tun rasuwar Khalil, a maimakon a gyaro wannan tunda ina da wata sai kawai nace "kada ka damu, akwai wata a gida" nan na yi ma Abdul bayanin inda wayar ta ke akan ya je ya ɗauko min, ya je ya kawo min na kunna da caji amma babu yawa Allah Ya sa akwai wuta sai kawai ma maƙala caji, daman akwai layi a cikin sa wanda lkcn Khalil ne kawai ya sanni da shi sai Mamma, wayar na gama booting na shigowar saƙwanni na san dai MTN ne ko wani notification, ban bi kan su ba sai can da nepa suka ɗauke wutan bayan Abdul ya tafi makaho ma ya fita akan zai siyo mana abinci, nace zan iya amma ya ƙi wai ban da lfy.

     Ina ɗaukar wayar na buɗe ta gabana ya faɗi domin saƙwannin daga Khalil su ke... Jiki na rawa na buɗe na farkon....

  _tawan ina son ki sosai, son ki ya min yawan da na ke jin kamar ba zan same ki ba_.

Na biyun kuma...
  _Allah Shi ne shaida akan yadda na ke son ki, ni fa gani nake ko baki sona, son da nake miki ya ishe mu, ba zan ɓoye ba na ƙagara na ga kin zama mallaki na, wallahi ranar zan nuna miki maita irin wanda miji ke wa matarsa, Allah Ya ba ni ke_...

     Ta ukun ita ce ta ɗaga min hnkl, don sai bayan ya zo gidan mu aka hana ni fita shi ke ya turo saƙo, sauran biyun ina ga ya kasa bacci ne ya turo min su a tsakiyar dare, kuma Allah bai bani ikon buɗewa ba sai yau...ta ukun kuwa tamkar bankwana ce da wasiyya ya bar min ta karɓar kaddara mai kyau ko akasin ta...har da cewa na kula da mijina...

Kai wa ƙarshen saƙon yayi daidai da fashewa ta da kuka kuma daidai shigowar Abdurrahman Makaho....

Yaa Rabbi ka sa mu cika da imani. Ameen

Uhmmm mun kusa fa...

#vote
#comment
#share
#oneluv
#rahmatullah

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now