intro

59 3 0
                                    

Family na Jaffa kenan.alhaji Ibrahim Jaffa mutum ne me kuɗi sosai kuma ya aure mata biyu waton kaka da kaku.kaka mace ce kyakkyawa fara gata da hankali da nitsuwa,ta aure Alhaji Ibrahim Jaffa Allah ya basu yaro na farko shine Aliyu waton daddy,daddy Yana da shekara biyu kaka ta haife Ahmad wato abu,abu yana da shekara biyu Alhaji ya aure kaku,kaku mace ce me son surutu gata da son addini,itama fara ce sosai dan tafi kaka ma da haske.abu yana shekara ɗaya kaku ta haife Nasir waton Abba,Abba yana da shekara ɗaya kaka ta haife mohd waton abi,daga abi kaka bata kara haihuwa ba.kaku abi yana shekara biyu ta haife sani waton baba.alhamdullilah dukkan su suna da haɗin kai.gashi suna zaman lafiya kamar ba kishiyoyi ba.baba yana shekara uku kaku ta haife Fatima waton mami.sosai sukayi farin ciki dan itace kaɗai mace a gidan.haka suka haɗa kai suka girmar da yaransu.duk suka tafi abroad karatu amma banda mami dan Alhaji yace ita mace ce ba inda zata je.awurin suka kammala University nasu sukayi masters dukka sannan kowa ya kama aikin yi.

Alhamdullilah Allah ya albarkace family nasu sosai dan se bunkasa sukeyi ba wanda bai san family na Jaffa ba a duk faɗin duniya.

A rana ɗaya mazan dukka sukayi aure, daddy ya aure Amina wato mommy, mommy kyakkyawa ce sosai Fulani ce ga haske ga gashi ga nitsuwa sosai take da kunya.abu ya aure Fatima waton ummi,ummi kyakkyawa baka ce gata da hankali.abi ya aure falmata wato ammi,ammi mace ce kyakkyawa baka ce amma ba sosai ba kuma tana son surutu.abba ya aure Khadija wato umma,umma kyakkyawa ce fara gata bata magana sosai.baba ya aure zainab wato mama,mama baka ce kyakkyawa gata da hankali.alhamdullilah dukkan su a babban gida suke kowa da side nashi.suna da ciki a lokacin Alhaji ya aurar da mami wa wani yaron ɗan uwan shi,aka sha biki sannan aka kai mami gidan ta,duk a anguwa ɗaya suke.

Mommy da ummi suka haihu rana ɗaya, mommy ta haife kalil ummi ta haife muffik, Masha Allah kalil yana kama da mommy sosai haka muffik ma yake kama da ummi.bayan sun haihu da wata uku mama da ammi suka haihu rana ɗaya,mama ta haife haidar ammi ta haife farid da farida.masha Allah kowa se farin ciki.da wata biyu umma ta haife ayban.haka dai Masha Allah yara suka tashi suna son junan su.bayan shekara ɗaya mami ta haife Jamila da Jamil se farin ciki ake yi.

Bayan shekara biyar su mommy suka kara samun ciki gaba ɗaya sosai sukayi murna.mommy ce ta fara haifar khairat da wata uku umma ta haife Anam,da wata biyubmama da ammi suka haihu,ammi ta haife Fatma mama ta haife Habib,da wata biyu ummi ta haife masir.aka sha suna.

Bayan shekara ɗaya mami ta haife junayya itama aka sha suna.yara suka shaku sosai duk da dai kalil baya shiga harkar kowa dan shi tun yana karami yake da wani hali gashi tun yana karami baya ɗaukan nonsense shesa duk yaran suke tsoron shi haka ma muffik shima ya biyo halin kalil ɗin.

Bayan wata biyar mommy ta haife kamal,kamal da baban shi yake kama sak.bayan wata biyar umma ta haife alisha er autan ta.da wata ɗaya mama ta haife twins hamra da hadaya.da wata ɗaya ammi da ummi suka haihu a rana ɗaya,ummi ta haife mira ammi kuma ta haife twins fiddat da Faisal en autan ta.

Yara Masha Allah,bayan shekara biyu mami ta haife jalil dan autan ta.mommy ma da wata biyu ta haife dan autan ta Kabir,da sati biyu ummi ta haife munal,da wata uku mama ta haife halisa er autan ta.

Bayan shekara uku ummi ta haife ɗan autan ta Majid.

Dukkan su gida ɗaya suke waton babban gida.suna zaman lafiya.yara mazan duk wanda ya gama primary abroad ake kaishi ya gama karatun shi.matan kuma a Nigeria za suyi karatun su.

Kalil dai shine babban yaron gidan,baya ɗaukan raini gashi kowa tsoron shi yake duk da baya magana sosai amma inya kalle ka to fa gwanda ka nitsu dan bayi da mutunci wurin mugunta.se ya zama kowa tsoron shi yake a gidan.

Haka muffik ma duk da dai gwanda shi.kowa da part nashi a gidan amma duk a  parlour na Alhaji ake cin abinci da hira,kuma yazama dole kowa yazo wurin a ci abinci bayan wannan ma akwai rules dayawa a gidan amma dai mu shiga labarin farko.

Kalil, muffik,farid,farida,haidar,ayban sa'o'i ne.

Jamila,Jamil, khairat,Anam,Fatma,masir sa'o i ne.

Junayya da kamal sa'o i ne.

Alisha,hamra,hadaya,mira, fiddat,Faisal sa'o i ne.

Jalil,Kabir,munal,halisa sa'o i ne.

Majid ne karamin gidan.

❤️Let's dive into the story

Babban gidaWhere stories live. Discover now