40(final)

22 2 0
                                    

BABBAN gida

40

"Yaya".Anam ta faɗa tana tashi zaune akan gado.

"Umm".ya ɗan buɗe idonshi na bacci.

"Yaya".ta faɗa da rashin hakuri.

"Me ne?".ya tambaya yana zama shima.

"Yaya ka zauna muyi hira bana jin bacci".Anam ta faɗa tana kallon shi.

"Karfe biyu na dare ne fa".ya faɗa yana kallon agogon dake bango.

"To me ne dan nace ka taya Ni hira karfe biyu".ta kalle shi da fuskan tausayi.

"Baki da lafiya ne?".ya tambaya yana sa hannu a goshinta.

"Lafiya na kalau kawai hira nake so kayi min".ta faɗa tana tura hannun shi.

"Ai ban iya hira ba".ya faɗa da gajiya a Muryar shi.

"Yau ka koya".ta tura baki.

"Kin san ban iya hira ba se aiki".ya faɗa yana janta jikin shi sannan ya fara kissing wuyan ta.

"Yaya baby fa yana kallon ka".ta tura shi.

"A ina?".ya tambaya yana juye juye.

"A nan".ta nuna cikinta daya ɗan fito.

"Baki ga cikin ya rufe shi bane".ya kara jawo ta yana kissing nata.

"Yaya baby yace ka Dena".Anam ta kara tura shi.

"Zo to na Dena".ya faɗa yana kallon ta.

Zuwa tayi kusa dashi ai kuwa ya koma abun da yake yi.

"Yaya".dakyar ta tura shi ta tashi da gudu ta fita tana dariya.

Murmushi yayi ya tashi ya bita.

                            ****
"Junayya Ni yaushe ne?".hamra ta tambaya da ƙaton cikin ta kamar yau zata haihu.

Zaune suke a side na fiddat yau sunan yaron ta Abbas wanda ya samu sunan Alhaji Ismail shima.

"Next week". junayya ta faɗa tana cin biscuit dake hannun ta itama da ƙaton ciki.

"Ke nima haka".hamra ta faɗa da farin ciki.

"Maybe ma rana ɗaya zaku haihu hadda fatma ma".Isha ta faɗa tana wasa da sadiq.

"Anya adda baki da ciki kuwa?". sumayya ta tambaye Farida dake zaune tana danna wayar ta.

"Wa ya sani".tayi dariya.

"Ya tabbata kenan".Anam dake shigo wa da apple a hannun ta na dama da kuma zoɓo a na hagu ne ta faɗa.

"Acici".mira ta faɗa tana kallon Anam dake zama kusa da Alisha.

"Ba laifin ta bane abun cikin ta ne yake sata".Amina ta faɗa tana wasa da munir.

"Oho dai ba wanda ze hana Ni jin daɗi na".Anam ta faɗa tana cin apple nata.

"Anam zo kiga ikon Allah".munal ta shigo, haryanzu lallen auren ta yana nan dan yanzu auren ta yayi sati biyu".

"Me ne?".Anam ta tambaya tana ɓata fuska dan batason tashi.

"Yaya kalil ne".munal ta faɗa da zumuɗi.

Anam tashi tayi ai sauran ma suka tashi hadda me jego,kowa yana so yaga abunda kalil yayi.

Suna fita suka hango shi yana wasa da adnan yana dariya wanda ko Anam dake matar shi bai taba mata ba.

Duk da mamaki suka tsaya suna kallon shi.

Babban gidaWhere stories live. Discover now