22

10 2 0
                                    

BABBAN GIDA

22

"Wannan kike nema?".cak ta tsaya a inda take zuciyan ta se buga wa yake, ahankali ta juya tace"yaya abuna ne ya faɗi ɗazu shine nazo nema".
Kalil yace"toh se ki fita tunda baki samu ba".
Anam taɓe baki tayi tace"yaya ayyah ka bani waya na wallahi bazan kara waya da wani ba".
Kalil yace"ki fita nace".
Takawa tayi har wurin gadon shi dan batasan inda yake ba,se tace"yaya kayi hakuri ka bani waya na".
Shiru taji kuma bata jin motsin shi,
Sauke nunfashi tayi ta zauna.
Ashe akan cinyar kalil ta zauna,tura ta yayi ya tashi se ya kunna wuta yana mata wani kallo.
Da tsawa yace"ke bance ki fita daga ɗaki na ba!!!".
Tashi tayi ta Mishi fuskar tausayi tana cewa"Allah sarki yaya kalil bazan kara ba wallahi na tuba".
Jan hannun ta yayi ya fitar da ita sannan ya rufe kofa.

Anam tsaki taja a fili tace"nayi maka na mutunci amma yanzu ya kare".
Wuce wa ɗakin ta tayi ta kwanta har bacci ya ɗauke ta.

Babban gida.

"Nikam wallahi na gaji ummi bazan iya ba".
Mira ta faɗa tana kuka a cinyar ummi.
Ummi ahankali take rarrashinta amma mira se kuka take.
Munal ce ta shigo tana cewa"su yaya masir sun tafi airport".
Ummi tace"toh Allah ya kiyaye musu hanya".
Sukace Ameen se munal ta zauna tace"yaya Nasir fa ya fita".
Mira tace"tafiya zeyi".
Munal da fara'a tace"Masha Allah Kinga ze tafi se ki kwantar da hankalin ki".
Mira murmushi tayi ta goge hawayen ta se tace"munal bazaki gane bane".
Munal tace"ko bangane ba amma ai ze tafi".
Mira gwaɗa kai tayi.

Farida da Mustapha.

"Sweetheart nikam yaushe zamu je in sha ice cream?".Farida ta faɗa tana zaune da karamin cikinta da ya ɗan fito.
Mustapha dake kusa da ita yace"ko yaushe kike so ai dole na kaiki".
Murmushi tayi tace"toh sweetheart muje gobe dan baby yace shi ice cream ze sha".
Murmushi yayi ya jata jikin shi sannan yace"muje yau mana tunda baby yana so".
Murmushi tayi ta gwaɗa kai se ta tashi.

Walid da Raisa.

"Baby wai mesa kake min haka ne,kasan dai cikin jiki na naka ne".
Raisa ta faɗa tana jefa jikin ta kanshi.ture ta yayi ya tashi sannan yace"Raisa kije ki nema wanda yayi Miki ciki ba niba".
Rike hannun shi tayi kamar tayi kuka tace"haba baby kai fa kasan kaine kaɗai wanda yayi min ciki,mesa kake min haka?".
Jan hannun shi yayi ze tafi ta rike rigar shi tana cewa"wallahi yaya Walid baka isa ba,kamin ciki kuma yanzu kace ba kai bane".
Wani kallo yayi mata sannan yaja rikar shi ya wuce upstairs,ita kuwa zama tayi ta fara kuka.

Canada.

Zaune suke suna cin abinci a dining.
Su alhaji suna ta hira Anam kuwa se cin abinci take tana tunanin yadda zata ɗauke wayar ta.
Alhaji yace"Yakamata mu koma gobe dan wasu aiki".
Anam ɓata fuska tayi tace"haba alhaji mu bari se nan da kwana biyu".
Abba ya kalle ta yace"makarantar ki fa wa ze Miki?".
Tura baki tayi amma batayi magana ba.
Haka suka gama cin abinci duk suka watse su Kalil kuma suka je makaranta.

Anam tana kwance a ɗakin ta tana tunani,chan se ta tashi tayi murmushi a fili tace"gobe zanje na ɗauke waya ta".
Fita tayi ta same umma tana zaune a parlour,zama tayi kusa da ita sannan tace"umma na yanzu haka zamu tafi bamu fita yawo ba?".
Umma murmushi tayi tace"yawo kika zo ko kula da ayban?".
Tura baki tayi tace"umma toh ai ya warke".
Umma tace"ba inda zanje se de kije ke kaɗai".
Tashi tayi tace"shikenan zan tafi Ni kaɗai".
Umma tace"karkije mu rasa ki fa zo ki zauna".
Anam karkaɗa kai tayi ta wuce ɗakin ta.tana shiga ta zauna a fili tace"hmm gaskiyan umma kar inje na ɓata,bari kawai na hakura".
Haka dai ta hakura ta Zauna tana kallon tv.

Se bayan magriba su haidar suka dawo.
Zama sukayi a parlour se Anam ta fito tayi musu sanda zuwa sannan ta zauna.
Kallon haidar tayi tace"yaya haidar ina so in fita yawo".
Haidar murmushi yayi yace"toh ki shirya se mu fita".
Da farin ciki ta tashi ta shiga ɗakin ta tasa gele akan ta sannan ta fito tace"na shirya".
Tashi yayi yace"mu je toh".

Babban gidaWhere stories live. Discover now