28

12 1 0
                                    

BABBAN GIDA

28


"Mira ta su ma!!!".

"Innalilahi how?".Anam ta tambaya tana tashi.

"Bansani ba amma yanzu muna hanyan asibiti".

"Ya rabb badai yaya Nasir bane ko?".Anam ta tambaya tana riƙe kanta.

"A'a ba shi bane,kawai su ma tayi".

"Ok toh yanzu zan zo".Anam katse wayar tayi zata tafi Aunty fatee ta riƙe hannun ta tana cewa
"Me ne ya faru?".

"Mira ce ta suma yanzu suna hanyan asibiti".

"Subanallahi Allah ya rufa asiri".aunty fatee ta faɗa.

"Kinsan mun saba da jin mira ta su ma a babban gida".hamra ta faɗa tana miƙa wa Fatma gelen ta.

"Wannan daban ne fa".Anam ta faɗa tana kokarin fita.

"Ina zaki je ke kuma?".aunty fatee ta tashi tana riƙe hannun Anam.

"Zan je asibiti ne".

"Yau fa auren ki Anam". aunty fatee ta faɗa tana jan ta wurin me kwalliya.

"Mira ce fa take asibiti".Anam ta faɗa tana zama a wurin me kwalliyan.

"Karki damu Raisa zata kula da ita".aunty fatee ta faɗa.

"Kiyi simple".Anam ta faɗa wa me kwalliyan.

Se bayan minti arba'in kafin aka gama mata kwalliyan,kallo kanta tayi tana ganin yanda ta canja.

Aunty zainab ta taya ta sa kaya sannan ta gyara mata kayan se tasa mata gele maroon da stones maroon ta ɓakin gelen.

"Masha Allah".tana fito wa duk suka ya ba.

Fatma wani fitted gown fari tasa wanda ya mata kyau sosai se baby kuma tasa red gown me kyau,Masha Allah duk sunyi kyau.

"Karfe nawa za'a ɗaura auren?".hamra ta tambaye munal.

"Saura minti ɗaya".munal ta faɗa tana duba lokaci a wayan ta.

Anam zuciyan ta wani buga wa yayi bata san lokacin data tashi ta fita da gudu ba,Binta a baya sukayi amma se gudu take.

Hatta kusa zuwa parlourn da ake ɗaura auren wani ya ja ta tabaya.tana juya wa sukayi ido huɗu da ayban.rungumar shi tayi ta fashe da kuka me sauti.

Rarrashinta ya fara yana buga bayan ta ahankali.

Se yanzu suka iso wurin duk suna sauke nunfashi kamar wanda sukayi aikin gona.

"Anam kiyi hakuri ki koma ciki nan akwai mutane".ayban ya faɗa yana share hawayen ta.

"Yaya banason na aure yaya kalil".ta faɗa tana kara sabon kuka.

"An ɗaura auren baby Abubakar da Farid mohd se kuma Fatma mohd da muffik Ahmad se kuma Anam Nasir da kalil Aliyu da sadakin kowanne a ciki dubu ɗari bakwai".suka ji an faɗa daga cikin parlourn.

Anam wani ihu tayi ta zuɓe a ƙasa tana ta kuka.anyi anyi tayi shiru amma se ƙara ihu take.

Haka har jama'an parlourn suka fara jin ihun ta,duk suka fito dan su ji daga ina ne ihun.

"Anam tashi su Alhaji sun fito".hamra ta faɗa tana kokarin jan hannun Anam amma taja hannun ta tana kara ihu.

Alhaji ne yaje wurin ta yace"Anam tashi kiyi hakuri".Anam kaman bata ji shi ba ta cigaba da ihun ta.

Kalil haushi ne ya cika shi da tsawa yace"ke bada ke ake ba?!!!".duk a wurin sanda kowa yaji tsoro dan yanda yayi ihun.

Ba shiri Anam ta tashi sannan su hamra suka taya ta koma wa side nasu.

Babban gidaWhere stories live. Discover now