25

13 2 0
                                    

BABBAN GIDA

25


"Zan haɗa auren Farid da baby se muffik da Fatma se kuma Anam da kalil".
Zaro ido kowa yayi ana mamaki da tausaya wa Anam ɗin.
Anam kam tunani ta shiga yi ko akwai wata Anam ɗin a wurin bayan ita.
Muryar Kalil ne ya dawo da ita hayyacin ta yana cewa"alhaji bazan aure Anam ba".
Anam tashi tayi tace"alhaji bazan aure yaya kalil ba wallahi".
Fatma kam kuka ta fara dan ita gaskiya batason ta aure muffik.

Alhaji kallon Anam yayi sannan ya kalle kalil da yanzu shima a tsaye yake
Yace"na riga dana faɗa kuma ya zauna ba me canja wa".yana faɗan haka ya fita daga parlour.
Anam zama tayi ta fashe da kuka.

Kalil bin bayan alhaji yayi,sanda suka ɗan yi nisa tukunnan Kalil yace"alhaji nifa bazan aure yarinyar nan ba".
Alhaji tsaya wa yayi yace"bazaka bi umarni na ba kenan?".
Kalil shafa kanshi yayi da haushi yace"alhaji bazan taɓa saɓa umarnin kaba amma bazan aure yarinyar nan ba,Ni bana ma son kallon ta".

Alhaji dafa kafaɗan kalil yayi yace"na zaɓa maka ita ne dan nasan ita ce ta dace dakai kuma maganan bazaka aure ta Bama karka soma,daga yanzu ma kasa a ran ka matar ka ne".
Barin wurin alhaji yayi Kalil wani baƙin ciki da haushi ne yake damun shi dan ba karamin tsanan Anam yayi ba.ahankali ya taka har side nasu.

A parlour kuwa anyi anyi Anam da Fatma suyi shiru amma inaaa sunƙi,Anam kam kamar wanda aka mata albishirin mutuwa take kuka.
Mazan duk fita sukayi muffik ma dai ranshi a ɓace haka ya fita,Farid kam bai nuna wani damuwa ba duk da bai nuna farin ciki ba.

Se chan tukunnan Anam ta share hawayen ta ta wuce waje tana neman alhaji.ta duba ko ina bata same shi ba sanda taje garden ta samu yana zauna daɗan damuwa a fuskar shi yana kallon wani flower a kusa dashi.
Anam zuwa wurin shi tayi a fusace tace
"Alhaji mesa zaka min haka ne,farko ka haɗa auren mira da yaya Nasir amma nayi shiru,na biyu ka haɗa auren khairat da yaya shureim nayi hakuri amma yanzu wallahi bazan iya ba,Ni bazan aure yaya kalil ba ko zaka kashe Ni!".ta gama maganan da rauni a fuskar ta.

Alhaji sauke nunfashi yayi amma bayyi magana ba.zama tayi kusa dashi ahankali tace"Alhaji mu ma fa ya kamata ka tambaye zaɓin mu kafin ka haɗa mu".
Alhaji juya wa yayi ya kalle ta sannan yace"Anam nasan abubuwa dayawa da nake yi bana muku adalci amma hakuri zaku yi, lokacin da baban mu yake raye abun yafi haka shesa yanzu na rage wasu abubuwa dayawa dan kar na Cutar da ku".

Anam kamar tayi kuka tace"yanzun ma ai kana cutar damu alhaji,na sani bin al'ada kake yi amma mu fa?,muma ai mutane ne kamar kowa".
Alhaji zeyi magana kaku dake zuwa tace"Anam ki Dena faɗin irin maganganun nan wa Alhaji,alkawari ya ɗauka kuma dole ne yayi".

Anam kallon tambaya tayi wa kaku, ahankali kaku ta zauna a kusa da Anam tace"Anam kiyi wa Alhaji biyayya ki aure wanda ya zaɓa Miki dan Allah ki Dena yiwa alhaji tambayoyi,yanzu ma abubuwa sun Mishi yawa".

Anam kallon Alhaji tayi tace"alhaji kasan dai Ni da yaya kalil bamu shiri balle ace mu zauna a gida ɗaya,dan Allah ka canja min wani".

Alhaji ahankali yace"Anam kalil zaki aura,se de kiyi hakuri".
Anam tashi tayi tabar wurin da ɓacin rai.

"Nifa bazan aure yaya muffik ba". Fatma ta faɗa tana kwance a cinyar Farida suna zaune a parlourn su.
Anam a fusace a shigo parlourn tana cewa"ke Fatma tashi mu bar gidan nan".

Fatma a zabure ta tashi tana cewa"amma Anam baki da hankali".
Anam hanyar ɗakin su ta fara tafiya tana cewa"in bazaki jeba shikenan se ki zauna".

Farida tace"kai Anam hakuri fa zakiyi ai ba se kin gudu ba".
Anam a kofar ɗakin su tace"ba gudu zanyi ba tafiya zan yi".
Shiga ɗakin tayi ta fara haɗa kaya.

Kalil kuma a ɗakin shi se rushe rushe yake ya kasa nitsuwa, hannun shi duk jini dan glasses da ya fasa,su ayban suna ta hana shi amma yaƙi Dena wa.
Mommy da sauri ta shigo tana kokarin riƙe kalil amma se ya tura ta,haidar ne ya riƙe mommy dan karta faɗi.
Mommy a tsorace tace"kalil ka Dena dan Allah".

Babban gidaWhere stories live. Discover now