15

14 1 0
                                    

BABAN GIDA

15

"Me kuke yi?".Anam ta tambaya tana kallon su Walid da Raisa suna iskanci.da suka ganta suka yi tsurutsuru kamar magunan da aka wanke da ruwa.
Anam da mamaki tace"dan Allah mesa kuke yin haka,ku bari mana ayi auren tukunnan,ai wannan haramun ne".
Walid kam fita yayi daga ɗakin raisa ma zuwa tayi zata fita Anam ta riƙe hannun ta da tsawa tace
"Ke Raisa wani irin rashin hankali ne yake damun ki,ehhh!!!!".
Raisa ba kunya tace"iyawa ne inkin iya kema kiyi mana".
Anam mari ta sauke mata da zafin nama tace"Allah ya sawaƙe in fara abinda kike yi,kinbar ko wani ɗan iska yana taɓa ki,ai yanzu kin zama gwanjo Ni kuwa dal nake".
Raisa ma marin Anam tayi ai kuwa suka fara kokuwa da juna.

Majid dake wuce wa yaji su da sauri yaje ya kira harun dan shine kadai na miji a gidan.ai kuwa ba'ayi minti biyar ba se ga harun yazo.
Dakyar ya samu ya raba su.
Harun da tsawa yace"me ne yake damun ku wai?,baku da hankali ne?!!".
Anam dake sauke nunfashi sama sama tace"yaya dan na faɗa mata gaskiya ne ta kama Ni da fa ɗa".Raisa tace"karya ne zagi na tayi".
Harun yace"ku wuce ku bar nan,kuma inna kara jin kunyi faɗa se na karya ku".
Anam fita tayi ta wuce side nasu ta kwanta.khairat dake kallon tv ta juya ta kalle ta tace"lafiya kin shigo kamar an Miki duka?".Anam tsaki taja ta juya.
Haka dai har dare yayi ba wanda ya gane kan Anam har sukayi bacci.

Harun da Jamila.
"Ke Jamila bance ki gyara min ɗaki kafin na dawo ba?!!!".harun ya faɗa da tsawa yana tsaye a kofar ɗakin shi.da sauri Jamila ta fito da kayan bacci a jikin ta tace"wallahi yaya na gyara ɗakin".
"Kizo nan dan ubanki".
Harun ya faɗa da tsawa.
Ahankali ta tako wurin ya riƙe gashin ta dake a buɗe,wani ihu ta sake se yace
"Dan ubanki a haka ne kin gyara ɗakin?!!!".hawaye ya taru a idonta ta fara cewa"yaya Allah na gyara".
Sake ta yayi ya mare ta  ta faɗi a ƙasa.
Da tsawa yace"ki shiga ki gyara ɗakin nan kafin nan da minti biyu in kuma ba haka ba jikin ki ze gaya Miki!!".
Da sauri ta tashi ta shiga ɗakin ta fara gyara wa duk da ta riga da ta gyara,shi kuwa yana tsaye yana duba lokaci a agogon hannun shi.
Minti biyu yana cika ya shigo ɗakin ya damƙe hannun ta da zafin nama yace
"Karuwa irin ki kinɗau zan barki ki huta ne,kin je kin bar wani ɗan iska yayi Miki ciki wawiya kawai".
Yana faɗan haka ya ture ta sannan ya wuce toilet.
Ita kuwa kuka ta zauna take yi dan tasan itama tayi laifi.da taji ya kusan fita ta goge hawayen ta tahau kan gado ta kwanta kamar tayi bacci.daya fita yaje yasa kaya se shima yaje ya kwanta.

Canada.
"Bro inaso in faɗa maka abu but bansan ma taya zan fara ba".haidar ya faɗa wa kalil dake zaune yana danna laptop nashi.
Kalil ɗaga ido yayi ya kalle haidar sannan yace"go ahead".
Haidar sauke nunfashi yayi sannan yace"bro gaskiya ina son Anam".
Kalil murmushin mugunta yayi sannan yace"ka kama aiki kuwa but good luck".
Haidar murmushi yayi yace"bro Anam ta haɗu kawai dai kaine ba zaka gane ba".
Kalil yace"ka riƙe zancen ka banson jin sunan ta ma balle har na gane".
Haidar murmushi yayi ya tashi ya fita daga ɗakin kalil".

Babban gida.
Tun safe suka wuce makaranta.anam da Raisa har suka gama lectures ba wanda ya kula wani.
Suna fita Anam ta kalle wani mota yayi parking a gaban class da suka fito.tana ganin motan ta gane na wanchan gayen ne.
Sauke glass na motan yayi ya mata murmushi se yace"one minute please".
Tsaya wa tayi tana kallon shi se chan kawai ta wuce ta shiga motan se ya kalle ta yace"You look beautiful".
Anam ba emotion na komai a fuskar ta tace"me kake nema a wuri na?".
Murmushi yayi yace"so nawa zan faɗa Miki Ni ke nake so".
Harararshi tayi tace"so nawa zan faɗa maka bazaka taɓa sami na ba".
Murmushi yayi yace"se de banga dama ba".
Wani irin dariya tayi tace"kasan family na kuwa?".
Murmushi yayi ya gyara zama sannan yace"Jaffa".
Murmushi tayi tace"se kaje kayi bincike su waye ne Jaffa kuma me zasu iya aikatawa".
Murmushi yayi yace"i already know".
Murmushi tayi tace"se ka fita a harka na tunda ka sani".
Murmushi yayi yace"do you think your family can stop me from marrying you".
Dariya tayi me sauti sannan tace"haryanzu baka sansu bane shesa".tana faɗan haka ta fara kokarin buɗe Kofar motar se taji a rufe.juya wa tayi ta kalle shi tace"ka buɗe min kofa na fita".
Taɓe baki yayi yace"amma ai bamu gama magana ba".
Anam da karfi tace"malam nace ka buɗe min kofa na fita!!!".
Murmushi yayi yace"by the way sunana agrif ba malam ba".
Se ya buɗe mata kofa ta fita tana jan tsaki ta wuce wurin Raisa da tunda Anam ta shiga motar take kallon motar hankalin ta a tashe.tana kallon ta ta fito tace"lafiyan ki ko?".
Anam da mamaki tace"ehh lafiya na kalau amma mesa kika tambaya?".
Raisa tace"naga kin shiga wani mota ne shesa kada sun Miki wani abu".
Anam murmushi tayi tace"ba abinda ya faru Raisa".a haka suka shirya. Su Fatma suka gama se suka wuce babban gida.

Babban gidaWhere stories live. Discover now