BABBAN GIDA
23
Anam kwance take a gadon asibiti haryanzu bata farka ba,kanta akwai bandage se ƙafan ta shima da bandage, jikin ta duk ciwo.
Duk hankalin su a tashe suna zaune.Chan se doctor lawan ya shigo ya duba ta sannan ya dube umma dake riƙe da hannun Anam yace
"Karku damu ba abun tayar da hankali bane,kawai dai ta buga kanta sosai ne se kuma ciwon da taji a jikin ta,dole muyi admitting nata dan ta warware sosai kuma inshallah nan da sati biyu duk zata warware".Alhaji da damuwa a fuskar shi yace"toh doctor lawan mun gode".
Doctor lawan fita yayi ya bar su a ɗakin.
Mira hawaye se zuba yake a idonta tana tuno yanda Anam ta faɗi daga saman steps har ƙasa.Se bayan sallar Isha Anam ta farka lokacin ba kowa se umma da Khairat a ɗakin sauran sun koma babban gida.
Ahankali take buɗe idonta har ta buɗe,ko kanta ta kasa juya wa dan azabebben ciwon da yake mata,hawaye ne ya fara zuba a idonta duk da Anam tana da dauriya sosai amma yau ta kasa.
Umma ahankali ta shafa hannun ta tace"anya wannan Anam nawa ne?,Anam nawa tana da dauriya sosai".
Anam murmushi kaɗan tayi amma bata ce komai ba.
khairat kusa da ita tazo tace"Anam sannu".
Anam ko motsi ta kasa yi da jikin ta kamar wanda aka manna a wurin take jin ta, ahankali ta rufe idonta.Umma tace"khairat anya bazaki kira doctor lawan ba?".
Khairat fita tayi ta kira shi.
Chan se suka shigo ya duba Anam se ya sauke nunfashi ya kalle umma yana cewa"karku damu ba wani matsala bane kawai dai jikin ta bai warware bane shesa kuma ze ɗan ɗau lokaci".
Umma gwaɗa kai tayi tana kallon Anam dake bacci.Haka dai akayi auren su Amina duk da kowa hankalin shi a tashe amma anyi biki kuma an kai su side nasu.amina side nata komai sky blue ne me kyau yana kallon side na ilham,side na ilham kuma light brown ne da fari se side na kauthar ash ne.amare Masha Allah sunyi kyau.
***
Haka dai kamar wasa yau Anam satin ta biyu a asibiti kuma haryanzu bata warware sosai ba duk da tana magana kaɗan kaɗan kuma tana cin abinci amma ba ta iya tashi dan ƙafan ta yayi targaɗe.Babban gida.
Dangin Jaffa ne duk tare a parlour na Alhaji dan ya kira kowa akan akwai sanar wa.
"Assalamu alaikum bada ɓata lokaci ba zan sanar da Abinda zan faɗa, wancan meeting da mukayi ban sanar da wani auren ba amma yanzu shine abinda yasa na tara ku". sauke nunfashi yayi sannan ya cigaba da cewa"na zauna nayi nazari akan haɗin auren da zan faɗa yau kuma duk nayi farin ciki sosai duk da wasu suna masters nasu amma baze zama matsala ba dan zasu iya zuwa su duba matan su kafin su gama gaba ɗaya.na farko dai zan haɗa auren Jamil da sumayya se Malik da sadiya se kuma khairat da shureim".
Ba karamin mamaki akayi ba musamman ma na khairat da shureim dan kowa yasan Anam tana son shureim.Khairat duk da tana farin ciki amma tana baƙin ciki wa Anam dan tasan Anam tana son shureim.
Malam da fara'a yace"gaskiya munji daɗin wannan haɗin sosai kuma Allah ya tabbatar da alheri".
Da sanyin jiki wasu suka ce Ameen.Aunty zainab tace"su yaushe za'a sanar dasu dan naga suna makaranta?".
Alhaji Ismail yace"wannan ai ba matsala bane za'a kira su a waya, Alhaji baka faɗa yaushe ne auren ba".
Alhaji murmushi yayi yace"bayan sallah da sati ɗaya".
Maman Nasir tace"saura wata ɗaya da sati biyu kenan".
Gwaɗa kai sukayi sannan tace"Allah ya nuna mana".
Akace Ameen sannan kowa ya watse.Suna fita kowa ya fara kananan maganganu akan auren nan,wasu na cewa ba'ayi wa Anam adalci ba wasu na cewa haka daidai ne wasu na cewa mesa ba'ayi wa manyan ba akayi wa yaran.haka dai kowa yake tofa albarkacin bakinshi.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.