BABBAN GIDA
38
"Alhaji Allah ya mishi rasuwa se de Allah yaji kanshi". doctor lawan ya faɗa kanshi a ƙasa.
"Innalilahi wa innailaihi raji un wayyo Alhaji".kaku ta faɗa tana fashe wa da kuka me sauti.
Anam zubewa tayi a ƙasa ta suma.
Kafin kace me gabaɗaya asibiti ya rikice kowa se tausayin su yake.
Mazan kuma wasu sunyi dauriya amma wasu sun kasa dauriyan.Su daddy ma sanda suka zubar da hawaye,Anam kuma an kaita ɗaki doctor lawan yana duba ta.
Haka rasuwar Alhaji ya zagaya duniya gabaɗaya da shike ba wanda bai sanshi ba.
Su Fatma ma se kuka kowa ya zama abun tausayi,dakyar aka maida su babban gida,chan bayan la'asar aka kawo gawan alhaji sannan aka mishi sallah suka je binne shi.
Se rannan sadakan bakwai aka sallame anam.itakam ko magana bata yi se kuka,ba yanda ba'ayi da ita ba amma bata da aiki se kuka, abinci ma se kalil ya zare mata ido tukunnan take cin kaɗan se tace ta ƙoshi.
****
Kwance Anam take tana ta kuka tana kallon hoton alhaji da take riƙe dashi a hannun ta, kullum maganan daya mata na karshe take tunawa da lokacin data kalle shi na karshe kafin ta fita daga ɗakin asibitin."Anam".kalil ya shigo shima kana kallon shi kasan akwai baƙin ciki a fuskar shi kawai dauriya yake yi.
"Yaya Alhaji na ya tafi ya barni".ta faɗa tana kuka.
Zuwa yayi kusa da ita ya jata jikin shi.
"Addu'a zaki mishi ba kuka ba".ya faɗa yana karɓan hoton dake hannun ta se ya ajiye a gefe.
"Yaya shikenan Alhaji na ya tafi".ta kara fashe wa da kuka sabo.
Rungumar ta yayi shima yana danna zuciyan shi dan shima ba karamin jin mutuwar Alhaji yake a zuciyan shi ba.
"Yaya shikenan ba wanda yake so na kamar Alhaji".ta faɗa tana kara shiga jikin shi dan ƙanshin turaren shi yana kwantar mata da hankali.
Shiru yayi dan bai san me ze ce mata ba.
"Yaya kai ma ai baka so na".ta faɗa tana sheshsheka.
Shiru yayi still Yana kallon ta.
"Ka gani ba".ta faɗa tana lumshe idonta.
"Wa ya faɗa Miki".ya faɗa ahankali.
Shiru yaji tayi se ya kalla fuskar ta tana bacci.ahankali take sauke nunfashi.
Murmushi yayi yace"back then I hate you so much Anam but bansan mesa yanzu bana jin yanda nake ji da ba".
Ahankali ya kwantar da ita se ya fita daga ɗakin.
(Bayan wata biyu).
"Nifa bazan aure munal ba". Habib ya faɗa yana kallon malam.
Zaune suke a parlourn Alhaji dukkan su.
"Alhaji yace kai zaka aure ta kuma baka isa ka canja hakan ba". Alhaji Aliyu ya faɗa.
"Yanzu ai Alhaji baya nan balle kuce se kun min dole".Habib ya faɗa da ko in kula.
"Kai Habib baka da hankali ko!!".baba ya faɗa da tsawa.
"Daman Alhaji ne yake bada doka kuma a bi yanzu da baya nan kowa yayi abunda yake so".Habib ya faɗa yana kallon su da rashin tsoro.
"Yaushe ma Alhaji ya rasu har ka fara faɗan irin wannan abun".kaku ta faɗa tana tagumi.
"Habib yanzu kai ba yaro bane kuma kasan da dokan Alhaji muka girma,kawai dan baya Nan baze zama baza'abi dokan shi ba".haidar ya faɗa da haushi.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.