2

18 1 0
                                    

BABBAN GIDA

2

Yau tun safe suka tashi fara shirin school.fatma da Khairat suna part 1 a state University.bayan sun gama suka wuce dining, ba kowa se yara matan.suka zauna akayi serving nasu suka fara ci.
Hamra tace"yaune kawai nake jin daɗin zanje school wallahi". dariya sukayi halisa tace"daman dai bakya son makarantar ne kawai karkiyi blaming zuwan su yaya aciki".mira tace"ke dai ki faɗa mata,ai babban gida ma kawai ya ishe ki". khairat ta tashi tana cewa"kuyi sauri karkuyi letti dan kunsan Ni da Fatma da Anam bamu da matsala".alisha ma tashi tayi tana cewa"gaskiya kam wanda ya gama ya tashi mu tafi mota ɗaya sauran su biyo baya". fiddat da hidaya da munal suka tashi,Anam ma ta tashi se hamra dake zaune tace"kuje mukam se mun gama".Fatma ta tashi tace"se kin gama dai Sarkin letti,ke da halisa da mira kam kuna da aiki".mira ta harare ta tace"oho dai mudai se mun kammala cin abincin mu a hankali".tafiya sukayi suka bar su mira a dining.as usual kowa ya shiga mota suka wuce.

Su Fatma da Anam da Khairat suka wuce class nasu dan course nasu daman daman.bayan Anam ta gama classes nata ta zauna jiran su fatma.se bayan azahar kowa ya kammala classes nashi se suka wuce gida.

Suna isa ɗakin su suka wuce duk sukayi wanka tukunnan suka wuce dining suka gaishe su suma suka zauna aka fara cin abinci.ana tsaki da cin abinci daddy yace"gobe zan tafi Dubai ina da wani aiki". sukace "Allah ya kiyaye hanya". Alhaji ya gyara murya yace"inshallah dai su kalil zasu koma masters nasu nan da wata uku a Canada".Anam a zuciyar ta tace har wata uku mudai mun shiga uku.mama tace"Allah ya kaimu". haka aka gama cin abinci Kowa ya wuce side nasu.

Anam tana shiga ɗakin su ta zauna khairat da Fatma ma suka shigo.wayar Anam ta fara ringing, murmushi tayi zata ɗauka fatma ta warce wayar tana cewa"wai ke mesa kullum kina nema wa kanki Bala i ne, yanzu in wani ya kamaki me zaki ce, kinsan dai ke ƴar babban gida ne".tsaki Anam taja tace "ke kiba Ni waya na kafin ranki ya ɓaci, banson iskanci me ruwan ki in an kamani". khairat tazo kusa da Fatma tace"bata wayanta kafin yanzu ku tara mana zama'a".Fatma tsaki tayi ta wurga mata wayar sannan ta fita daga ɗakin.(daman Anam da Fatma sun saba faɗa sosai.fatma ita tana faɗan gaskiya anam kuma bata son gaskiyar).anam kuwa waya ta fara yi da salim.

A ɗakin su alisha kuwa hamra ce take shirya wa wai zata je picnic da friends nata.alisha dake zaune tace
"Hamra ki rufa wa kanki asiri ki zauna a gidan nan dan wallahi tsautsayin da zesa ki fita wani yazo neman ki ace bakya nan".hamra dake sa gele tace"zan dawo da wuri dan wallahi ba abinda ze hana Ni fita daga gidan nan". fiddat tace"alisha kyale ta akace jiki magayi".hamra harararta tayi tace"oho dai,alisha dan Allah ki duba min in waje clear ne se na fita".alisha tashi tayi ta fita fiddat tace"wahalelliya kawai".alisha taje ta duba sannan ta dawo tace"clear amma kiyi sauri".hamra gwaɗa kai tayi ta fita.fiddat tace
"Wallahi hamra dai nasan tsautsayi ne ke kiran ta".alisha tace"Allah ya rufa asiri". fiddat tace"Ameen".

A ɗakin su khairat kuwa har yanzu Anam waya take yi hankalin ta kwance, knocking sukaji anyi, Anam ta katse wayar ta sannan sukace"come in".Farida ce ta shigo da murmushi a fuskar ta tazo ta zauna kusa da Khairat tana cewa"kun manta da addar ku ko hira baza kuzo ku taya Ni ba". murmushi sukayi khairat tace"mun isa mu manta da adda Farida ne".Anam ta matsa kusa da farida tace"adda haryanzu mamakin yadda kika samu aka barki kikayi karatu a abroad nake". murmushi tayi tace"wallahi fa kinsan da aka ze yiwa su farid se akayi mistake aka biya harda nawa kawai shine Alhaji ya barni ba wai dan yana so ba". khairat tace"adda kekam daman kina da Sa'a".farida dariya tayi se Anam tace"gaskiya kam adda tafi kowa Sa'a a gidan nan".wayar khairat ce ta fara ringing,zaro ido tayi tace"yaya muffik yana kira na".Anam tace"ke da shi ai tunda wayar ki ya kira".amsa wayar tayi tace"yaya muffik ina wuni". muffik yace"lafiya,ki ce wa hamra ta kawo min fruit salad ɗaki na"."toh bari naje na faɗa mata". khairat ta faɗa tana tashi wa,katse wayar yayi a fili tace"in ba tsaban jaraba ba mesa baze kira hamra ba ko en ɗakin su se Ni".Anam tace"oho dai kiyi sauri kije ki kira ta". gwaɗa kai tayi se kuma ta zauna tana cewa"bari ma kawai na kira ta a waya".ta kira hamra a waya ta amsa se Khairat tace"ke yaya muffik yace ki kai mishi fruit salad ɗakin shi".hamra ta cikin wayar tace"na shiga uku wallahi bana gida". khairat zaro ido tayi ta wuce toilet sannan tace
"amma You are not serious,a babban gida ne zaki fita bayan kinsan is prohibited".hamra tayi shiru dan a tsorace take, khairat ta kara cewa"bari nace Mishi kanki na Miki ciwo so kinyi bacci".hamra tace"thank you thank you sister".katse wayar tayi sannan ta wuce kitchen ta haɗa mishi fruit salad ɗin sannan ta wuce ɗakin shi.knocking kofar shi tayi yace ta shiga,tana shiga ya kalle ta yace"sunan ki hamra ne?". khairat tace"a'a hamra kanta ne ke ciwo dakyar ta samu tayi bacci shine ban tayar da ita ba". muffik yace
"Kije kice mata ta shirya mu tafi asibiti". khairat zaro ido tayi tace"ciwon ba so---".katse ta yayi da tsawa yace"maida min magana kike yi?!!!".tace"sorry bari naje na kira ta".ta ajiye mishi fruit salad ɗin sannan ta fita.
Tana fita ta kira hamra a waya ta amsa se Khairat tace"ke yaya muffik fa yace ki shirya kuje asibiti,Ni bansan ya zanyi ba". hamra tace"what ni hamra na shiga uku". khairat ta buɗe baki zatayi magana taga kalil yana zuwa wurin, khairat tace"ina wuni". gwaɗa kai yayi yace"da wa kike waya?".tace"hamra".karɓan wayar yayi yasa a kunne yace"kizo ɗaki na in one minute".ya mika wa khairat wayar ya wuce, khairat tace"shikenan yau kin shiga uku a babban gida".hamra a rikice tace
"innalilahi wa innailaihi raji un,ni hamra yau na shiga uku,bari yanzun nan zanzo". khairat tace"kinsan yaya baya jiran mutum balle ma ya baki time,nikam na fita a harkar ki kafin a haɗa dani".hamra tace"wallahi yanzu zanzo kiyi hakuri". khairat tace"toh kiyi sauri".ta katse wayar sannan ta wuce ɗakin su taga ba farida.tana shiga ta zauna tana cewa"yau hamra ta shiga uku a gidan nan".Anam tace"me ya faru kuma". khairat gyara zama tayi tace"hmm wai picnic taje da friends nata".zaro ido sukayi Fatma tace"amma hamra madai bata da hankali"."ba wannan ba ma duk yaya muffik da yaya kalil suna neman ta". khairat ta faɗa tana kokarin kwanciya.anam tace"shikenan yau su yaya sun samu nama".dariya sukayi.

Babban gidaWhere stories live. Discover now