21

17 2 0
                                    

BABBAN GIDA

21

"Yaya ayban yayi hatsari".Anam razana tayi ta tashi a rikice tace"yaushe kuma a ina?".
Mira ma tashi tayi ta zauna.
Hamra tace"yanzu su yaya suka kira wai suna asibiti".
Anam da sauri ta fita daga side ɗin taje side na umma.
Tana shiga ta same umma se kuka take Abba yana rarrashinta.
Anam ma kawai hawaye ya fara zuba a idonta.
Daddy ya shigo yana cewa"ku shirya kawai mu tafi".
Da sauri su umma suka shiga ɗaki.
Anam kama hannun Daddy tayi tace"daddy Nima zan biku".
Daddy yace"Anam ki kwantar da hankalin ki mu zamu tafi".
Jan hannun shi yayi ya fita.anam zuwa side nasu tayi ta ɗauka school Bag nata tasa wani kaya guda biyu se tasa gele akan ta sannan ta wuce side na Alhaji.

Tana shiga ta same Alhaji suna kokarin fita,Anam da sauri tace"alhaji nima zan biku".
Alhaji yace"Anam ki zauna zamu kula dashi".
Anam tace"alhaji inaso naje".
Umma tace"alhaji kawai ku barta muje".
Haka dai suka yarda suka tafi tare da ita.
Alhaji da umma da Abba da Anam se daddy ne suka tafi.
Da Private jet suka tafi.

Mira da Nasir.

Mira da hamra suna zaune suna kukan ayban se Nasir ya shigo ɗakin yana cewa"kai kuna damu na".
Shiru sukayi hamra ta tashi zata tafi mira ta riƙe hannun ta tana karkaɗa mata kai.hamra tsoron Nasir take amma dai se ta koma ta zauna.
Nasir tsaya wa yayi yana kallon abinda suke yi.
Chan se yazo ya zauna kusa da mira,mira da har hawaye ya cika idonta ta fara kokarin tashi amma ta kasa dan bata iya tashi.
Murmushi yayi yace"ina zakije?".
Hamra kam tsoro taji ta tashi ta fita.
Mira ta fara kiran sunan ta amma har tayi nisa.
Mira kuka ta fara tana cewa"yaya dan Allah karka taɓa Ni zan mutu".
Murmushi yayi yace"mira ai kowa ze mutu".
Kwanciya yayi akan gadon yace"huh mira me zanyi dake ne?".
Mira kuka take ta dunkulu tana addu'an wani yazo amma ba wanda yazo.
Da tsawa yace"I'm asking you!!!".
Mira firgita tayi dan Muryar shi,a rikice tace"ya--ya ba-bu".
Murmushi yayi yace"mira babu?".
Da sauri ta gwaɗa kai.tashi yayi ya tsaya yana cewa"je ki dafa min abinci".
Mira tace"yaya bazan iya ba kafana yana min ciwo".
Ɗaga giran shi ɗaya yayi yana kallon ta.
Se yayi murmushi yace"baza kiyi ba kenan".
Mira da sauri tace"zanyi".
Kokarin tashi ta fara yi kawai se ya tura ta ta faɗi daga kan gadon.
Ihu tayi tana kuka,zuwa yayi yaja hannun ta suka fara fita.mira kuka take ga ƙafan ta ciwo yake.
Sanda suka isa kitchen ya tura ta ta faɗi Sannan yace"na baki nan da minti talatin ki dafa min abinci".
Fita yayi ya barta a kitchen ɗin tana ta kuka gashi kuma ta kasa tashi.

Chan se ga alisha ta shigo se taji Muryar mira tana kuka a kitchen,da sauri ta shiga kitchen ɗin ta tarar da ita a ƙasa tana kuka.
Alisha da damuwa tace"me ya fito dake mira?".
Mira a cikin kuka tace"alisha kafa na ciwo yake,ki bani magani na a ɗaki".
Alisha tashi tayi ta ɗauko mata maganin ta miƙa mata.
Mira shan maganin tayi sannan tace"alisha ki taya Ni dafa abinci".
Alisha ɓata fuska tayi tace"ai za'a kawo anjima kaɗan".
Mira tace"yaya Nasir yace in dafa Mishi".
Alisha taya ta tashi tayi dakyar dai mira ta samu suka dafa abinci.

Bayan sun gama suka jera a dining.
Jamila ta shigo tana cewa"mira ke da baki da lafiya me kike yi a nan?".
Mira tace"yaya Nasir yace na dafa Mishi abinci".
Jamila taɓe baki tayi tace"ayyah mira se hakuri".
Alisha tace"nikam wa yaga Anam ne".
Jamila tace"ance sun tafi Canada duba yaya ayban".
Mira ɓata fuska tayi tace"shine bata faɗa mana ba".
Jamila tace"kawai shirya wa tayi suka tafi".
Alisha tace"ayyah yaya ayban Allah ya bashi lafiya".
Sukace Ameen se Jamila ta fita.
Su khairat ma suka zo side na mira suka fara hira.

Se bayan sallar Isha tukunnan Nasir ya shigo.yana shiga duk suka tashi suka fita, mira se rokon su take karsu tafi amma suka tafi.
Nasir yace"ina abinci na?".
Mira a tsorace tace"gashi chan a dining".
Zuwa dining yayi ya zauna sannan yace"kizo nan".
Mira a tsorace ta tashi tana takawa ahankali dan ƙafan ta,haka har tazo wurin dining ɗin.
Nasir yace"zuba min".
Zuwa tayi hannun ta na rawa ta fara zuba mishi.bayan ta gama se ta matsa daga kusa dashi.cin abincin ya fara yana danna wayar shi.

Babban gidaWhere stories live. Discover now