BABBAN GIDA
5
"Ganinan Alhaji"doctor lawan ya faɗa yana shiga parlour.alhaji yace"bismallah ka shigo".zama yayi sannan Alhaji ya kara cewa
"Na kira ka ne inaso kamin aborting na cikin Jamila". doctor lawan yace"toh Alhaji duk abinda kace ai haka za'ayi".
Mami taje ta tsuguna a gaban Alhaji tana kuka tace"Alhaji dan Allah kar a zubar da cikin nan wallahi na yarda inta haihu zan karɓa yaron". Alhaji ya kalle ta sannan yace"mijin da zata aura yace baya son cikin Kinga dole a zubar dashi".mommy tace
"Alhaji toh a ɗaga auren se in ta haihu tukunnan se tabar yaron a wurin mami".
Alhaji shiru yayi se ya kalle harun yace"harun ka yarda da haka?".Anam ji take kamar ta shaƙe harun dan ta tsane shi,yana da bakin hali sosai.
Harun sanda yayi nazari kafin yache
"ehh Alhaji na yarda amma tana haihu wa da wata ɗaya za'a ɗaura auren".Alhaji yace
"Toh shikenan na ɗaga auren Jamila da harun se nan da wata takwas,kuma daga yau gaba ɗaya yaran mami zasu dawo babban gida da zama dan ban yarda da tarbiyyar da kuke bawa yaran nan ba".kawu yace
"Toh Alhaji mu ai bamu isa muja da kaiba".Alhaji yace"jibi ku gama shiri kuzo,na sallame kowa".Anam suka wuce side nasu aka zauna a parlour kowa yayi shiru kamar an musu mutuwa.
Mira ce ta fara magana
"wallahi Ni kam bansan wani irin marasa tausayi bane yaya harun ai da wani ne wallahi ze ce ze girmar da abun cikin ta".
Halisa tayi tsaki tace"hmm ai adda Jamila ta shiga uku dan yaya harun wallahi ba ze barta ba".Anam tayi tsaki tace
"Se ya kashe ta ai in yaga dama, wallahi Ni kam gidan nan ta ishe Ni". shiru ne ya biyo baya sannan munal tace
"Anam ke da mira ku dinga sanin abun faɗa dan wata rana bakin ku ze jawo muku bala'i".Anam tsaki taja ta wuce cikin ɗaki se Fatma tace"ai saura Anam da mira kar kuyi hankali".mira ta harare ta tace
"ai mu baza mu bari soyayya ta rufe mana ido har mubar na miji ya taɓa mu balle ɗaukan ciki,Ni bansan me adda Jamila take tunani ba harta bari ta samu cikin Bashir".
Khairat tace"nima abinda nake tunani dai".Farida tayi murmushi tace"baku san na miji bane,ze yi yanda zata yarda da kanta".halisa tace"hmm Allah ya rufa asiri".munal tace
"Yanzu adda Farida zaki riga adda Jamila aure fa kenan".Farida gwaɗa kai tayi sannan ta wuce ɗakin ta.
Hamra tace"munal da kinyi shiru ai kin san zata ji wani iri".hidaya tace"is better dai ta dinga tuno mata". fiddat tace"ita tayi Sa'a ai yaya Mustapha zata aura"."shine ai".Fatma ta faɗa tana tashi sannan ta fita daga side ɗin.Lokaci ya tafi har lokacin cin abinci yayi duk aka haɗu aka fara cin abinci.
Yau dining ɗin kamar gidan mutuwa kowa yana cin abinci.
Baba ne yace"Alhaji gobe ya kamata muje mu duba kayan da suka zo".Alhaji yace"ehh gaskiya kam se muje goben".Faisal yace
"Baba nima zan bi ku".Alhaji yace"Toh shikenan se muje da kai kaima". fiddat hararar Faisal tayi.Bayan sun gama cin abinci suka zauna a parlour hira kamar kullum.
Anam ta zauna kusa da kamal tace"munafiki ka faɗa min inda ka samo hoton ranar ko in faɗa Mishi". Kamal dariya yayi yace
"munafukai dai ai inni munafiki ne to ai ke kuma bansan me zan kira ki dashi ba". harararshi tayi tace"toh na yarda amma ranar kace zaka faɗa min inda ka samu amma baka zo ba".kamal yace
"Nazo ranar amma ba kowa a ɗakin ku shesa kawai na koma".Anam tace
"Ohh ranar ai munje yin game a ɗakin masir shesa".Faisal yazo ya zauna kusa da su yace"nima a bani na sha".Anam tace"Faisal kai akwai ka da son gulma wallahi,ba abinda muma muka sha balle mu bak---".ihun da suka ji ne yasa Anam katse maganar da take yi.munal ce tayi ihu dan halisa ta karɓe wayar ta."ungo naki".ummi ta faɗa tana zagin munal da hannu.
Anam taja tsaki tace"kuna abu kamar yara". masir yayi dariya.aka cigaba da surutu,masir ya zauna kusa da Faisal yana cewa"gobe ku shirya mu fita wallahi gidan nan ta ishe Ni".kamal yace"gaskiya kam ya kamata musha iskan waje".Anam tace"nidai ba ruwana amma fa zanje".dariya sukayi se masir yace"baza mu tambaya ba fa".Anam tace
"Daman wa ye ze tambaya".Kamal dariya yace"shesa kike burge Ni ai".mira tazo tace"zancen me kuke yi?".Anam jan hannun ta tayi tace"nasan bakya jin tsoro ki shirya gobe muje yawo".mira tace"an gama ai kin san mu da kiran ruwa".Faisal yace"zan bi su Alhaji da na biku wallahi".mira tace
"Ai kayi wa kanka".masir yace"gobe karfe sha ɗaya mu haɗu a garage sannan kowa ya tabbatar da ba wanda ya ganshi".Anam tace"an gama,yawwa se muje ka kowa min mota ma".masir yace"ai wannan me sauki ne".
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.