1

31 2 0
                                    

BABBAN GIDA

Yau su kalil, muffik, farid, farida, haidar, ayban suka kammala karatun degree nasu.su kaka dasu mommy duk sunje graduation nasu amma banda yara matan da suna zuwa school so basu jeba.

"Albishirin ki".Fatma ta faɗa tana zama a kusa da Anam wanda hankalin ta ke kan wayar ta,Fatma buga ta tayi tace
"Dake fa nake Anam banson rainin wayo".Anam ɗaga kai tayi tace"ba kunne bane ke ji".tsaki Fatma taja tace"ke daman ba'a isa an kawo Miki abu me daɗi ba se shegen masifa to na fasa faɗa Miki".
Anam harararta tayi tace"oho dai ki rike abin ki daman ba son ji nake ba". khairat ce ta shigo tana cewa"toh uwar masifa me kuma ya faru".
Fatma ta kalle ta tace"nazo na faɗa mata gobe su yaya ayban zasu dawo shine take min yanga".
Khairat da Anam suka zaro ido Anam da sauri tace"yaya ayban ne kaɗai ze dawo ko dukkan su?". Khairat ma zama tayi tace"kar kice min hadda su yaya kalil?".Fatma gwaɗa kai tayi Anam tace"wayyo Allah mun shiga uku, wallahi tunda suka tafi hankalin mu a kwance amma suna dawo wa shikenan".
Khairat tace"hmm ke dai ƙya faɗa".Fatma dariya tayi tace"ai koma me ne su yayun mu ne".Anam tace"bana taɓa manta lokacin da ya sumar da Ni wallahi mugu kawai".
Dariya sukayi daidai lokacin mira ta shigo tana cewa"gobe addababbun zasu dawo mun shiga uku ba kwanciyar hankali kuma".Fatma tace"a kunnen su". mira shiru tayi ta zauna tana cewa"Ni fa wasa nake yi Allah ya kawo su lafiya".sukace Ameen  khairat tace"gobe akwai aiki kenan amma wallahi makaranta zanje na yini".Anam tace"Ni Ko ke,ai gobe se magriba zan dawo".
Fatma tace"ai baku isa ba dan kunsan su mama basa nan so dole mu zamuyi".Anam tace"ga masu aiki me anfanin su".Fatma ta tashi ta wuce waje khairat ma Binta tayi mira kuwa kusa da Anam taje tace"se ayi hankali dai gobe dan kinsan yayun namu se a hankali".tana faɗan haka ta tashi ta gudu Anam a fili tace"da ma ki tsaya mana". cigaba da danna wayar take yi.

A ɗakin su alisha kuwa suna zaune suna kallon tv kowa hankalin shi a kallo yake.munal ce ta shigo ɗakin ta zauna tana cewa"kuna nan baku san abinda ke faruwa ba".ɗaga kai sukayi suka kalle ta fiddat tace
"Me ke faruwa kuwa".munal ta gyara zama tace"hmm ai gobe su yaya muffik zasu dawo".zaro ido sukayi hamra tace"na shiga uku Ni da na gama plan nawa akan zan fita gobe shikenan ai kuma fita ya kare".alisha tace
"Ai kuwa ya kare kam,Ni tsoro na ma wallahi jiya by mistake na fasa flower vase a ɗakin yaya muffik".
Zaro ido sukayi munal tace
"Shikenan ki shirya kuwa dan gobe jikin ki se yayi tsami". harararta tayi tace"ai zan bashi hakuri".hamra tace
"Bayan ya gama daka ki ba".dariya sukayi amma banda alisha dake ɗauke da damuwa a fuskar ta.fiddat ta duba lokaci tace
"Lokacin cin abinci yayi ku tashi mu tafi". gwaɗa kai sukayi suka wuce side na Alhaji dan a wurin kowa yake cin abinci a gidan duk da dai yanzu ba kowa se yara matan.

Suna shiga suka haɗu da sauran a dining ai kuwa suka kama hira masu aiki suna serving abinci.
Halisa tace"gobe dai kowa ze nitsu a gidan nan". fiddat tace
"Wallahi fa Ni har banso goben yazo dan kallon yaya muffik ma kawai ya ishe ka balle yaya kalil".mira tace
"Ni ku tsaya mana kunsan dai basa so masu aiki su gyara musu ɗaki ko".
Anam harararta tayi tace"ai kuwa se de ɗakin ya zauna da datti dan Ni kam bazan gyara wa kowa ɗaki ba". khairat tace
"Ai kuwa idan baso kike jikin mu yayi tsami ba gwanda mun raba wa kowa inda ze gyara".suka gwaɗa kai Anam tace"nifa ba ruwa na yanzu wani abu ya ɓa ci a daka ka bayan ba laifin kaba ne".alisha tace"wallahi gaskiya kam".munal tace
"Mu gama cin abinci tukunnan se mu tattauna". gwaɗa kai sukayi aka ci abinci suka gama masu aiki suka tattara wurin sannan khairat tace"gaskiya kunsan dai dole mune zamu yi gyaran nan in bamu yi Ba ma wani matsala ne".mira tace"gaskiyar khairat kawai ayi hakuri a raba  wa kowa aikin shi tunda Khairat ce babba anan se ta raba wa kowa".suka amince khairat ta fara da cewa"hamra, fiddat da mira ku gyara ɗakin yaya farid,ali--". fiddat ce ta katse ta da cewa"alhamdullilah".dariya sukayi khairat ta cigaba"alisha da halisa ku gyara ɗakin yaya muffik".zaro ido sukayi alisha tace"Ni na shiga uku kina so ki ɗaura min laifi bibbiyu yanzu ma ya na kare".mira tace"itace zatayi deciding se kiyi hakuri ki rungume ƙaddara". khairat ta cigaba"munal ki gyara dakin yaya haidar se hidaya ki gyara dakin yaya ayban se Fatma ki gyara ɗakin adda Farida se Ni da Anam zamu gyara ɗakin yaya kalil"."tab ɗijam me sa seni kunsan dai ba mu shiri ko". khairat tace"tare zamu yi ai karki damu".ta gwaɗa kai sannan kowa ya wuce ɗakin su.

Babban gidaWhere stories live. Discover now