BABBAN GIDA
6
"Ina zakuje?". zuciyar Anam yayi dum har zata tashi se taji Muryar hidaya na cewa"Alhaji ne yace mu duba Faisal dan ba ya ɗakin shi".
Anam wani sauke nunfashi tayi tana lekan su.
Muffik ne da twins ɗin wato hidaya da hamra suna tsaye.
Muffik yace"ok ku duba shi a side na Ammi".
Hamra tace"toh yaya". sannan suka wuce muffik ma yayi hanyar side na ummi.
Mira ta sauke wani nunfashin da batasan dashi ba tace"kai wallahi naɗau yaya muffik damu yake yi".Kamal yayi dariya yace
"Ni Ko ke,ai har zan tashi".Anam ta fashe da dariya tace"Allah nima daman zan tashi se naji Muryar hidaya".masir ya tashi yana cewa"ku tashi mu fita da wuri dan yanzu su Alhaji zasu fito".
Shiga motar sukayi masir yaja mota suka fita daga babban gida.Zagaya gari sukayi sosai sannan suka wuce wani wani fili dan masir ya koya musu mota.
Haka suka kai awa biyu a wurin har su Anam suka gwada tuka wa sannan suka kama hanyar babban gida."Pariii ga motan su Alhaji".masir ya faɗa yana juya mota da sauri.suka zaro ido kamal yace
"Bro kayi sauri dan suna ganin motar nan sun san nake Ni balle number na babban gida ne".
Ai kuwa da sauri masir ya same wani lungu yayi parking dukkan su a tsorace suke duk da dai a gidan suna basu da tsoro.
Mira tace"yanzu ya zamuyi?".Kamal ya kalle ta yace"mu tsaya se sun isa tukunnan".Anam dake duba agogon hannun ta tace"lokacin cin abinci saura minti ashirin".
Masir yace"ai kuwa bamu ga ta tsaya wa ba".kunna motar yayi da gudu yake tuki,basu kai minti goma ba suka isa babban gida aka buɗe musu gate sukayi parking,zasu fita Anam tace
"Daga nan side na Alhaji zamu wuce".
Direct side na Alhaji suka je ba'a wani taru ba ma kawai se suka zauna a dining.bayan minti kaɗan kowa ya haɗu aka fara serving na abinci.
Khairat ahankali tace wa Anam"ina kika je ne mukaita neman ki?".Anam ta kalle ta sannan tace
"Mun fita ne da su mira".zaro ido khairat tayi zatayi magana taga kalil na kallon su se tayi shiru.
Alisha tazo kunnen anam tace"yau kuma ina kuka je?".Anam wani kallo ta mata sannan tace"kin zama er sanda ne,toh ban sani ba".
Alisha murmushi tayi ta karkaɗa kai se Anam tace
"Toh banson tambayo yi". gwaɗa kai tayi ta cigaba da cin abincin ta.
Majid da fara'a yace"albishirin ku".
Shiru sukayi aka manna mishi.umma tayi murmushi tace"ayya Majid yana muku albishir amma kun manna Mishi".
Munal tace"umma kinsan ai me ze faɗa".
Ummi tace"gaskiya kam Majid tun bayan sati biyu a waya kace mana birthday naka ai bamu manta ba, Allah ya nuna mana goben".
Majid tura baki yayi yace"ina tuna muku ne dan karku manta".
Munal harararshi tayi tace"ai bamu manta ba". murmushi yayi sannan kowa ya cigaba da cin abinci.
Anam ne tace"akwai waɗanda in anzo cin abinci zaka rantse basu nan".
Wanni kallo suka mata wanda yasa ta sauke kai amma bai hana ta kara cewa"Ni fa ban kira suna ba se de in mutum ya tsargu".
Umma tace"Anam ke bakya jin magana Koh?".
Ayban yace"umma barta ai se nayi maganin ta tukunnan".
Rolling idonta tayi tana ɗaga ido suka haɗa ido da kalil wanda ke mata wani kallo da sauri ta sauke kanta.
Kaku ne tace"ku barta ai gaskiya take faɗa ya kamata kowa dai ya tofa albarkacin bakin shi".
Anam murmushi tayi se Alhaji yace
"In ana cin abinci ba'a magana".
Shiru sukayi kowa ya maida hankalin shi gun abinci.Bayan sun gama ci kowa ya watse Anam taje side nasu da taga ba daɗi se ta wuce side na Ammi.tana shiga ta samu Ammi a parlour tana kallon tv.
Zama tayi a kusa da ita tace"Ammi Ni gaskiya banji daɗin yadda kika yarda da auren adda Farida ba".
Ammi ta kalle ta sannan tace"kaji yarinyar nan Ni na isa na ja da Alhaji ne,ki rufa min asiri".
Kwanciya a cinyar Ammi tayi sannan tace"yanzu Ammi in nazo aure haka zaki yarda kenan?".shafa kan Anam tayi tace"Anam ai wannan ba daga wuri na bane, Alhaji ne yake zaɓi kuma Ni ban isa nace a'a ba".
Anam ta kalle ta tace"amma tayaya aka fara wannan abun".
Ammi sauke nunfashi tayi sannan tace
"Kinga kaka dai auren haɗi aka musu da Alhaji amma kaku kuma shi ya aure ta da zaɓin shi shima dakyar baban shi ya barshi dan kaka bata haife na mace ba,abun dai ya samu asali ne tun kakanni ai Kinga maza ba'a musu dole se de in za'a haɗa su da wata a dangin,amma mata kuma dole a haɗa su aure da dangin su".
Anam ta tabe baki tace"toh mesa aka bar su abi su aure ku?".
Murmushi Ammi tayi sannan tace"kin manta umma ai haɗa su akayi,mu kuma ai nace Miki maza ba'a haɗa su se de in akwai na macen da za'a haɗa su".
Gwaɗa kai tayi se tace"toh mesa in aka san kana soyayya to se bazaka ƙara kallon saurayin ka ba ko labarin shi?".Ammi ta taɓe baki tace
"Nima ban sani ba amma akwai lokacin da umma tace min ta taɓa soyayya da wani a ɓoye,da baban ta ya gane toh bata ƙara jin labarin shi ba ko yana raye ko ya mutu sanda ta haife alisha kafin taji labarin wai yana business a Dubai".
Anam ɓata fuska tayi tace"mesa tun a baya ba'a same shiba sanda ta haife alisha tukunnan?".
Ammi tace"bansani ba Anam amma dai watakila an Mishi gargaɗi ne shesa yabar ƙasan".
Anam tace"mesa toh dangin Jaffa suke da tsauri sosai?".
Ammi tace"Anam tambayo yinki yayi yawa".
Anam murmushi tayi tace"toh nayi shiru".
Haka suka ci-gaba da kallon tv.bayan minti kaɗan Farid da Farida suka shigo suna dariya suna hira.
Farida tana kallon Anam tayi murmushi tazo da wasa tace"tashi min akan cinyar ammi na".
Anam tura baki tayi tace"ai nima Ammi nane bazan tashi ba".
Ammi tayi murmushi tace"kai Farida kibar min Anam ta sarara".
Farid ya zauna yana cewa"yau kuma zancen me ake yi?".Anam ta kalle shi tace"babu fa kawai muna kallo ne".
Farida ma zama tayi a kusa da Farid tace"Farid yau fa se munje ka nuna min inda ka ajiye min abuna".jan hannun ta yayi suka fita daga side ɗin, Anam ta kalle Ammi tace"Ammi taya kika raine su adda Farida ne?".Ammi bugun wasa ta mata da gudu Anam ta wuce kofa tace"kai Ammi daga tambaya toh Ni na tafi".
Tana faɗan haka ta fita direct side nasu Majid ta wuce.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.