BABBAN GIDA
30
"Ke Anam zo nan".taji Muryar kalil daga parlourn sama yana kiran ta.
"Ikon Allah Anam me kuma kikayi".ta tambaye kanta tana hawa steps.
"Gani nan yaya".tana faɗan haka ta zaro ido tana kallon luby dake parlour akan kujera.
"Ban ce ki fita da abun nan ba?!!".ya tambaya yana matso wa kusa da ita.
"Ya--ya walla--hi na fita da ita amma se ba'a samu me riƙe taba shesa".ta faɗa zuciyan ta se buga wa yake.
"Ki fita da abun nan kafin na karya shi dake gaba ɗaya!!!".razana tayi yanda yayi ihun har bata san lokacin data fara hawaye ba.
"Ke ina Miki magana kina Min kuka?!!".ya tambaya da tsawa da kuma haushi.
"Yaya kayi hakuri".ta faɗa tana ɗaukan luby a hannun ta.
"Inkin dawo da abun nan se na karya ki".ya faɗa yana wuce wa kofan shi.
Anam kuka ta fara tana sauka daga steps.
Haka ta fita ta tafi garden nasu ta zauna tana ta kuka.
"Me ya same ki enmata?".salis ya tambaya yana zama kusa da ita.
"Yaya kalil ne wai in fita da luby".ta faɗa tana sheshsheka.
"Wa ye kuma luby Anam?".ya tambaya yana taɓe baki.
"Ga tanan".ta faɗa tana nuna kuliyan.
Dariya yayi dan abun ya bashi dariya.
"Dariya ma kake yi ko?".ta tambaya wani sabon kuka ta fara.
"Kiyi hakuri tashi muje wurin Amina ko zata riƙe Miki ita".ya faɗa yana tashi.
"Kasan matar ka da baƙin hali kaman yayan ta".Anam ta faɗa tana goge hawayen fuskar ta.
Dariya yayi yace"muje dai farko tukunnan".
Tashi tayi suka wuce side nasu salis.
"Salam".Anam tayi sallama tana shiga side ɗin.
"Amina kina ina".salis ya kwala mata kira.
"Ganin nan yaya".ta faɗa tana sauko wa da wani straight skirt da sleeveless top.
"Zo kiji".salis ya faɗa yana jan hannun ta.
"Amina daman luby nake so ki riƙe min kafin na samu wurin ajiye ta".Anam ta faɗa tana nuna mata lubyn.
"Toh shikenan amma dai zaki dinga ɗauka da dare kinsan bana son kuliya".Amina ta faɗa tana kallon luby.
"Shikenan zanzo na ɗauke ta anjima".Anam ta faɗa tana ajiye luby a ƙasa.
Fita tayi daga side ɗin tana tafiya tana cewa"se shegen baƙin hali,me ze hana ta riƙe har daren ma,kai dama wa adda nakai wa wallahi".tsaki taja tana shiga side na Farida.
"Sahid oyoyo".ta shigo tana faɗa.
Farida dake zaune da sahad tace"Anam sahad ne ba sahid ba,shi yana wurin baban shi".
"Don't tell me".Anam ta faɗa tana dariya sannan ta zauna kusa da sahad.
"Bari na tafi dashi ya taya Ni hira".Anam ta faɗa tana ɗaukan sahad dake ta mata dariya.
"Ɗauke shi daman na gaji".Farida ta faɗa tana kwanciya akan kujera.
Anam dariya tayi sannan ta fita.
Salis da Amina.
"Yaya bana so kasan bana son kuliya".ta faɗa tana gudu.
"Ai yau se na sa Miki a jiki".salis ya faɗa yana rike da luby a hannun shi.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.