BABBAN GIDA
4
"Ina er iskan nan?!!".kalil ya faɗa da tsawa,duk suka tashi dan tsoro."ganinan yaya kalil".Anam ta faɗa tana murmushi.khairat ta kalle ta tace"ke ce er iskar".Anam tazo kunnen ta tace"sunana na biyu kenan awurin ɗan iskan yayan ki".shigo wa yayi da shirt a hannun shi ya ɗaga yace"ke ce kika ɓarga min riga ko?!!!". gwaɗa kai tayi,da sauri ya fara zuwa wurin ta ya kusan zuwa ta ruga a guje ta fita,bata tsaya a ko ina ba se side na Alhaji,taje ta rike shi.alhaji dake kallon ta yace"wa ya koro ki haka?".tana nunfashi sama sama na gajiya tace"ya--ya kalil ne Alhaji ze kashe Ni".kaka ta shigo daga waje tana cewa"in baki tsokane shi ba ai ba abinda ze Miki".tura baki tayi tace"daman ai haka zaki ce".kaka ta zauna kusa da ita tace"me kika Mishi?".shiru tayi tana kallon Alhaji, murmushi yayi yace"kin Mishi wani abu ko?". gwaɗa kai tayi tace"amma ai shi ya fara se na rama".
A daidai lokacin kalil ya shigo rai a ɓace yace"yau me raba Ni dake se Allah".ya faɗa yana zuwa kusa dasu.kaka ce ta tashi tace"kai kalil mesa baka da hakuri ne, ƙanwar kace fa".kalil ya fara nuna Anam da yatsa yana cewa"shiga ɗaki na tayi ta ɓarga kaya na da scissors".zaro ido Alhaji da kaka sukayi suna mata kallon mamaki.alhaji yace
"Gata nan kayi mata duk abinda zaka mata".
Alhaji ya tashi Anam ma tashi tayi tana cewa
"Alhaji ka Dena so nane?,yaya kalil fa kashe Ni ze yi".
Ta faɗa kamar zatayi kuka.alhaji yace
"Ni ba ruwa na ke kika je har ɗakin shi kika tsokane shi".
Kalil zuwa yayi yaja hannun ta tana ihu suka wuce side nasu kalil ɗin.
Suna shiga parlour ya sake ta da tsawa yace
"dan ubanki mesa kika ɓarga min kaya?!!!!".
Kuka ta fara yi shi kuwa abun ya kara bashi haushi.farid ne ya fito yana cewa"bro dare fa yayi me ya faru take kuka?".farid ya faɗa yana sauko wa daga steps.kalil yace"ɓarga min riga taje tayi da scissors".farid zaro ido yayi ya kalle Anam dake kuka yace"Anam wai baki da hankali ne?".kuka ta cigaba da yi.farid yace
"bro dan Allah kayi hakuri kaga dare yayi ka barta bazata ƙara ba".
Kalil yace
"zata sake ai bata jin magana,yau se na karya ki a gidan nan".
Ayban ya fito yana cewa"harda karaya abun babba ne".farid yace"hmm Anam yarinyar nan rashin jin ta yayi yawa,kayan bro taje ta ɓarga da scissors".ayban sauko wa yayi yana cewa"shine baka daka taba?".ayban koma wa yayi ya ɗauko belt ya sauko.
Anam tana kallon shi ta fara ihu tana bada hakuri amma ayban yace shi da kanshi zeyi maganin ta.ai kuwa haka akayi ayban duka ya mata su haidar sun fito taimako amma inaaa ayban yaki hakura.sanda ya dake ta son ranshi sannan yace
"gobe in kara ganin kina rashin ji a gidan nan,dan tsaban rashin hankali ma se ki ɓarga kayan mutum,this is the first and the last,ok!!!".
Ya faɗa da tsawa da sauri ta gwaɗa kai.ayban yace
"Ki bashi hakuri"."yaya kalil kayi hakuri bazan kara ba".ta faɗa tana kuka.gwaɗa kai yayi dan taɗan bashi tausayi.ayban yace ta tafi side nasu.Tana shiga side nasu ta same su a parlour suna zaune kowa da damuwa a fuskar shi.suna kallon ta duk suka tashi,alisha ne tace"sannu Anam kije ki kwanta".
Gwada kai tayi ta wuce tayi wanka se sallah se ta kwanta.Basu tashi daga bacci ba se karfe tara lokacin breakfast,da sauri duk suka shirya sannan suka wuce dining.as usual suka gaisa sannan akayi serving abinci.
Kaka ce tace"Anam ya kikayi da yayan ki jiya".Anam bata kula ta ba ta cigaba da cin abinci.kabir ne yace
"Hmm ai jiya yaya ayban ne ya daka ta".umma tace
"Ayban mesa ka dake ta?".
Farida ne yace"yarinyar nan kayan bro taje ta ɓarga da scissors".kowa ya zaro ido mama tace"Anam abun har yakai na ɓarga kaya ne?".Anam ko ci kanku bata ce musu ba.ummi tace"daman ai kunsan Anam da tsokana".ammi tace"ai yayi daidai daya duke ta gobe baza ta kara ba".umma tace
"Gaskiya kam ayban kamin daidai gobe zata nitsu".Anam haushi kamar ya kashe ta a zuciyan ta tana cewa badai duka bane ai se de su kashe ta amma ba abinda ze hana ta abinda take son yi.
Khairat tace"in mun gama breakfast zamu wuce gidan mami". mommy tace"to ku gaishe su". gwaɗa kai sukayi.Bayan sun gama cin abinci suka wuce gidan Mami.suna isa suka gaisa da mami sannan suka wuce ɗakin jamila.a kwance suka same ta,Anam tace
"Amarya baki da lafiya ne?".Jamila tashi tayi ta musu murmushi tana cewa"harkun zo?". gwaɗa kai sukayi suka zauna Jamila tace
"wallahi saura kaɗan mami ta gane ina da ciki,tsoro nake ji".khairat ta rike hannun ta tace"karki damu komai ze wuce".Anam tace
"Yanzu shi Bashir ɗin yasan kina da ciki ne?".
Gwada kai tayi se Fatma tace
"Kawai ki samu Alhaji ki faɗa Mishi kina da cikin Bashir kuma shi kike so ki aura".zaro ido sukayi Anam tace
"Ke mesa baki iya bada shawara bane,tana faɗa wa Alhaji wallahi se an zubar da cikin nan,Bashir kuma ya shiga uku itama Jamila haka".
Jamila tace
"Ba maganan faɗa wa Alhaji ma".
Khairat tace
"Ga shawara,kawai kiyi hakuri ki aure yaya harun se ki haihu a gidan shi Kinga ba me tambaya".
Fatma tace"kinsan yaya harun yana sanin tana da cikin da ba nashi ba ze faɗa wa Alhaji".
Anam tace"kuma haka ne fa,Alhaji yana ji kuma komai ya ɓaci".
Jamila kwanciya tayi ta lumshe ido sannan tace"kune fa komai nawa yanzu,dan Allah ku taimaka min wallahi Ni bana son harun ko kaɗan".
Junnaya tayi sallama ta shiga tana cewa"kun zone dama?". murmushi sukayi Fatma tace
"Munzo tunɗazu".junayya tace
"Mami tace ku shirya se ku tafi dan Alhaji yace ku koma da wuri".
Gwada kai sukayi sannan suka shirya suka wuce shopping.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.