BABBAN GIDA
7
"Abinda kike yi kenan ko dan uban ki".wani razana tayi harun yazo yaja hannun ta salim ma ya rike hannun ta ɗayan.
Harun da zafin nama yace"kai ka sake ta kafin naci uban ka anan wurin".
Salim zeyi magana Anam ta kalle shi tace
"Salim kayi hakuri ka sake min hannu".sake ta yayi ahankali sannan tace"ka yafe min se wata rana".
Harun yaja ta suka shiga motar shi.Basu tsaya ko ina ba se babban gida.jan hannun ta yayi suka wuce side na Alhaji.suna shiga Alhaji yana zaune yana karanta newspaper.
Harun yace
"Alhaji yau naga Anam da wani ɗan iska suna soyayya a makarantar su".
Se yanzu Alhaji ya ɗaga kai daga newspaper ya kalle su sannan yace"Anam ɗin?".
Harun yace"ehh ita da wani har kama hannun ta yayi".
Alhaji wani kallo yayi wa Anam ita kuwa hawaye ne suke zuba a idonta, ahankali ta taka taje gaban Alhaji ta tsuguna tace
"Wallahi Alhaji ba soyayya muke yiba kawai ya zo tambayar ko lafiya waya na a kashe kuma wallahi nace Mishi mu rabu".
Alhaji yace"jiya me kika ce min?".
Anam ta fara kuka tana cewa
"Wallahi Alhaji shi yazo kuma sallama mukayi na maka alkawarin bazan ƙara kula shi ba".
Harun yace"Alhaji karya take yi karka yarda da ita".
Wani kallo ta Mishi yazo da zafin nama ya ɗaga hannu ze mare ta ayban dake shigo wa ya rike hannun shi.
Ayban yace"me ta Maka da zaka sa hannu zaka mare ta".
Harun yace"banzan kallo ta min".
Ayban yace"wannan ba hujja bane".
Alhaji yace
"ya isa haka daga yau ina so harun ka sa min ido akan Anam kuma daga yau da bodyguard zaki dinga zuwa makaranta sannan ko da wasa naji an ganki da wani toh wallahi wallahi wallahi Anam aure zan Miki".
Zuciyar ta yayi dum sannan tace"inshallah hakan baze ƙara faruwa ba".
Alhaji yace"na sallame ku".Tashi tayi duk suka fita sanda ayban ya tafi tukunnan harun yace
"Se nayi maganin ki, Alhaji ya bani aiki me kyau".harararshi tayi ta wuce side nasu daidai lokacin su Fatma suka dawo daga makaranta.
Suka haɗu a kofa Fatma tace"Anam ke kuma zaki dawo gida da wuri shine baki faɗa mana ba mukai ta jiran ki".
Anam jiki a sanyaye tace"Ni da yaya harun ne muka dawo shesa".
Khairat tace"me ya kaishe makarantar mu kuma".
Anam tace"je ki tambaye shi ai bai tafi ba".
Khairat tace"rufa min asiri a barni a gida maza su binne Ni".munal ta shigo da sauri tana cewa
"Kuyi sauri za'a fara birthday".
Fatma tace"Ni na manta ma wallahi".
Khairat tace
"Ni Ko ke,amma fa ban manta da fitan anjima ba".
Da sauri suka shirya sannan suka wuce side na ummi dan a wurin za'ayi birthday ɗin.
Anam tana shiga ta zauna kusa da Kabir a kunnen shi tace
"Ka samo min?".
Murmushi yayi ya mika mata wani abu a leda ta karɓa itama tayi murmushi sannan Majid yazo yace
"Adda Anam ina gift nawa".
Murmushi tayi tace"se anjima zan kawo maka". gwaɗa kai yayi.
Suka haɗu aka fara Mishi waƙan birthday Anam taje bayan ayban ta buɗe ledan hannun ta ta ɗeba kaɗan ta zuba a wuyan shi da sauri ta matsa haka taje bayan muffik ma ta zuba Mishi se kalil ma haka.ba wanda ya kalle ta sannan kowa ya fita waje ɗaukan hoto.
Muffik ya fara sosa wuyan shi haka fa kalil da ayban suka fara sosa wuyan su abu kamar wasa har kowa hankalin shi ya dawo kansu.kowa danne dariyar shi yake ana sannu amma banda Anam wanda ke dariya har ƙasa har hawaye take dan dariya mira ma fa dariya ta fara saura se danne wa sukeyi iyayen ma kansu sunyi sunyi su danne amma ina kowa dariya yake.
Alhaji ne yace su haidar su kaisu asibiti sannan aka wuce dasu asibiti.
Anam ta kasa shuru har bakin ta ya fara ciwo dan dariya.
Khairat ne tace"kar ki Dena dariya ai se an ce ke kika musu".
Anam dakyar tace"toh daman wa ya sa musu in ba Ni ba,hmm ai asosa na sa musu a wuya".
Khairat da Fatma zaro ido sukayi Dan su kaɗai ne suke ji.
Fatma tace"tabɗijam yau Anam kin shiga uku a gidan nan".
Khairat tace"ba ruwa na banji ba".
Mira ce tazo ta ɗaga anam itama dariya take tace
"Na daɗe banji daɗi irin na yau ba".
Anam a dariya tace"I'm telling you".Ummi ne tace"kai dariyar nan ya isa muje muci cake kafin su dawo".
Ai kuwa suka cigaba da celebrating birthday.Mira tazo kunnen Anam tace"nasan ke kika zuba musu ko?".
Anam tace"ai kuwa ramako ne nayi dan yaya muffik da yaya ayban sun mare Ni a gaban kowa shi kuma yaya kalil daman tara shi nake".
Mira tace"kin burge Ni amma fa insun dawo akwai matsala".
Anam taja tsaki tace"su kashe Ni in sunga dama Ni dai ba na rama ba,abun kunya".
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.