32

9 1 0
                                    

BABBAN GIDA

32


"Da izinin waye kika fita?".

Mira zuciyan ta wani irin buga wa yayi dan tsoro.

"Mira tambayan ki nake".Nasir ya faɗa yana tashi.

"Ya--ya dama--".Anam ne ta katse ta da cewa

"Ni nace ta raka ki".

Murmushi yayi yace"bata ce Miki na hana ta fita ba da izina na ba?".

"Ta faɗa amma nace mata yanzu zamu dawo".Anam ta faɗa da tsoro kaɗan a Muryar ta.

"Ta faɗa Miki amma da shike kin raina Ni kika ce ku tafi ko".ya faɗa yana kallon ta.

"Yaya kayi hakuri".mira ta faɗa duk tabi ta haɗa gumi dan tsoro.

Zuwa yayi kusa da mira dake kokarin gudu.

"Ke bani yaro na".Nasir ya faɗa.

A tsorace a matso kusa dashi tana miƙa mishi Hisham.

"Munal je ki kawo min belt,yau se na nuna Miki inna bada iko a gidan nan ba wanda ya isa ya taka".Nasir ya faɗa yana kallon Anam.

"Yaya kayi hakuri kawai fa waya na na karɓo".Anam ta faɗa hawaye sun cika idonta.

Ba jima wa munal ta kawo mishi belt se ya miƙa mata Hisham sannan ya matso kusa da Anam.

"Yaya dan Allah kayi hakuri bazan sake fitar da ita ba".Anam ta faɗa tana matsa wa baya.

Murmushi Nasir yayi ya ɗaga belt ɗin ze zuba mata aka riƙe ta baya.

Murmushi yayi yace"third time,kalil baka tunanin limit naka ya wuce".

Kalil jan belt ɗin yayi ba wasa ko kaɗan a fuskar shi yace

"Nasir baka da ikon dukan matata in baka tambaye izini ba".

"I guess yau ina da iko tunda ita ta ɗauke matata suka fita ba tare da izini na ba".Nasir ya faɗa yana kallon Kalil cikin ido.

"Ka tambaya kafin ka ɗauke hukunci".kalil ya faɗa.

"Kalil kenan".Nasir ya faɗa yana murmushi.

"Go ahead".kalil ya faɗa yana bashi belt ɗin.

"Yaya kalil dan Allah ka bashi hakuri".Anam ta faɗa tana komawa baya.

Kalil wuce wa yayi ya zauna yana kallon su.

"Gobe ki tambaye izini na kafin ki ɗauke matata".Nasir ya faɗa yana zuba mata belt ɗin a baya.

Sanda ya duka ta iya son ranshi kafin ya barta,se kuka take tana ihu.

"Kowa ya wuce side nashi".Nasir ya faɗa yana jan hannun mira.

Kowa ya watse se Anam dake kuka da kalil dake danna wayar shi yana zaune.

"Ke ki ɓace anan kafin na kara Miki".kalil ya faɗa yana danna wayar shi.

Tashi tayi ta wuce side nata.

Amina da salis.

"Kai wannan yayan ki akwai baƙin hani".salis ya faɗa yana zama akan kujera.

"Hmm ai yaya Nasir kam se addu'a".Amina ta faɗa tana zama dakyar.

"Cikin nan yana wahalar min dake fa,gashi se girma yake yi".salis ya faɗa yana jan ta jikin shi.

"Eh fa yaya ina shan wahala kuma doctor yace kaman twins ne".

Zaro ido yayi yana farin ciki.

"Masha Allah kai nayi murna".salis ya faɗa yana kissing kumatun ta.

Babban gidaWhere stories live. Discover now