BABBAN GIDA
33
"An nema hamra an rasa".munal ta faɗa da damuwa a fuskar ta.
"Amma yaya ayban yace bari ya duba ta bazatayi nisa ba".halisa ta faɗa.
"Ya rabb toh Allah yasa a same ta".Anam ta faɗa tana zama a steps na shiga side ɗin.
"Yau se taci ubanta in aka same ta".hidaya ta faɗa.
"Haba mana kukasan dalilin ta".Isha ta faɗa tana riƙe da Adnan.
"An same ta?".mama ta tambaya suna shigo wa side ɗin da sauran iyayen.
"A'a ba'a same ta ba".halisa ta amsa wa mama.
"Karku damu za'a same ta".haidar ya faɗa yana fitowa daga side nashi.
Zama sukayi kowa hankalin shi a tashe,sauran ma duk fitowa sukayi gashi ana ta kiran wayan ayban baya ɗauka.
Se bayan kusan minti talatin se ga motan ayban ya shigo sabon gida.
Duk tashi sukayi suna jira ya fito.
Hamra ce ta fara fitowa se ayban ma ya fito.
"Ke dan ubanki ina kika je?".mama ta tambaya tana zuwa kan ta.
"Mama kiyi hakuri".hamra ta faɗa tana matsa wa baya.
"Ke waton duk nasihar da aka Miki baki ji ba ko".Ammi ta faɗa tana girgiza kai.
"Ku barta dani,zan hukunta ta da kaina". ayban ya faɗa yana jan hannun hamra.
"Yaya dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara gudu ba".hamra ta faɗa kamar tayi kuka.
"Se da safe".ayban ya faɗa yana rufe kofar su.
Watse wa kowa yayi daga wurin.
Ayban da hamra.
"Na ce Miki karki yadda ki aure Ni amma kika ƙi ji yanzu kuma da mukayi aure kina tunanin zaki barni ne". ayban ya faɗa yana jan hannun ta ɗakin shi.
"Yaya dan Allah kayi hakuri na tuba bazan kara gudu ba". hamra ta faɗa tana kuka.
"Yau ne zan saki nadaman aure na na gaske hamra".ayban ya faɗa yana ture ta kasan carpet.
Closet nashi ya shiga ya dauko belt,baya baya ta fara tana bada hakuri amma ko a jikin shi.
"Yau se na nuna Miki kinyi kuskuren aure na hamra".ya faɗa yana matso wa kusa da ita.
"se na nuna Miki halin ayban da ba wanda ya sani,se na maida rayuwar auren mu lalatacecciya hamra,se na maida ki abun tausayi hamra,se na raunatar dake hamra wannan alkawari ne".ya faɗa yana zuba mata belt a baya.
Ba karamin duka ayban yayi mata ba,daga tana kuka har ta dena, nunfashin ta se sama sama yake amma bai Dena dukan ta ba,sanda yayi na isan shi sannan ya barta.
"Ki fita daga ɗakin nan".ayban ya faɗa yana wuce wa kofan toilet nashi.
Dakyar ta tashi tana jin jiri jiri amma a haka ta wuce ɗakin ta,kukan ma ta kasa yi kawai tana tuno furucin da yayi ne.
Muffik da Fatma.
"Yaya me zan dafa maka".Fatma ta tambaya tana sauko wa daga steps da ɗingishi.
"Nace Miki ina jin yunwa ne?". muffik ya tambaya hankalin shi nakan news a tv.
"Baka jin yunwa kenan?".ta kara tambaya tana zuwa parlourn.
"Ke kurma ne?".ya tambaya yana kallon ta.
"A'a kawai dai naga baka ci abinci ba ne".
"Me ya shafe ki da cin abinci na?".ya maida mata tambaya.
"Yaya kai fa miji na ne kuma dole ne nasan ko ka ci abinci ko baka ci ba".ta faɗa tana kallon shi.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.