13

13 2 0
                                    

BABBAN GIDA

13

Suka zaro ido suna kallon wanda ya fito daga motan.wa zasu gani se suka ga kalil ya fito se mira ma ta buɗe dayan kofar.
Kana ganin ta kasan ba karamin dakuwa tayi ba.
Tana fita zubewa tayi a ƙasa tana kuka ta fara cewa"dan Allah ku yafe min nasan nayi laifi,ku hukunta Ni duk yanda kuke so".

Ummi ce taje ta wanke ta da mari sannan ta rungume ta itama kuka ta fara dan ba karamin kewar erta tayi ba.mira a cikin kuka tace"ummi ki yafe min nasan na saki a damuwa,wallahi sharrin shaidan ne bazan kara ba ki yafe min".
Ummi tace"mesa kika tafi kika bar ummin ki a damuwa,kinsan damuwan dana shiga da kika tafi kuwa?".
Mira tace"ummi na tuba kimin duk abinda kike so".
Ummi sake ta tayi ta tashi,Anam da sauri taje ta rungume mira tana cewa
"Munafuka kika tafi kika barni,baki san zanyi missing naki ba".
Mira a kuka tayi murmushi tace"Sarkin tsokana nima nayi missing naki ba kaɗan ba".
Anam ta kalle fuskar ta tace"mugun nan ne ya miki haka ko?".
Mira gwaɗa kai tayi se Anam ta sake ta, haka sukai ta farin ciki da sannan mira taje ta tsuguna gaban Alhaji tace
"Alhaji nasan nayi laifi amma ka yafe min bazan kara ba na tuba".
Alhaji yace"mira na daɗe da yafe Miki amma aure zan Miki kuma kin gama makaranta kenan".

Mira zaro ido tayi tace"Alhaji dan Allah karka min haka Alhaji sharrin shaidan ne".
Abu yace"ba maganan sharrin shaidan kece sheɗaniyar tunda da ƙafan ki kika fita ba wanda yace kije".
Shiru tayi Alhaji yace"kalil me ya faru ne wayan ka ya Dena shiga kuma taya ka same ta?".
Kalil dake zaune akan kujera yace
" Ni na kashe wayar da kaina sannan na samu mira a wani park ne ita da saurayin nata".
Alhaji ya tambaya"ya kayi dashi?".
Kalil yace"maganan ya wuce Alhaji se de wani labarin kuma".
Shiru sukayi suna kallon kalil da mamaki.

Anam a zuciyar ta tana cewa me yake nufi maganan ya wuce?.
Alhaji yace"toh yayi kyau,haidar ka kira kowa gobe akwai meeting".
Haidar gwaɗa kai yayi.
Harun ne yace"kun manta dasu Anam fa".
Anam wani kallo tayi Mishi.
Farid yace"a bar maganan gobe baza su ƙara ba".
Kalil ne ya tambaya"me suka yi?".
Harun yace"sun fita ne basu tambaya ba".
Kalil tashi yayi yace"shine kuma za'a barsu ai gobe zasu ƙara,munal kawo min belt".
Ya gama maganan yana kallon munal.
Ai kuwa munal taje ta kawo belt ya karɓa ya fara zuwa kan Anam,ya ɗaga ze zuba mata ta riƙe belt ɗin.
Wani kallo yayi mata yace"daga tafiya na har kin koya raini kenan".
Jan belt ɗin ta fara yi tana cewa"kai da yanzu kazo me ruwan ka da dukan mu".
Kalil daya wani ja belt ɗin ya zuba mata,ihu tayi taja baya zata gudu ya riƙe hannun ta.

Ai kuwa ta daku kuma yace abar sauran tunda itace uwar raini.
Bayan ya gama dukan ta ya bar wurin ita kuwa kuka take yi,dakyar suka rarrashe ta sannan kowa ya watse a wurin su ma suka wuce side nasu.

Anan ne suke tambayar mira taya ta gudu kuma me kalil yayi da saurayin ta
Mira ce ta fara cewa"daman na daɗe ina so na gudu se saurayi na yace in shirya mu gudu shine kawai ranan na fita na same shi muka tafi Dubai,muna Dubai aka sanar mana Alhaji yana neman mu shesa muka dinga zagaya duniya.saurayi na kuma  lokacin da yaya kalil ya same mu  se yasa wasu suka ɗauke shi Ni kuma muka tafi tare dashi ya min dukan da ko motsi bana iya yi,sanda naɗan warware tukunnan muka dawo".
Anam dake kwance tace"a hakan ma kin warware kenan,kice kin daku".
Dariya sukayi se hamra tace
"Amma ya kika ji da kika gudu farko?".
Mira tace"freedom yafi komai daɗi,da na gudu ba karamin murna nayi ba amma yanzu ina nadama sosai".
Fatma tace"daman ai dole kiyi nadama gashi yanzu Alhaji aure ze Miki kuma watakila ma gobe a family meeting za'a sa rana".
Mira da damuwa a fuskar ta tace"wa ye ne ze haɗa Ni da?".
Munal tace"bai faɗa ba yace se kin dawo".
Mira tayi tagumi tace"Allah yasa yaya shureim ne".
Anam tace"ku wai me damuwan ku dashi ne,kowa in ya tashi se yace yaya shureim,toh bari kuji yaya shureim nawa ne Ni kaɗai".
Khairat dake harararta tace"ai baki isa ba yaya shureim Ni ze aura".
Fiddat ce tace"calm down bakusan wa ye ze aura ba kawai mu jira mu gani".
Shiru sukayi se mira ta tambaya
"Me ya faru da bana nan?".
Ai kuwa suka ba ta labarin komai sannan mira tace"Allah Sarki Jamila cikin ta ya zube wallahi harta bani tausayi".
Anam tace"ai ba tausayin rashin cikin bane kaɗai harda mijin da ta aura".
Wata me aiki ne ta shigo tace musu lokacin cin abinci yayi.

Babban gidaWhere stories live. Discover now