10

22 2 0
                                    

BABBAN GIDA

10

Duk suka juya dan suga daga ina sautin marin yazo.ai kuwa harun ne ya wanke Jamila da mari a gaban kowa.
Duk suka tashi Jamil ne yaje wurin da zafin nama yace
"Me haka,me ta Maka da zaka mare ta a gaban kowa?".
Harun kallon Jamila yayi wanda ta rike inda ya mare ta tana Mishi wani kallo duk da akwai tsoro a idonta.
Harun yace"tun yaushe nake kiran ki a waya amma dan tsaban raini kika ƙi ɗaga wa".
Anam tace"tabɗijam amma yaya harun ka fara shaye shaye ko?".
Wani kallo ya mata ze fara zuwa wurin ta Jamil ya rike hannun shi yace
"ai gaskiyar tane yaya harun bai kamata ka mare ta ba dan bata ɗauka wayar ka ba,ka sani ko wayar baya kusa da ita".
Harun yayi wa Jamil wani kallo sannan yace
"Kai ne zaka faɗa min abinda zan yi da mata ta".
Anam zatayi magana Alhaji dake zaune yace"Jamil kabar wurin,ai yayi daidai ya kamata ta fara Mishi biyayya tun kafin suyi aure".
Kowa kallon mamaki yake wa Alhaji.
Ammi tace"haba dai Alhaji ai ba'a ɗaura auren ba tukunnan balle yace ze hukunta ta".
Abi ne yayi mata wani kallo yace
"Kar in kara jin Muryar ki,abinda Alhaji yace shine gaskiya kuma haka ze zauna".
Wurin kowa tsit yayi sannan Alhaji ya dube Jamila  yace"ki bashi hakuri".
Jamila kamar tayi kuka tace"yaya harun kayi hakuri bazan ƙara ba".
Harun yace"next time Ina kiran ki ki ɗaga min waya dan bana son jira".
Gwaɗa kai tayi sannan ya bar wurin.
Kowa jikin shi yayi sanyi amma haka aka cigaba da walimar.

Bayan an gama kowa ya wuce side nashi.jamila kam har tayi bacci dan tayi ta kuka kafin ta samu tayi bacci.

Junayya ce tazo wurin Fatma tace"dan Allah Fatma ki rakani wurin jalil zan karɓa abu na".
Fatma tace"ina wani abu ga Anam ta raka ki".
Anam tashi tayi tace"zo muje".
Side nasu Majid suka wuce.suna shiga suka same su duk a parlour suna zaune.junayya taje wurin jalil suna magana Anam kuwa wurin salis taje ta zauna tana cewa"nazo na rama abinda ɗazu kamin".
Murmushi yayi yace"toh gani nan rama abunki".
Wayar shi ta warce ta tashi ta gudu tana cewa"junayya in kin gama Ni na tafi side namu".

Salis tashi yayi shima ya bita a baya,saura kaɗan ta isa kofar side nasu ya riƙe hannun ta yana dariya yace"wa na kama".
Itama dariya tayi tace"yaya salis ka sake Ni ai yau kai da wayar ka kunyi bye bye".
Fara kokarin karbar wayar yake yi ita kuwa damƙe shi a hannun ta.
"Me kuke yi anan wurin?".
Daddy ya faɗa yana tsaye ta gefe,sake hannun ta salis yayi sannan yace"daddy nazo na karɓa waya na ne".
Daddy ya kalle Anam yace"second wife kiyi hakuri ki bashi wayar shi".
Tura baki tayi tace"ai shine ɗazu ya karɓa min jaka na sanda yaya Yasir yace ya bani kafin ya bani".
Salis yace"yi hakuri tsokanar ki nake yi".
Mika mishi wayar tayi se yayi murmushi sannan ya wuce Anam kuma wurin daddy taje tace
"Daddy ka manta dani ko?".
Murmushi yayi yace"na isa na manta da mata ta ne".
Wayar shine ya fara ringing kawai se ta wuce side nasu ta same su munal da halisa suna dambe.tsaki taja ta wuce ɗakin su inda su Fatma dasu Isha suke hira,itama zama tayi .
Kauthar tace" hmm ɗazu naje side na Alhaji se na shiga ta kofan baya naji suna magana da Alhaji Aliyu wai za'a haɗa auren yaya Jamil da sumayya".
"Hmm sun faɗa yaushe?".sumayya ta tambaya tana taɓe baki.
Kauthar ta karkaɗa kai,Anam tsaki taja sannan ta tashi tace"se wata rana kun jiyo wa kanku bala'i".
Tana faɗan haka ta wuce toilet.bayan ta gama komai ta kwanta bacci.

Tun asuba suka tashi aka fara shirye shirye gashi kuma yau su Nasir, shureim,fadil,Mansur,Abdul da isa zasu dawo dan sun gama masters nasu.kowa yau busy gashi ana shirya amare,Jamila kam har zazzaɓi ya kama ta dan kuka.a inda Alhaji ya gina dan inyaran sunyi aure za'a ajiye su,gate ɗin estate ɗin yana cikin babban gida so in zaka fita daga estate ɗin se ka shiga babban gida.a estate ɗin akwai side daban daban wanda zasu kai ashirin kuma duk beni ne kuma paint ɗin duk milk colour ta waje amma ta ciki daban-daban ne.

Mesa ne zasu sauka a babban gida?". khairat ta tambaya tana shafa lip gloss a bakin ta.anam dake miƙa wa Farida gele ne tace
"Nifa bani da matsala da sauran kawai bana so yaya Nasir ya sauka a nan ne".
Farida tayi murmushi tace"ayi dai ahankali kafin ku jawo mana bala'i a babban gida".
Hamra tace"ki faɗa musu kam ɗan kinsan ƙaramin aikin shi ne".
Tsaki Anam taja ta fita daga ɗakin.

Babban gidaWhere stories live. Discover now